Abba Ibrahim Wada" />

Suares Ya Karya Tarihin Cristiano Ronaldo A Laliga

Suarez

Ranar Litinin Atletico Madrid ta tashi wasa 2-2 da kungiyar kwallon kafa ta Celta Bigo a karawar mako na 22 a gasar La Liga kuma tsohon dan wasan kungiyar Liverpool da Barcelona, Luis Suarez shi ne ya ci mata kwallayen gaba daya.

Kwallon da ya ci ya sa ya haura tsohon dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo a lokacin da ya buga wasa a Sifaniya sannan kawo yanzu Luis Suarez ya ci kwallo 16 a wasanni 17 da ya buga a kakar bana ta La Liga tun bayan da ya koma kungiyar daga Barcelona.

Tsohon dan wasan na Ajad da Liverpool shi ne na farko da ya ci kwallo 16 a wasanni 17 a La Liga a karni na 21 sannan a baya Cristiano Ronaldo ne ke rike da wannan tarihin na zura kwallaye 15 a wasanni 17 a La Liga a lokacin da ya buga wasa a Real Madrid, wanda ya koma Jubentus daga baya.

Atletico wadda ke da kwantan wasa daya tana jan ragamar teburin La Liga da maki 51, sai Barcelona ta biyu mai maki 43, sannan Real Madrid mai maki iri daya da na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.

A kwanakin baya kociyan kungiyar Atletico Madrid, Diego Simeone, ya bayyana cewa dan wasan kungiyar na gaba, Luis Suares, zai iya zama dan wasan da yafi yawan zura kwallaye a raga a kakar wasa ta bana da ake bugawa.

Luis Suarez ya ci kwallo 16 a wasanni 17 da ya buga a gasar La Liga, ya yin da  aka shiga karawar mako na 22 kuma dan kasar Uruguay din ya yi wannan bajintar a Atletico Madrid a karon farko tun bayan rawar da Radamel Falcao ya taka a baya.

‘Yan wasan Atletico da suka ci kwallo irin wanda Suarez ya zura a raga a bana sun hada da Christian Bieri a kakar wasa ta 1997 zuwa 1998 sai dai kafin shi akwai dan wasa Pruden da ya yi wannan kwazon a kakar wasa ta shekarar 1940 da kuma Baltazar da ya yi hakan a shekarar 1980.

Kuma dukkan ‘yan wasan ukun na Atletico Madrid su ne suka lashe kyautar takalmin zinare a Spaniya a matakin wadanda suka fi cin kwallaye a raga a kakar hakan yasa Simeone yake ganin wannan shekarar ma Suares zai iya kafa irin wancan tarihin.

Suarez ne kan gaba a cin kwallo a gasar La Liga a bana, idan ya lashe takalmin zinare zai zama dan kwallon Atletico Madrid na farko da ya yi hakan tun bayan Diego Forlan a shekarar bayan ya koma kungiyar daga Billareal 2009.

Exit mobile version