Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace matafiya bakwai akan babbar hanyar Ilesa zuwa Akure.
An tattaro rahoton cewa, wadanda aka sace din suna tafiya zuwa Akure ne ranar Talata lokacin da ‘yan bindigar ke dauke da makamai, suka tsayar da motar bas dinsu suka yi awon gaba da mutane bakwai. Jaridar banguard ta tattaro cewa yan fashin, yayin da suke sakin mutane uku daga cikin wadanda aka sacen, namiji da mata biyu, a ranar Laraba, sun umarce su da su je su nemi kudi domin a sako sauran mutane hudun. An kuma ce sun fada wa wadanda aka saki din cewa su Fulani ’yan fashi ne da ke bukatar kudi ba ‘yan fashi da makami ba.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamandan rundunar ta Amotekun na Jihar Osun, Birgediya-Janar Bashir Adewinmbi ya ce, ‘yan bindigar sun kutsa cikin dajin, amma ma’aikatan Amotekun na bukatar tura su zuwa yankin tare da tseratar jama’ar da ke cikin gandun dajin.
“Gaskiya ne an yi garkuwa da mutum bakwai a daren Talata kuma an saki uku ranarar Laraba yayin da hudu ke hannunsu. Amotekun tare da hadin gwiwar Oodua People’s Congress da sauran hukumomin tsaro sun dade suna neman wadanda lamarin ya rutsa da su. Na kuma ziyarci wurin da abin ya faru kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba a kokarinmu na ganin sauran wadanda abin ya shafa sun dawo da gida cikin iyalinsu”, in ji shi.
Har ila yau, Kodinetan OPC na jihar, Prince Deji Aladesawe ya tabbatar da ikirarin, yana mai cewa ‘yan bindigar sun saki uku daga cikin wadanda suka sace kuma sun umarce su da su je neman kudi domin ceto ‘yan uwansu. “Muna aiki tare da ma’aikatan Amotekun don bincike dajin tare da tabbatar da ganin an sakin sauran wadanda abin ya shafa.
Sun saki mutaum uku kuma sun ba da sako ta hanyar wadanda aka sako cewa su ‘yan fashin ne da ke bukatar kudi. “‘Yan fashin sun kuma umarci wadanda aka sako din da su je neman kudi don a sako sauran mutum hudun da ke hannunsu”, in ji shi. Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Yemisi Opalola ba ta amsa kira ba don jin ta bakinta.