Khalid Idris Doya" />

SUBEB Ta Hana Wazifa A Makarantun Tsangayar Bauchi

-Ku Daina Yi Mana Izgili Da Addini –Shehi Dahiru Bauchi

-An Hana Ne Don Babu A Tsarinmu –Shugaban SUBEB

Gwamnatin Jihar Bauchi ta hannun hukumar kula da ilimin bai daya na jihar Bauchi wato SUBEB ta umurci makarantun Tsangaya da su dakatar da yin wazifa ko kuma karanta Salatil Fatihi a cikin hidimar makarantar, a cewar hukumar yin hakan bai daga cikin tsarin koyarwar makarantun Tsangaya a fadin Jihar ta Bauchi da ma tsarin da hukumar UBEC ta fitar kan karatun Tsangaya.

Bayanin hakan na kumshe ne a cikin wata takarda wacce shugaban hukumar SUBEB Yahaya Ibrahim Yero ya fitar wanda wakilinmu ya samu kwafinta, dauke da sanya hannun Mahmood A. Kari, wanda shi ne sakataren hukumar SUBEB, wacce aka yi mata kwanan wata da 5 ga watan Fabrairu, wasikar dakatar da wazifa da salatil fatihi mai addireshi kai tsaye zuwa ga Shugabannin makarantun Tsangaya-Tsanya da suke fadin Bauchi.

Yahaya Yero ya ce; “Ina mai shaida muku cewar hukumarmu ta samu muhimman wasikun korafe-korafe daga bangarorin jama’a da iyayen daliban da suke karatu a makarantun Tsangaya kan yadda ake tafiyar da Tsangaya a cikin Bauchi,”

SUBEB din ta yi bayanin cewar ta samu korafin cewar ana tilasta wa dalibai yin wazifa da salatil fatihi “kamar yadda suka shaida, Wazifa da Salatil Fatihi ana tilasta wa dukkanin daliban makarantar Tsangaya yinsu, don haka ina mai shaida muku cewar wannan bai daga cikin tsari ko manhajar koyarwa a makarantun Tsangaya na Bauchi”.

“Don haka, a bisa wadanan dalilin daga yau, muna sanar da ku cewar mun dakatar mun kuma hana aiwatar da irin wannan aikin ko koyarwar wanda ya saba wa tsarin da aka shimfida wannan makarantun da su”.

“Babu wani malami ko dalibi da yake da ikon tilasta wa wani yin salatin fatihi ko wazifa”.

Daga bisani ne wasikar ta bukaci wadanda abin ya shafa da su amshi wannan mataki na Shugaban SUBEB kan dakatarwa da yin wazifar da salatin fatihi da matukar muhimmanci.

Wannan matakin dai kai tsaye ba ta yi wa babban Malamin Darikar Tijjaniyya kuma mamallakin wannan makarantar Tsangayar Shehu Dahiru Bauchi dadi ba, haka su ma magoya bayansa suna ganin wannan matakin tamkar cin fuska ne kai tsaye ake yi wa babban malamin nasu, a bisa haka ne ma Shehu Dahirun ya fito balo-balo a bainar jama’a ya yi suka kan lamarin hade da tambayar gwamnati kan dokar da ta baiwa kowani dan kasa iko da dama hade da zarafin yin addininsa yadda ya fahimta ba tare da tsangwama ba.

A bisa wannan dalilin ne LEADERSHIP A Yau ta tuntubi Shehu Dahiru Usman Bauchi don jin ta bakinsa kan wannan batun, Shehin ya bayyana cewar akwai ayar tambaya kan wannan batun, inda ya ce, abu na farko shin da gaske gwamnati ce ta aike da wasikar ko wasu wadanda ake kiransu ‘yan Izala? ya ce “wasu ‘yan Izala sun yi taro sun ce sune suka hau da Buhari mulki, kuma suna da ikon su sauke duk wanda suke so a mulki, haka suka ce Buhari dan uwansu ne,” kamar yadda ya shaida.

Ya kara da cewa, “Tun da suka fara hana wazifa da salatil fatihi a makarantu suna son su tabbatar da cewar gwamnatin ta Izala ce, mu kuwa mun zauna da gwamnatin Turawa ba ta hana mu yin wazifa da salatil Fatihi ba; balle gwamnatin farar hula ta ‘yan kasa”.

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce sun tambaya amma an ce musu ba gwamnati bace ta hana wannan “an yi dokar hana salatil fahiti da wazifa a Nijeriya ne ba a gaya mana ba? don haka ka ga wannan ba daga gwamnati ya fito ba. kawai dai ‘yan Izala ne ke wannan ‘Propaganda”.

Dahiru Bauchi ya ce ‘yan Izala sun ci mutuncin mutune uku a Nijeriya “yanzu dukkanin kiristocin da ba ‘yan Izala ba; da suka zabi Buhari ka ga ‘yan Izala sun ci mutuncinsu, sauran musulman da ba ‘yan Izala ba suma haka, sai kuma na uku wadanda suke su babu ruwansu da kowace bangare da suka zabi Buhari, an zo an ce Izala ne suka kawo gwamnatin Buhari”.

Shehu Dahiru, ya ce, Izala suna son su sake jawo wa Nijeriya wani tashin hankali ne, duba da yadda ake tsaka da rikicin Boho Haram, Masu garkuwa da mutane, rikicin ‘yan Shi’a da kuma rikicin makiyaya da manoma wanda har yanzu kasar take tsaka da mashashsharansu ba tare da shawo kansu ba “irin wannan zai jawo tashin hankali fiye da kowace irin tashin hankali, ka nemi ‘yan Tijjaniyya muna da yawa a fadin kasar nan fiye da kowace bangaren masu taro; mu ba kungiya bane, mu jama’a ne masu addini. an kara da ‘yan shi’a wannan tashin hankalin bai kare ba, ga shi tsakanin manoma da makiyaya ba ta kare ba, masu kashe mutane a Zamfara da sauran wurare suna kai, masu gurkuwa da mutane suna kai; yanzu kuma su ‘yan Izala suna son su suke kara wa gwamnatin wani tashin hankali; domin mu tashin hankalinmu ya fi na kowaye a Nijeriya,” a cewarsa.

Bauchi, ya ce, su ’yan Tijjaniyya ba su cakalar gwamnati ko wani bangare “mu muna da yawa, babu wanda ya isa ya iya kashe mu da bindigoginsa”.

Dahiru ya ce maganar hana wazifa ko salatin fatihi ai wasa ne domin kuwa babu wanda ya isa ya hana wannan lazumin “mun yi rayuwa da gwamnatoci ciki har da na soja, basu iya sun hana mana zikiri ba, sai a gwamnatin Buhari ta ‘yan Izala tace za ta hana wannan ai wasa ne. kuma Buhari bai isa maida gwamnatin nan ta Izala ba, babu wanda ya isa ya maida gwamanati ta bangarensa ko ta musulmi ko ta kirista, idan ma ya maida kansa dan Izala ya maida gwamnatinsa ta Izala bai isa ya hana mana wazifa da salatin fatihi ba; domin dokar yin addini yadda mutum ya fahimta dokar duk duniya ce ba wai a kasa kawai ba,”

Dangane da kiransa ga mabiyansa wadanda wannan mataki ya hassala ko ya bata wa rai, Shehin ya shaida musu cewar babu wani abu da za su yi domin su a bangarensu ba masu tayar da hankali ko kuma sukar gwamnati ba ne, don haka ne ya bukaci su kwantar da hankalinsu “ai wannan abin ma ba zai iyu ba ne. misali yanzu idan aka zo zabe muka ce wa mabiyanmu kada su zabi mutum iri kaza ko mutum kaza duk ihun da ‘yan siyasa suka je suka yi ta yi wasikarmu daya tak ta isa ta rushe dukkanin shirunsu, wasika daya idan muka rubuta muka ce su wane makiyanmu ne kada a zabesu da mu da mabiyamu har wadanda ba su Darika za su bi mu,”

Malamin ya shaida cewar bai kamata wasu su zura ido su bari wasu na neman kunno wuta a Nijeriya ba, ya kirayi bangarorin jami’an tsaro da yi aiki da kwarewarsu domin daidai matsalolin da suke akwai.

Idan aka ce SUBEB ba gwamnati ba ne jama’a za su shiga dan wani wasu-wasi domin ai hukuma ce ta gwamnati, ko za ka yi karin haske? Tambayarmu, ya amsa da cewa babban malamin Tijjaniyar “eh, SUBEB gwamnati ce, amma ba gwamnatin tarayya ba; ba kuma ita ce mai zana dokokin Nijeriya ba; su suna kura da wasu fannoni ne na karatu, to amma kowa ya samu dama sai ya nemi yin.. a cikinsu wani wanda ake kira da suna Yahaya Ibrahim Yero din nan shi ne mai tayar da rikici, shi ne ya sa da gwamnatin baya ta koreshi a lokacin da ya yi yunkurin kawo rikici a Misau, wannan sabowar gwamnatin ne ta sake dawo da shi”. A cewar Malamin Tijjaniyar.

Ya ce, “ko ba gwamnatin Buhari ba, wallahi babu gwamnatin da ta isa ta hana wazifa da salatin fatihi ba, babu gwamnatin idan akwai gwamnatin da take yunkurin haka ta gwada ta gani, ba tada hankali zamu yi ba, za su gani”. A cewarsa.

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan batun, Khalifa Ibrahim Shehu Tahir Bauchi shugaban Gidauniyar ta makarantun Alkur’ani na Shehu Dahiru Bauchi a Nijeriya gabaki daya ya bayyana cewar “wannan batun hana salati da wazifa gaskiya ba a yi adalci ba, kamar yadda muke sanar da jama’ar mu cewa batu ne bana gwamnati ba ne, kawai na shugaban hukumar SUBEB ne wanda kowa daman ya san halinsa, domin a lokacin da yake Misau ma ya taba hana maulidin Manzon Allah a makaranta, yanzu kuma don ya ce a daina salatin fatihi da wazifa fadinsa ne kawai, ba za a daina ba, za a ci gaba da yi”.

Sayyid Ibrahim ya ci gaba da dace “a irin wannan dalilan ne fa muke cewa da wani mai sallar gwamma wanda bai salla, wanda baya salla ba zai cakole ka akan harkar addininka ba, ka ga mutum yana sallah amma zai yi yunkurin takura maka akan addininka, amma wancan baya sallah amma bai rabaka da wani abu da kake yi na addininka ba, don haka idan aka ce ka zabi wani zaka zabe wancan ne,” a cewarsa.

Ya kara da cewa, babu wani zamanin da zai zo ya ci karo da hdimar addininsu don haka ne babu wani yunkurin zamanantar da makaranta da zai sanya a hana wazifa ko zikiri gami da wazifa don haka ya ce maganar da ake yi na cewar ana tilasta wasu yin karatun salatil fatihihi da kuma wazifa babu wannan shirin “Muna kira ga gwamnatin jihar Bauchi ba wa wannan mutumin ne kadai farfesa ba, a nemo wani wanda ba zai haifar da rikici ba a ba shi wannan kujerar ya shugabanta, ba a tilasta wa babba ba balle wa yaro? Dukkanin wani uban da ya kawo yaronsa wannan makarantar ya amince da tarbiyyar da ake basu ne,”

“wannan abin gaskiya akwai tsokana a ciki, amma mu dadinmu ainuhin gwamnati bata san da wannan abin da ake ciki ba, wannan dalilin ne ya ke ta tayar wa mabiyanmu da hankali, domin idan ka duba kafafen sadarwar zamani za ka gani ana ta yawo da wani mutum wai sune suka yi Buhari, gwamnatin ta Izala ne, wannan karya ne domin gwamnati ta ‘yan Nijeriya ne, babu wanda ya isa ya hana mu yin addininmu”.

Shehu Ibrahim ya ci gaba da cewa ‘yan Izala ne suke shissige wa jikin Buhari don haka ne ya bayyana cewar ya kamata Buhari ya yi kaffa-kaffa da masu neman haifar masa da rikici da tashin hankali.

Dangane da kiransa ga gwamnatin kan makarantun Tsangaya ya bayyana bukatar da ke akwai gwamnati ta sake izinin gudanar da komai ga hannun wadanda suka dace ta dauke lamarin daga hannun wadanda suke jin kansu gwamnati ne “ya kamata gwamnati ta tauyasa mana, wa mu aka yi makarantun Tsangayar nan, saboda haka idan da adalci a cikinmu ne ya kamata a nemo irinmu-irinmu, tun da akwai irin almajiranmu da suka yi Bokon a dibosu a zuba su kan lamarin gwamnati da tsangayar mana, domin ka zo ka ce makarantu na tsangaya ka zo ka dauko wanda bai san harkar ba, kawai ya je ya karanta ne a littafi ka zo ka bashi ta yaya ne al’amura za su yi kyau? Idan gwamnati tana son komai ya tafi daidai ta nemo almajiran ta basu tsangaya domin su tafiyar da harkar”. A cewar Khalifa.

Ya bayyana cewar, ko a gwamnatin baya har aka kammala tsare-tsaren lamarin tsangaya babu wani almajiri a ciki “wannan gwamnatin ne ma da ta zo ita UBEC ta fara nemanmu ana tattaunawa, harkar tsangaya namu ne, a bamu kayanmu kawai idan gwamnati tana son gyara lamari, in ba a yi hakan ba kuma za a ci gaba da zama ana yawo ana bara, mune yaranmu suke bara, mune yaranmu suke almajiranci suke karantun tsangaya, don haka mune ya kamata a bamu lamarin mu ci gaba da gudanarwa domin muna da wadanda suka zama farfesoshi da sauransu wadanda almajiran ne kuma”

Khalifa ya kara da cewa, “in ban da rashin kunya, kamar su iyayenmu Shehu Dahiru Bauchi wai da su ne za ka zo in-ce-in-ce da su akan hidimar addini?, ai tsoho kam ko ba na addini ba, aka ce ka girmama shi, amma shi wannan Yero da gwamnatin Bauchi suna ganin kamar za su saka mana bakin ciki wallahi basu isa ba, komai ya faru da mu Allah ne mai yi mana maganinshi”. A cewar Shehu Ibrahim.

Khalifa, Ya nanata batun cewar gwamnatin Buhari ba ta Izala ba ce, don haka ya bukaci wadanda abin ya shafa da su hanzarta shawo kan matsalolin da suke akwai dangane da batun Tsangaya domin cire baragurbi masu neman kawo rudani.

A hirarsa da manema labaru kan wannan zargin da bangaren darikar suka yi a kan shugaban hukumar ilmin bai daya Yahaya Ibrahim Yero na cewar yana kokari Izalantar da dalibar ta barauniyar hanya, don haka ne ya kira wani taron manema labaru a ranar Litinin inda ya bayyana cewar wannan maganar babu gaskiya a ciki.

Yero ya bayyana cewar ko kadan shi bai da wani yunkuri na maida kowani dan makarantar Tsangaya Izala, yana mai bayanin cewar sun aike da sako wa kowani shugaban makarantar tsangane bayan samun korafe-korafen da hukumarsa suka yi daga bangarorin jama’a da kuma wasu bangarorin iyayen yara, yana mai bayanin cewar “wasu iyaye sun kawo mana korafin cewar ana tilasta wa ‘ya’yansu yin wazifa da salatil Fatihi a dukkanin bayan sallar magriba da Ishah, wanda kuma hakan bai daga cikin tsarin koyawar wannan tsangayar”.

“kowani dan kasa yana da ikon ya yi addininsa yadda ya fahimta ba tare da an tauye masa hakki ba, don haka mu bamu hana kowa yin addininsa ba; maganar wai da ni da ma’aikatana muna kokarin tilasta kowani dan makarantar tsangaya da su zama ‘yan Izala wannan maganar ba gaskiya ba ne” .

“Don haka ne muka bayyana cewar dukkanin wani abin da bai daga cikin manhajar kowayar a makarantun Tsangaya mun tsaya kan da fata ba za mu taba bayar da kofa a shigo da wani abu ba, don haka muna sanar da cewar muna da takardun da hukumar UBEC ta shimfida kan manhajar koyarwar karatun tsangaya”. A cewar Yero.

Dangane da wasikar da suka aike wa dukkanin makarantun tsangayar da fadi jihar, Yero ya ce suna nan a kan bakarsu ba za su taba barin ana shigo da abubuwan da basu cikin wannan mahanjar na koyarwa na tsangaya a fadin jihar ta Bauchi.

 

Exit mobile version