Ta Ina Tinubu Zai Fara?

Biyo bayan nada babban jigo a jam’iyyar APC ta kasa, Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin sasanta rikita-rikitar da ta kanannade ya’yan jam’iyyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi, ya jawo kace-nace tare da yamadidin zargin ‘anya mai bunu a gindi zai iya kai gudumawar kashe gobara?’ Ta duba da manufar kwamitin na sulhunta ‘yan jam’iyyar wadanda suka hana ruwa gudu, wanda kuma ake yiwa kallon ‘jan aiki’ ko abu mai kamar wuya, tare da bayar da dalilan yadda rikita-rikitar ta yiwa APC kawanya a cikin kowacce jiha a kasar nan.

Bisa hasashen da masana suke dashi, shi ne ayyana wannan kwamitin keda wuya, a karkashin Bola Ahmed Tinubu, baya ga yadda dama daga cikin jigajigan jam’iyyar daga shiyoyin kasar nan, sun dana tarkon dakon jiran wakilan kwamitin, domin bayar da korafe-korafen su tare da amayar da koken da ke zukatan su da jimawa, kana da gindaya sharudda da ka’idojin da dole sai in an yarda dasu ne- kurar rikicin zata lafa, amma da zaran ba haka ba, to fau-fau.

Bugu da kari, ta bayyana a fili kan cewa APC ta samu tasgaro tare da rarrabuwar kawunan ya’yan ta; a kalla mafi shahara a cikin jihohi 10, wadanda muhimmai sune Bauchi da Ondo da Ogun da Oyo, Kogi, Kaduna da Kano hadi da Zamfara da makamantan su. Wadanda kuma manyan jigajigan masu rike da madafun iko ke fito-na-fito da junan su; tsakanin gwamnoni da sanatoci da ministoci, yanayin da ya taimaka wajen ruruwar wutar rikicin.

Akwai yuwuwar Kano ta amsa sunan ta- ko da me ka zo an fi ka, akwai hasashen ayarin Tinubu ya hadu da ciwon kai a Kano fiye da kowacce jiha, wadda rikicin cikin gida ya daidaita yan jam’iyyar APC. Rikici tsakanin  Gwamna Ganduje da tsohon maigidan sa, Dakta Rabiu Kwankwaso, yayi zurfi sosai tare shan kan sauran. Masana suna kallon cewa, wannan kwamitin ya zo a makare- idan an kalli wannan gutsiri-tsoma ta Kano, wasu na ganin da wahali APC ta kai banten ta a 2019.

A nashi bangaren, Ganduje ya yiwa rikicin kwab-daya, inda ya ci alwashin musanya kujerar Kwankwaso ta Sanatan tsakiya da wanin sa a zaben 2019 mai zuwa. Akwai alamun sasanta tsakanin su da maigidan sa ya hadu da turjiya.

“Suna son mu sasanta dasu. Wanne dalili ne zai sa mu sasanta? Kuma a kan me zamu yi sulhu dasu?” Inji Ganduje.

A Kaduna ma, batun bai sauya ba, jiha ce wadda zaman yan-marina ke ci gaba da zafafa mai matukar rashin tabbas dangane da shawo kan kurarar da ke ci gaba da turnukewa a tsakanin Gwamna Nasir El-Rufai da bangaren Sanata Shehu Sani da Sanata Hunkuy hadi da tsohon shugaban jam’iyyar APC, Dakta Hakeem Baba Ahmed. Halin da kowanne bangare ya ja daga tare da shan alwashin ganin bayan wani a zaben 2019 mai zuwa.

A fita batun sauran bangarori ko jihohin kasar nan, wadanda rikicin cikin gidan jam’iyyar APC ya kazanta, wanda ake sa ran kwamitin da Tinubu zai jagoranta ya tabuka abin a zo a gani. Hatta a jihar Lagos, bata kubuta daga afkawa a cikin gida ba, yayin da akwai zafafan musayar kalamai tsakanin gwamnan jihar Akinwunmi Ambode da wanda yangabace shi, Babatunde Raji Fashola, kuma ministan ayyuka, makamashi da gidaje. Akwai masu ra’ayin ko a Legas kadai, wankin hula na iya kai Asiwajo Bola Tinubu dare.

Har wa yau, kwamitin Tinubu yana da gagarumin aiki tare da jibin goshi a jihar Bauchi ganin yadda rikicin yayi kamari a tsakanin shugaban majalisar wakilai, Hon. YaKubu Dogara ta duba da yadda ake samun sa-toka-sa-katsi da shi da gwamnan jihar Mohammed Abubakar wajen wa ke da ikon tafiyar da APC a jihar. Ga rikicin Sanata Olamilekan Adeola da Gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun, dangane da zaben 2019 mai zuwa.

Karara kuma bainar jama’a gwamna Amosun ya nuna Adeola (Yayi) da cewa babu yadda za a yi su kyale bako ‘Tekobo’ ya gaji kujerar sa- ta gwamnan jihar. Yayin da a can kuma jihar Oyo, rikicin cikin gidan APC ya barke a tsakanin ministan sadarwa, Adebayo Shittu tare da Gwamna Abiola Ajimobi, wanda kurar cece-kucen saida ta turnuke har a-in-san har Aso Billa.

Dadin-dadawa kuma, turnukun rikicin ya’yan jam’iyyar APC a jihar Kogi shi kuma ya dauki sabon salo, wanda Gwamna Yahya Bello yake buga-in-buga da manyan kososhi a jihar. Ga tata-burzar da ke tsakanin sa da James Faleke a kotun koli sannan ga rikicin su da magoya bayan Sanata Dino Melaya.

Akwai hasashen cewa rikicin rarrabuwar kawunan yan jam’iyyar APC a Kogi kadai ya ishi kwamitin Ahmed Tinibu jibin goshi, wajen gano bakin zaren ballantana ya sasanta tsakanin.

A Katsina, Gwamna Aminu Masari ne ke tayar da jijiyar wuya tare da yiwa juna kallon hadarin kaji, tsakanin sa da yan jam’iyyar APC wadanda suka kira kansu da APC-Akida, mutane irin su MT Liman, Sadik Yar’Adua, Sada Ilu hadi da Usman Bugaje.

Can kuma Zamfara, Sanata Kabiru Marafa ne ke kokarin kasancewa babbar barazana ga gwamna mai ci yanzu, Abdul’aziz Yari, tare da zazzafar muhawarar nuna wa juna yatsa, masu cike da alamun rarrabuwar kai a tsakani. Musamman a cikin yan kwanakin nan inda Marafa ya kwancewa Yari zane a kasuwa da zargin bai tabuka wani abin a zo a gani gabal’ummar da ta zabe shi ba. Akwai alamun yana hararen hawa kujerar gwamntin jihar Zamfara a zabe mai zuwa.

Masu bibiyar lamurran siyasa sun yi ta canjin yawu a tsakanin su dangane da bayar da ra’ayin cewa shigar rakumi a kofar allura yafi sauki fiye da aikin Tinubu wajen sasanta tsakanin yan jam’iyyar APC- musamman a cikin wadancan jihohi wadanda turar rikicin ta kai bango. Inda karawa da karau, shi kanshi Tinubun kanwa ne uwar gami tare da kasancewa na gaba-gaba da ake zargi da tayar da husuma a cikin jam’iyyar APC.

A cikun shaguben da Barista Frank Okon, kuma mamba a jam’iyyar APC a yankin kudu maso-kudu yayi, ya bayyana cewa kuna kokarin hada kan dukkanin bangarorin jam’iyyar APC saboda shi kan sa mutumin da yake jagorantar kwamitin bai kubuta da kasancewa kanwa uwar gami ba: ksoshin jam’iyyar APC na kasa sune suka fi kowa zama kanwa uwar gami wajen hana ruwa gudu, tare da rura wutar rikicin.

“Ta yaya ne zaka sanya mutumin da shi ne na daya wajen hana ruwa gudu a jam’iyya, ya jagoranci sasanta tsakani ? Wannan jigon fa, shi ne wanda ya rura wutar rikici da dama da jam’iyyar ke ciki a yanzu. To shi kuma wa zai sulhunta tsakanin Tinubun da shugaban jam’iyyar APC na kasa, John Odigie-Oyegun? Ko kana son ka ce baka san cewa Tinubu ne yake kawo cikas a wannan tafiyar ba ? Akwai bukata da farko ya fara da tsabtace kan sa dangane da zargin yiwa shugaban kasa makarkashiya.”

“Tinubu yana da tabanni da dama a zukatan yan jam’iyyar APC da daman gaske, musamman wadanda suka hana shi rawar gaban hantsi a lokacin zaben shugaban majalisar dattijai. Babu ga-maciji a tsakanin sa da shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki tare da sanatocin da suka goyi bayan Saraki. Sannan kuma babu ina-kwana tsakanin sa da Yakubu Dogara da Gwamna Aminu Tambuwal, akan mukamin shugabancin majalisar wakilai. Shi kuma wa zai sasanta shi da wadannan yan majalisar, ko shi ne zai sulhunta kansa dasu?”

Yayin da a hannu guda kuma, Femi Fani-Kayode, ya bayyana ra’ayin sa dangane da aiki da fadar shugaban kasa ta dora wa Bola Ahmed Tinubu, na sasanta yayan jam’iyyar APC da cewa, makarkashiya ce wadda Buhari ya kulla na nufin shafe hasken tauraruwar Tinubu daga farfajiyar siyasar Nijeriya.

Tsohon minista a jam’iyyar PDP, ya ce bayan Buhari ya gama rusa Tinubu, har wa yau, zai kuma zarge shi da gazawa wajen taka muhimmiyar rawa a jam’iyyar.

Fani-Kayode ya ce “domin a duk lokacin da sarki ya so dushe hasken wani daga cikin kwamandojin sa, sai ya kirkiro aiki mai wuya, wanda ba zai yuwu ba- ya ce yayi, ko yakin da Ba za a taba cin nasarar sa Ba”.

“Nada Bola Ahmad Tinubu (BAT) domin sasanta tsakanin  mabambantan ra’ayoyin yan jam’iyyar APC, abu ne mai kamar wuya. Manufa a nan ita ce, domin ya dushe hasken tauraruwar sa, kuma daga karshe ya zarge shi da gazawa.”

Tun kafin wannan lokaci, jama’a da dama, a ciki da wajen jam’iyyar APC an yi ta kiraye-kiraye ga uwar jam’iyyar kan ta dauki matakan gaggawa wajen yiwa rikita-rikitar cikin gidan ta kan-da-garki amma tayi biris da batun. Amma sasura da me, lokaci ne zai tabbatar da sakamakon da zai biyo bayan nauyin da aka damka wa wannan kwamiti a karkashin Bola Ahmed Tinubu.

Duk da ko yadda wasu da dama na tofa albarkacin bakin su dangane da samar da kwamitin sasanta tsakanin ya’yan jam’iyyar APC da sabani ke neman daidaita tafiyar ta.

Da yake bayar da nashi ra’ayi dangane da matakin, Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a zauren majalisar dattijai, Shehu Sani, a shafin sa na Tweeter cewa yayi” wannan kwamitin shi ne dama ta karshe ga jam’iyyar APC”.

Exit mobile version