Kungiyar Amnesty International ta zargi jagorar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi, da kokarin rufa-rufa kan aika aikar da akayi a Jihar Rakhine, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin kisan kare dangi kan Musulmi ‘yan kabilar Rohingya.
Kungiyar tace mutanen Rohingya da suka samu mafaka a Bangladesh bazasu koma gida ba a karkahsin irin wannan yanayin, ganin yadda Suu Kyi ta nemi dora laifin cin zarafin da aka samu kan mutanen da aka tauyewa hakki.
To sai dai, Jagorar Gwamnatin kasar ta Myanmar Aung San Suu Kyi, ta bukaci taimakon kasashen duniya wajen hada kan al’ummar kasar, bayan tashin hankalin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin kisa kare dangi.
Yayin da take jawabi kan rikicin da ya barke tun ranar 25 ga watan Agusta, Suu Kyi tace kofar kasar a bude ta karbi ‘yan gudun hijirar da suka gudu bayan tantance su.