Ta Mayar Wa Mijinta Sadakin Naira 28,000 Bayan Shekaru Bakwai Da Aurensu

Wata mata a Abuja ta mayarwa mijinta kudin sadakin da ya biya lokacin da ya aure ta Naira 28,000. Hakan ya biyo bayan kai shi kotu matar da mata ta yi kan a raba aurensu domin ba ta da ra’ayin cigaba da zama da shi. Mijin ya nemi kotu ta ba su dama su yi sulhu amma hakan bai yi wu ba don haka ya ce ta biya shi kafin ya sake ta. Mutum mai suna Boyi Adamu sadakinsa Naira 28,000 ne, bayan wata kotu mai daraja ta 1 da ke zamanta a Gwagwalada Abuja ta raba aurensa sakamakon karar da matarsa, Hauwa Abdulkarim ta shigar a kotu. Hauwa, wace ke zaune a Unguwar Dodo a Gwagwalada, a cikin karar da ta shigar da ta nuna bata da ra’ayin cigaba da zama da mijinta bayan shekaru bakwai da aurensu, kamar yadda majiyarmu ta ruwaito.

Adamu, wanda ke zaune a Rafin-Zurfi, da farko ya nemi kotu ta bashi daman yin sulhu da matarsa amma hakan bai yiwuwa ba inda matar da dage sai ya sake ta. Don haka, ya nemi matar da mayar masa da jimillar kudi Naira 203,500 daga matarsa a matsayin kudin da ya kashe wurin aurenta. Sai dai daga bisani, ma’auratan biyu sun cimma matsaya a kan Naira 28,000 wanda shi ne sadakin da ya biya lokacin da zai aure ta.

Alkalin, Adamu Isah, ya raba auren bayan da matar da mayarwa mijinta kudin sadakin da ya bayar yayin da za a daura aurensu da ita.

Exit mobile version