Su Waye Suka Tsine Wa Arewacin Kasar Nan?

Tsine wa

Kwamared Sunusi Mailafiya.  alimailafiyasunusi@gmail.com – 08036064695

Nasan kalmar tsinuwa za ta zo da rudani musamman ganin cewa mummumar kalma ce a hausance. ‘Tsinuwa’ tamkar la’anta ce ko kuma neman kar abu ya yi albarka. Kuma ana iya cewa duk wanda aka cewa an tsine masa tamkar ya rasa albarka ne. To kusan hakan take akan Arewacin kasar nan idan har ka bibiyi tarihi, musamman irin albarkar da wannan yanki ya samu tsakanin yankunan kasar nan abaya, kusan koda turawa suka zo mulkin mallaka, sun tarar Allah (S.W.T) ya albarkaci Arewacin kasar da tsarin Shugabanci da Sana’o’in su, wato dai dama can yankin mai tarin albarka ne da tsari, amma nida kai/ke/ku munsan yanzu yankin shine koma baya idan aka hadashi dana Yarabawa da Inyamuran Kasar nan, yanzu yankin shine abin tausayi da neman taimako saboda yadda yashiga tasku da kakanikayi, mune cikin matsalar Shugabanci, mune cikin matsalar tsaro, talauci, wuta, ruwa, ilimi mune duka akan gaba wajen kuka da rashinsu, shin ina albarkar da kakanninmu da iyayenmu suke gaya mana, wannan shine abin tambayar, shin waya tsinewa Arewacin kasar daga kyakykyawar rayuwa zuwa kakanikayi, ta lalace kuma ta balbalce har haka? Sannan abin tambayar anan shin su wanene suka jefa yankin a cikin halin da yake ciki yanzu?

Idan muka dubi tarihi. Yankin arewa yafi kowane yanki a kasar nan dinbin arziki abaya, mune muka wadata da arzikin ‘Dalar Gyada’ wacce ita kadai ta rike yankin da makotansa, dalar gyada tazama daya daga cikin hanyar samun kudin shiga mai yawa ga kasar nan. Noman gyada yasamu babban tagomashi da babu rashin abinci a wannan lokaci, babu fatara ballantana yunwa, har takai Arewacin kasar ne ke siyar wa babban kamfanin kasar Ingila gyada don sarrafawa (Royal Niger Company) a lokacin. Shin yanzu ina wannan arzikin?  Koda manyan attajiran wannan lokacin irinsu Marigayi Alhasaan Dantata da suka gargadi kasar nan cewa indai har Arewacin kasar ya wancakalar da noma, to sai anyi babban danasani. Yau gashi abin kunya, wai Arewacin kasar ne yake cikin yunwa, wai yau mutanen Arewacin kasar ne abinci sau uku a rana yake gagarar mutanen cikinsa, an kashe noma ayankin, anzo an kashe manyan jihohin da ake alfahari dasu a kasuwanci a yankin.

Manyan kamfanunnukan da suke ciyar da Arewa, suka zama ginshikin sana’a ga mazaunan yankin, suma anyi musu korar kare, yau ina Aba Textile Mills, ina Afprint, ina Arewa Textile Mills ina Gaskiya Textile Factory, dukansu mallakin yan Arewacin kasar ne, yau suna ina?. Amsar ita ce sun zama tarihi, shiyasa kullum matasa ke kukan rashin sana’a, zaman banza da shaye-shaye.

Idan ka koma bangaren Shugabaci da Siyasa. Arewacin kasar shi ne ginshikin duk wani ci-gaba na kasar nan, mune mukafi kowane yanki ko yare samun damar Shugabanci a kasar, amma abin bakin ciki har kawo yanzu ba zamu iya cewa hakan yai mana wata babbar rana ba. Daga mutuwar su Sardauna (Allah ya rahamshesu), daga 1966 zuwa yau Shugabannin kasa na soja dana hula guda 9 muka yi ‘yan yankin arewa, sannan atsahon shekaru 53 da aka yi ana mulki a kasar nan, mune muka yi shekaru talatin da bakwai (37) muna mulkar kasar, ya yin da yan uwanmu na kudu suka yi shekaru sha shida (16) kacal, amma shin wace gudummawa zamuce muna alfahari da ita. Har yau a Arewacin kasar nan ana kukan rashin hanyoyin sufurin kasa, kuce daya, muna kukan rashin wadatattun makarantun boko, kuce biyu, har yau muna kukan asibitioci, likitoci, malamai, shi kansa ilimin har yau mune komabaya a cikinsa, har yau mune muke kukan rashin wuta da ruwa, mune muke kukan rashin tsaro, kasuwanci, banda kukan yunwa, fatara da bakin talauci.

Shin yaushe ne mutanen Arewacin kasar zasu gane ainihin abinda ke damunsu, yaushe ne zamu gane suwaye Shugabannin daya kamata mu zaba don su wakilcemu. Ayau takai cewar yan kudancin kasar nan na mana gorin cewa duk talaucin da za suyi, bazai sa suyi bara ba. Wannan babbar izina ce garemu musan cewa an cutar da arewa, an cutar da MATASAN yankin, an sace kudin kasar da sa hannun yan Arewa, an hanamu duk wani kayan more rayuwa, an sanya mana talauci, lalaci da kiyayya a tsakanin junanmu musamman ta fuskar siyasa da muka kasa hada kanmu don samowa kanmu bakin zaren.

Yanzu ya rage matasan yankin dasu tashi tsaye don dawo da martabar yankin namu. Dole ne mu koyi sana’o’in hannu don daina dogara da Gwamnati, dole mu samowa kanmu mafuta. Masu akidar bokon cikinmu dole ne mu tsaya musu don kaiwa kowane irin mataki don samun dama a kasar nan, haka masu kishin siyasa dolene mu tsaya musu don ganin mun fara yiwa tsofaffin nan ritaya a siyasa, mu tsaya da kafarmu don kwatowa yankin da kasar daga mutuwar rabin jiki da take ciki wanda idan har ba’a dauki matakan gaggawa ba, tabbas za a iya rasata.

Dole ne Jagororin Arewa su tsaya kai-da-fata wajen ganin waccan tsinuwar da ni ke tunani, to ba gaskiya bane. Domin ibtila’in da muke ciki a yanzu, ya yi dai-dai da wanda yake cikin dimauta da jarabta ta rayuwa, babban abin damuwar shi ne yadda tsahon shekaru kullum abubuwan sai gaba suke yi, madadin su dinga yin baya ana samun masalaha. Mafi muni yadda yan bindiga dadi suke ta kashe al’ummar Arewar, wanda da yawa manoma ne da makiyaya da suke tallafawa rayuwar al’umma yau da kullum.

Allah Ya dawowa da Arewa martabarta. Ameen.

 

Exit mobile version