Yusuf Shuaibu" />

Ta Daba Wa Mai Rabon Fada Wuka

Wata matar aure mai suna Salimat Hamza ta gurfana a gaban wata babbar kotu da ke Jihar Kaduna, bisa tuhumar ta da soke mai rabon fada lokacin da ta zo rabon fada. Wacce ake tuhumar mai shekaru 22 tana zaune ne a kan titin Taiwo Road da ke cikin Jihar Kaduna, a na dai tuhumar ta da raunata mai rabon fada.

Lauya mai gabatar da kara Abubakar Shehu, ya bayyana wa kotu cewa, mai rabon fadar makwabciyar wacce ake tuhuma ce mai suna Halima Musa, ita ce ta kawo rahoton lamarin zuwa ofishin ‘yan sanda da ke yankin Sabon Gari a ranar 15 ga watan Maris.
Ya zargi wacce ake tuhuma da daba wa mai rabon fada wuka a ranar 15 ga watan Maris lokacin da take kokarin raba fada a tsakanin Salimat da wata makwabciyarta. Shehu ya kara da cewa, mai rabon fadar ta yi fama da raunin da ta samu wanda ta yanke ta a kanta da kuma hannunta.
Ya ce, wannan laifi ya saba wa sashe na 219 na dokar fanal kot ta Jihar Kaduna. Wacce ake tuhumar ta musanta laifin da ake tuhumar ta da shi.
Alkali mai shari’a, Mustapha Umar, ya bayar da belin wacce ake tuhuma kan kudi na naira 100,000 tare da mutum daya mai tsaya mata. Bayan kama, ya dage sauraron wannan kara har sai zuwa ranar uku ga watan Afrilu.

Exit mobile version