Daga Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
A karon farko a tarihi dan asalin Jihar Sakkwato ya samu nasarar zama babban lauya mafi kwarewa, gogewa da sanin makamar aiki (Senior Advocate of Nigeria) SAN.
Barista Sulaiman Usman shine Babban Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Sakkwato daga 2015 zuwa yau ya kuma samu kaiwa ga kololuwar matsayin aikin lauyanci a yayin da Kwamitin musamman na mahukunta shari’a wato ‘Legal Practitioners Pribileges Committee’ (LPPC) ya bayyana nasarar da lauyoyi 30 suka samu na zama manyan lauyoyi na Nijeriya.
Babbar Magatakarda ta Kotun Koli Hadizatu Mustapha ce ta fitar da wannan sanarwar a Abuja a kwanan nan a yayin da take yi wa manema labarai bayanin karshen taro na 127 da suka gudanar. An dai fara bayar da lambar girma ta SAN a shekarar 1975.
Mustapha wadda ita ce Sakatariyar Kwamitin LPPC kwamitin da Babban Mai Shari’a na Nijeriya ke jagoranta ta bayyana cewar mutane 156 ne suka gabatar da bukatar neman babban matsayin, yayin da 123 suka cancanta da shiga cikin matakin farko na gwaji.
A bayanin ta, ta ce lauyoyi 72 ne suka tsallake gwajin mataki na karshe yayin da 26 sun fito ne daga fannin aikin lauyanci, yayin da hudu daga ciki suka fito daga fannin koyarwa.
Tsohon Mashawarci na Musamman ga Jam’iyyar PDP Olusola Oke yana daga cikin sababbin kusurguman manyan lauyoyin da kuma Kwamishinonin Shari’a na Jihohin Kwara da Jigawa Kamaludden Ajibade da Sani Husaini Garun- Gabas.
Daga ciki Lauya Festus Keyamo wanda sau tara yana gabatar da bukatar kaiwa ga wannan matsayin amma ya kasa samun nasarar kaiwa ga wannan matsayin a yanzu yana cikin sababbin SAN 30. Haka kuma Oluwatoyin Bashorun ita ce kadai ce mace da kwamitin ya aminta da zamanta babbar lauya daga cikin lauyoyi biyar mata da suka nema.
Sauran sune Chibuike Adindu Nwokeukwu, Johnnie Nnaemeka Egwuonwu, Bert Chukwuneta Igwilo, Sylbester Emenike Elema, Ikenna Bictor Egbuna, Wilcod Achace Abereton, Michael Abayomi Bisade Aliyu, Akinlolu Oluyinka Osinbajo da kuma Francis Egele.
Sauran sun hada da Farfesa Enefiok Effiong Essien, Farfesa Sadik Slybester Shikyl, Farfesa Adebambo Anthony Adewopo, Farfesa Adedeji Olusegun Adekunle, Olusola Aled Oke, Nasser Abdu Dangiri, Emeka Peter Okpoko, Abdul Atadoga Ibrahim, John Olusegun Odubela, Gboyega Sanmi Oyewole, Joshua Yusuf Musa, Ibrahim Sani Mohammed, Ekemejero Ohwoboriole, Oyetola Oshobi, Kehinde Olamide Ogunwumiju da kuma Chiesonu Igbojamuike Okpoko.
Kwarewa da lakantar makamar aikin shari’a duk su kan tabbata ne a karkashin basira, kamanta gaskiya, adalci da rikon amana. Masana shari’a da wadanda suka tsinci kansu a gaban manta sabo duk suna da cikakkiyar masaniyar cewa a fannin sanin shari’a da rikon amanar wadanda bukatar aikin lauya ta kama duk suna farin cikin kulla hulda da Barista Sulaiman Usman.
Kwararren lauyan mutum ne wanda abokan huldarsa kan yi masa lakabin gaskiyarka ta fissheka ko gaskiya ba ta zuwa marina. Tabbas hakan ta tabbata har a matakin Tarayya domin daga cikin kwararrun lauyoyi 72 da suka tura bukatar zama SAN sunan Sulaiman Usman ya bayyana a matsayin SAN na farko da ake da shi a Sakkwato.
Sabon gogaggen lauya Sulaiman Usman wanda ya fito daga Karamar Hukumar Mulkin Kware ya kasance Mashawarci na Musamman ga Gwamnatin Attahiru Bafarawa kan Sha’anin Shari’a daga watan Satumba 2003 zuwa Nuwamba 2006.
Barista Sulaiman Usman ya samu digirin sa na farko a aikin Lauya LLB Common & Islamic Law (Combined Honours) a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato daga shekarar 1993 zuwa 1998.
Bugu da kari fitaccen lauyan ya kuma fadada karatun sa a digiri na biyu a Jami’ar Liberpool da ke kasar Ingila daga shekarar 2009 zuwa 2012. Lauyan ya zama wakili a taron Tattauna Makomar Kasa (National Reform Conference) Abuja a 2005.
Gabanin zamansa Babban Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a shine Jagoran Cibiyar Aikin Lauya ta Gamzaki Law Chambers wadda ke da mazauni a Abuja da Sakkwato wadda kuma ta yi fice tare da samarwa kanta suna a matsayin ofishin nagartattun lauyoyi wadanda ke gudanar da aiki na kwararru cikin gaskiya da amana.
Sulaiman Usman SAN ya jagoranci samun nasara a mabambantan shari’u tun daga karamar kotu har zuwa Kotun Koli a aikin da aka tabbatar da cewar ya ji gishirin gudanar da shi yadda ya kamata. Bugu da kari lauyan ya rubuta littaffai da dama kan fannin da ya fi iyawa, wayo da lakanta.
A matsayinsa na Kwamishinan Shari’a ya jagoranci canza fasali da daga darajar Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Sakkwato ya kuma dauki sababbin lauyoyi 20 aiki baya ga lauyoyi 56 da ke ga ma’aikatar sa.
Duka baya ga wannan a matsayinsa na Babban Lauyan Gwamnati wanda ke da kwarewa da gogewa tare da sanin ciki da wajen aikin Shari’ah, a kashin kansa Barista Sulaiman Usman ya samu gagarumar nasara a shari’u daban-daban da ke gaban Gwamnatin Jihar Sakkwato har guda 15 kama daga Kotun Koli, Kotun Daukaka Kara da Manyan Kotuna.
A karkashin ikonsa, wasu daga cikin dokokin da Gwamnatin Tambuwal ta samu nasarar zamansu doka bayan amincewa daga Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato, sun hada da Dokar Hana Aikata Miyagun Laifuka A Komfuta Da Duniyar Gizo, da Dokar Kirkiro Hukumar Bunkasa Kanana da Matsakaitan Masana’antu (SOSMEDA) da Dokar Kafa Hukumar Zakka da WaKafi da kuma Dokar Kafa Hukumar Kula Da Makarantun Sakandare, da Dokar Ritaya Daga Aiki A Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Umaru Ali Shinkafi da Kwalejin Nazarin Shari’ah da Addinin Musulunci da Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, da Dokar Kafa Hukumar Kula Da Sayen Amfanin Gona da sauran dokoki da dama, baya ga Dokar ‘Yancin Ilimi ta 2016 wadda tana daya daga cikin muhimman nasarorin Gwamnatin Tambuwal.
Ma’aikatar Shari’a ta Sakkwato daga watan Mayu na shekarar 2015 zuwa yau ta karbi miyagun laifuka daban-daban har 163 domin bayar da shawara. Daga ciki an sallami 23 saboda karancin shaidu, yayin da aka gabatar da laifuka 140 a kotuna daban-daban wadanda ke da hurumi, 17 daga ciki an kammala su a dalilin hukuncin kisa, dauri a kurkuku ko kuma tara. Sauran kuwa suna nan ana fafatawa a kotunan da ke cikin jiha da kuma kotun daukaka kara.
Tuni dai lauyoyi da abokan aiki a ciki da wajen fannin shari’a tare da ‘yan uwa da abokan arziki suka fara yi wa Barista Sulaiman SAN murnar sabon matsayin da ubangiji ya bashi tare da yi masa fatar gamawa lafiya.