Daga Abdulrazaƙ Yahuza Jere, Abuja
Wani yaro da bai wuce shekara goma da haihuwa ba a duniya ya gamu da fushin matar wansa inda ta rufe ido ta cire Imani ta kwarara masa kalanzir a jiki kana ta ƙyasta ashana saboda y aɓatar da wandon sawa da ta saya masa.
Yaron mai suna Chimobi ya sha wannan azabar a hannun matar ne a titin Adenugba da ke Unguwar Agunfoye a yankin Ƙaramar Hukumar Ikorodu da ke Jihar Legas. Matar mai suna Gift Igwe ana zargin ta banka wa yaron wuta ne bayan ta fahimci ya ɓatar da wandon da ta saya masa a yayin da ta nemi ya kawo wandon ya tsaya yana inda-inda.
Rahotanni sun nunar da cewa jami’an ‘yansanda na yankin Igbogbo sun yi awon gaba da Gift tana can tsare a hannunsu domin gudanar da bincike.
Yaron ya bayyana cewa tun da ya zo gidan matar ta hana shi sakat, kuma ɗan’uwan nasa bai sanya shi a makaranta ba ballantana idan ya fita makaranta ya samu sa’ida.
Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yansandan yankin, Olarinde Famous ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce da zarar sun kammala bincike za a gurfanar da wacce ake zargin a gaban kuliya.
Rahotannin na nunar da cewa yankin na Ikorodu wanda yake samun bunƙasa a kullu yaumin, yana ƙara zama wurin da masu aikata assha ke cin karensu babu babbaka.