Sunayen Wurare Mafi Yawan Haruffa A Duniya

Daga Imam M. Muhammad

Mutanen da ke zaune a garin “Mamungkukumpurangkuntjunya” da ke kasar Ostiraliya, suna hakuri sosai idan aka zo ga koyon rubuta sunan garinsu. Amma kun san mene ne? Haka zalika mutanen garin Tafkin “Chargoggagoggman-chauggagoggchaubunagungamaugg” a yankin Massachusetts da ke kasar Amurka da “Tweebuffelsmeteen-skootmorsdoodgeskietfontein” da ke Afirka ta kudu.

Babu dayansu da ke shan wuya wajen rubuta adireshinsa kamar wadanda ke zaune a garin “Taumatawhakatangihanga-koauauotamateaturipukakapikimaung-ahoronukupokaiwhenuakitanatahu” da ke kasar New Zealand.

Wannan shi ne sunan wuri mafi tsayi a duniya mai kunshe da haruffa 85.

Exit mobile version