Sulhu: Zan Saki Duk ‘Yan Bindigar Da Ke Tsare – Masari

Gwamnan Jihar Katsina, Bello Masari

A kokarinsa na kawo karshen hare-haren ’yan bindiga a jihar Katsina ta hanyar yin sulhu, Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya tabbatar wa ’yan bindigar cewa, za a sako masu ’yan uwansu da ke tsare a hannun hukumomi ’yan sanda da sojoji da kuma wadanda ke gidajen kurkuku daban-daban a cikin jihar ta Katsina, wadanda su ke zaman jiran sharia a kotuna muddin ba a yanke mu su hukunci ba.

Gwamna Masari ya bayyana haka ne, a lokacin da ya ke cigaba da shiga daji, inda barayin su ke da sansani a garin Runka da ke iyaka da dajin Rugu a karamar hukumar Safana.

Masari ya kara da cewa, “haka ku ma ’yan bindiga dole ku sako duk wani wanda ku ka sace ko’ina ya ke. Ku tabbatar ma na da sako ma na shi ba tare da bata lokaci ba, saboda wannan sulhun duk wanda bai rungume shi ba, ya zama shaidan, to gwamnati za ta yake shi yadda ya kamata. Gwamnati a shirye ta ke ta biya mu ku dukkanin bukatunku, wanda ba zai gagare ta ba.”

Shi kuwa da ya ke maida jawabi, daya daga cikin  hugabannin ’yan bindiga, Alhaji Abdulaziz Magware, ya bayyana cewa, wannan sace-sacen mutane da kashe-kashen akwai hannun jami’an tsaro, masarautar gargajiya da kuma wasu daga cikin jami’an gwamnatinsa. Don haka, a cewarsa,  ya kamata gwamna ya kara Sanya ido sosai, domin akwai bara-,gurbi a bangarensa.

Abdulaziz ya yi kira ga Gwamnan jihar ta Katsina da ya gina mu su makarantun da  za su sanya yaransu, samar da ruwan sha da kuma kayan more rayuwa. Kuma sun yi alkawarin yin sulhu na amana, muddin a ka cika mus u wadannan alkawurran da su ka nema a wajen gwamna ya dauka.

Da ya ke jawabi a madadin jami’an tsaro da ke aiki a jihar Katsina, Kwamishinan ’yan sanda na jihar Katsina, CP Sanusi Buba, ya ce, “mu na goyan bayan wannan sasasanci da sulhu da Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, kuma za mu bada duk guddummuwar da ta dace, don ganin an samu nasara.”

Exit mobile version