Connect with us

LABARAI

Sulhu Da Mahara Ya Dakile karfin ’Yan Ta’ada A Zamfara – Hon. Hassan

Published

on

Shugaban Kwamitin yada labarai na Majalisar Dokoki ta Jihar Zamfara, Hon. Shamsudini Hassan, mai wakiltar karamar hukumar Talata Mafara a majalisar, ya bayyana cewa, sulhu da gwamnatin jihar ke yi karkashin jagorabcin Gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun da mahara ya taimaka wajen dakile karfin ‘yan ta’addan da su ka addabi jihar.

Hon. Shamsudini ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a zauren majalisar da ke Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara.
dan majalisar ya kara da cewa, kafin shekara da zuwan wannan gwamnatin al’ummar Jihar Zamfara na cikin mawuyacin hali na fargabar hari ga mahara ko masu garkuwa da mutane.
“Sakamakon damar da Majalisar Dokokin Jiha ta ba wa Gwamna Bello Muhammad Matawalen Maradun na daukar duk matakin da yakamata a kan samar da tsaro, lallai kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.
“Don yanzu haka mun samu nasara dakile ta’addancin ‘yan ta’ada kashi 80%, al’ummar garuruwan da su ka kaurace wa garuruwansu sama da 250 sun koma garuruwansu, kuma sama da mutane 500 ne gwamnati ta amso daga hannun masu garkuwa da mutane. Wannan babbar nasara ce gare mu,” in ji dan majalisar.
“A kan haka mu ke kira ga al’ummar Jihar Zamfara da su cigaba da mara wa kudirorin gwamnatin goyan baya da kuma yi ma ta addu’a, don ganin mun samu nasarar kawo zaman lafiya a wannan jiha tamu ta Zamfara.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: