Abba Ibrahim Wada" />

Su Waye Su Ka Fi Taimakawa Wajen Zura Kwallo A Raga?

kwallo

 

Ranar 17 ga watan Oktoba za a ci gaba da wasannin mako na biyar a gasar cin kofin Premier League ta kakar wasa ta shekarar 2020 zuwa 2021 kuma kawo yanzu an buga wasanni 38 an kuma ci kwallo 144, bayan kammala wasannin mako na biyar.

Kuma kawo yanzu dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Everton, Dominic Calvert-Lewin da kuma Son Heung-min na Tottenham su ne kan gaba wajen cin kwallaye a raga inda kowanne ke da kwallaye shida-shida a raga.

Gasar ta Premier League ta bana na samun armashin cin kwallaye da dama, sai dai kuma masu bayar da kwallon da ake zura wa a raga su ne ke taka rawar gani a wasannin saboda yadda suke nuna kwarewa wajen bada kwallayen.

Duk da cewar wasanni hudu aka kara a kakar bana kawo yanzu, dan wasa kuma kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Harry Kane shi ne kan gaba da kwallo shida da ya bayar aka zura a raga a gasar shekarar nan.

Kuma ya yi namijin kokari a bana duk da cewar guda bakwai ya bayar da aka ci a kakar wasan shekarar 2016 zuwa 2017, saboda haka yanzu aka fara lissafi ko da yake ana ta buga wasannin bana ba ‘yan kallo don gudun yada cutar korona.

Tun cikin watan Maris aka dakatar da wasanni daga baya aka ci gaba ba ‘yan kallo da ta kai aka karkare kakar bara wacce kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lashe kofin kuma na farko tun bayan shekara 30.

A kakar da ta wuce dan wasan Manchester City  Kevin De Bruyne shi ne kan gaba a bayar da kwallo a zura a raga inda ya taimaka aka zura kwallaye 20 a kakar wasa ta shekarar 2019 zuwa 2020, inda ya yi kan-kan-kan da Thierry Henry wanda ya fara bajintar a kakar Premier League.

Wasan da aka zazzaga kwallaye a Premier League ta bana a gida shi ne wanda Aston Billa ta doke mai kare kambu wato Liverpool mai rike da kofi da ci 7-2 a wasan da suka fafata ranar 4 ga watan Oktoba.

A kuma ranar ce kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta je har filin wasa na Old Trafford ta doke Manchester United da ci 6-1, kuma shi ne wanda wata kungiya ta je waje ta ci kwallaye da dama a bana.

‘Yan wasan da ke kan gaba wajen bayar da kwallo a zura a raga a shekarar 2020 zuwa 2021:

Harry Kane -6

John McGinn -3

Jack Grealish -3

Daniel Podence -2

Richarlison -2

Willian -2

James Rodriguez -2

Roberto Firmino -2

Pablo Fornals -2

Matheus Pereira -2

 

Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a gasar Premier ta bana:

Dominic Calbert-Lewin -Everton FC -6

Heung-min Son -Tottenham -6

Mohamed Salah –Liverpool -5

Jamie Bardy -Leicester City -5

Callum Wilson -Newcastle -4

Neal Maupay -Brighton -4

James Rodriguez -Everton FC -3

Jorginho –Chelsea -3

Danny Ings -FC Southampton -3

Harry Kane -Tottenham -3

Sadio Mane –Liverpool -3

Ollie Watkins -Aston Billa -3

Wilfried Zaha -Crystal Palace FC -3

Alexandre Lacazette -Arsenal FC -3

Jack Grealish -Aston Villa -3

Patrick Bamford -Leeds United FC -3

 

Wasannin mako na biyar:

Ranar 17 ga Oktoba, 2020

Everton da Liverpool

Chelsea da Southampton

Manchester City da Arsenal

Newcastle United da Manchester United

Sheffield United da Fulham

 

Ranar 18 ga watan Oktoban 2020

Crystal Palace da Brighton & Hobe Albion

Tottenham da West Ham United

Leicester City da Aston Billa

 

Ranar 19 ga watan Oktoban 2020

West Bromwich Albion da Burnley

Leeds United da Wolberhampton Wanderers

 

Exit mobile version