Daga Hussaini Yero, Gusau
A shirin Gwamnatin Jihar Zamfara na sasanci da sulhu da ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane da satar shanu da gwamnatin Jihar Zamfara ke yi karkashin jagorancin Gwamna Bello Matawalle Maradun yanzu haka gwamnatin ta ‘yanto mata takwas da ‘ya’yansu hudu da masu garkuwa da mutane suka sace a karamar hukumar Bungudu.
A bikin masu wadanda aka ceto, Gwamna Matawalle ya mika godiyarsa ga Allah akan ceto wadannan mata takwas da ‘ya’yan hudu da suka kwashe wata biyu suna hannun mahara a dajin dansadau.
“Kuma shirinmu na sulhu shine alheri na samun zaman lafiya a Zamfara, kuma duk hanyar da zan bi wajen samar da zaman lafiya a Zamfara zan bi. Sukar masu suka ba za ta hana ni sulhu da mahara ba. Tunda addinimu na Musulunci ya yarda da sulhu, mun amshe shi hannu biyu,” inji Gwamna Matawalle.
An sace matan ne da yaran da suke shayarwa a lokacin da su mahara suka shiga kauyen Rugumau dake cikin karamar hukumar Bungudu wata biyu da suka wuce, amma yanzu gwamnatin Zamfara ta amso mata da ’ya’yansu a bisa sulhu da gwamnatin ke yi da su maharan yanzu haka ba tare da biyan kudin fansa ba, kamar yadda ta bayyana.
Kwamishinan Tsaro na Jihar Zamfara, Hon. Abubukar Dauran, ya bayyana cewa, gamsuwa da sulhu da gwamnatin ke yi da su ‘yan bindiga suka gamsu da shirin Gwamna Matawalle ba yaudara ba ne ya sanya suka bada wadannan mata takwas da ‘ya’yan hudu suka kuma mika makamansu ga gwamnati su ‘yan bindiga 11 daya a cikin wannan satin.
Hon Dauran ya kara da cewa, “wannan ya tabbatar mana da cewa, sulhu alheri ne, don ta hanyarsa mun ceto mutane sama da dubu daya a cikin jihar Zamfara har da wadanda ba ma ’yan Jihar ba, kuma ’yan bindiga sama da 50 ne suka tuba suka mika makamansu. Wannan ba karamin alheri ba ne a gare mu.
“Don haka masu adawa da wannan shirin na samar da zaman lafiya lallai ba za mu bar su ba. Jami’an tsaro za su dauki mataki akansu, don ba son cigaban Jihar Zamfara suke ba.”
Tuni dai Gwamna Matawalle Maradun ya mika wa Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Abutu Yaro, bindigogin da su maharan suka bada da alburusai a fadar gidan gwamnati dake Gusau babban birnin jihar Zamfara a jiya Laraba.