Sukar Shugaba Buhari Kan Zuwa Binuwai Tsabar Jahilci Ne -Gwamna Ortom

Gwamnan Jihar Binuwai Samuel Ortom,  ya bayyyana  wasu ‘yan Nijeriya masu sukar Shugaba Buhari kan kin zuwa Jiharsa ta Beniwe sakamakon barkewar anbaliya ta ruwa da ya faru a ranar 27 ga watan Agustan wannan shekara, a matsayin wadanda ke bayyana jahilcin a fili.

Ortom ya yi nuni da cewa masu yin wannan suka wata alama ce ta karancin ilmin yadda ake tafiyar da harkar mulki. Gwamnan ya bayyana bacin ran nasa ne a hirar da ya yi da kafar yada labarai ta Primium Times da ke gidansa na gwamnati a Makurdi babban birnin jihar.

Ortom, ya ci gaba da cewa, Buhari bai yi kasa a gwiwa ba lokacin da rahoton ambaliyar ruwan ya riske shi.

Ya ce, “da abin ya faru, na umarci Darakata Janar na Hukumar Bada

Agajin Gaggawa ta Kasa, inda shi kuma ya sanar da Shugaban Kasa.”

Ya bayyana cewa, ana sanar da Shugaba Buhari ya umarci Shugaban na NEMA, da ya wuce kai tsaye zuwa jihar, inda bayan kwana daya aka turo da kayan agaji.

Ortum ya yi nuni da cewa, sukar rashin fahimta ce kawai, domin kuwa,

mataimakin Shugaban Kasa da kansa ya zo jihar don jajantawa wadanda abin ya shafa da kuma gwamnatin jihar, inda kuma ya tabbatar masu cewa, Gwamnatin Tarayya za ta taimaka.

Ya ci gaba da cewa, wadanda ma suke yin sukar, ba ‘yan asalin jihar ba ne, abin da ya haifar da sukar shi ne, rahotannin da wata kafar yada labarai ta buga cewar, Shugaba Buhari bayan kammala Shagulgulan Sallah babba da ta wuce a jiharsa ta Katsaina,  zai  wuce ne zuwa Kasar Amurka don amsa goron gayyatar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi masa tun a cikin watan  Fabrairun wannan shekara. An ruwaito cewa, mutane da dama sun rasa muhallinsu kimanin 110,000 a sanadiyyar ambaliyar ruwan.

Exit mobile version