Wata mata ‘yar kasar Japan da ake zargin ta boye gawar mahaifiyarta a cikin wani firiji a cikin gidanta tsawon shekaru goma, ta shaidawa ‘yan sanda cewa tana tsoron bincike ne idan aka gano mutuwar mahaifiyar ta ta, in ji kafofin watsa labarai a ranar Asabar.
‘Yan sanda sun fada wa kamfanin dillacin labaran kasar Faransa na AFP cewa, an tsare Yumi Yoshino, mai shekara 48, a kan zargin boye gawar wata mata da aka samu a ranar Laraba a cikin firiji a wani gida cikin garin Tokyo.
Yoshino ta ce, bayan gano mahaifiyarta da ta mutu shekaru 10 da suka gabata, ta boye gawar ne saboda ba ta son ta fita daga gidan da suke zaune, kamar yadda kafafen yada labaran cikin gida suka ruwaito, inda ta ambaci majiyar ‘yan sanda da ba a bayyana sunan ta ba.
Mahaifiyar, wacce ake tunanin shekarunta sun kai 60 a lokacin da ta mutu, an yi rajistar gidan da sunan ta ne a wani rukunin gidaje na birni. An tilasta wa Yoshino barin gidan ne a tsakiyar watan Janairu bayan ta ki biyan kudin haya, a inda mai tsabtace muhalli ya gano gawar a cikin firinjin da aka boye a wani kabad.
Rahotannin sun ce, binciken da aka yi a kan gawar bai nuna lokaci da kuma dalilin mutuwar matar ba, kuma babu wasu raunuka da ake gani a jikin daskararren gawar. Yoshino ta tankwara gawar ne don ta shiga cikin firijin, kamar yadda ‘yan sanda suka fada wa jaridar Jiji. An kama Yoshino a cikin wani otal a garin Chiba, kusa da Tokyo, ranar Juma’a.