Wani maraki da aka haifa da Kafa biyar ya zama sanannen dan gari, a inda ‘yan kauyaku ke zuwa daga ko ina don bauta mashi.
Hotunan da aka nuna sun nuna yadda mazauna kauyukan suka taru a filin wasa don daukar juna suna shafa saniyar da ba a saba gani ba a lardin Surin da ke Arewa maso Gabashin kasar Thailand, a ranar 6 ga Janairu.
Kyamarar ta nuna yadda saniyar nake, wanda ana iya ganin karin kafa daga bayanta. Kafarsa saniyar na biyar yana da kofato biyu, wadanda suke hade da juna. Abin mamaki shine, dan marakin dan shekara biyu mai suna Kamkoo yana da koshin lafiya kuma yana iya yawan sa ko ina yayin da yake kiwo tare da mahaifiyarsa.
Iyalan da suka mallaki saniyar sun yi imanin cewa hakan zai kawo musu sa’a kamar yadda kalandar kasar Sin ke cewa shekarar 2021 ita ce shekarar Sa’a (Od).
Matarsa kuma, Bualee ta ce, “Na yi mafarkin wani mutum ya zo ya gaya mani cewa lamba 551-465 zai zama lambar cacar da zan lashe.” Bugu da kari kuma, ba wai kawai masu Kamkoo ba ne wadanda suka yi imanin samun sa’a da shi, sauran jama’ar kauyen ma sun yi.
Mazauna yankin sun ce, tun lokacin da aka haifi marakin, suna ta mafarkin dan mamata na gaya musu lambobin cin caca wanda za su yi amfani da shi don tikitinsu kamar yadda daman sun dade suna ganin dabbobi a matsayin abubuwan kawo sa’a.
Masana sun yi imani da cewa, an haifi marakin ne da ‘plymelia’, lahani na haihuwa wanda ke haifar da karin kafafu, wanda ke yawan samun dabbobin da ke zaune a kasar. An haifi makamancin irin wannan saniyar a kwanakin baya da ake kiran ta ‘mu’ujizar Allah’ bayan an haife ta da ido daya kuma ba hanci.