Mahukunta a yankin Arewa maso Gabashin kasar Brazil na duba ga wani kisan da a ka yi wa wata yarinya ‘yar shekara biyar da mahaifiyarta ta amsa kisan, inda take cewa ita ce ta kwakule idanun yarinyar, sannan kuma ta yanke wani bangare na harshen ta kafin ta tautaune su duka.
An kama Josimare Gomes a gidanta da ke karamar hukumar Marabilha a ranar Lahadi, sannan kuma ta fada wa masu binciken cewa ita da kanta ta kashe ‘yarta mai suna, Brenda da Silba, domin aikin tsafi.
‘Yan Sanda na farar hula sun ce Marinho da Silba ya yi kiran neman taimako ne da karfe 4 na yamma na agogon kasar, bayan ‘yarsa ‘yar shekara 30 ta kulle kanta a bandaki tare da jikar ta na tsawon mintuna 30 kuma ta ki bude kofar.
Damuwar dangin ya ta’azzara ne a lokacin da suka hango jini da ruwa suna zubowa daga magudanar ruwa na bayan gidan wanda yake a kauyen Marabilha na São Cristóbão. Daga nan Marinho da Silba ya fasa kofa ya tarar da Gomes tana makale da almakashi yayin da Brenda da Silba ke kwance a kasa cikin jini ba idanunta da harshenta.
Mahukunta sun isa wurin sai suka ga Gomes tana addu’a rike da wani abin tsafi kusa da gawar ’yarta, kafin su kama ta. Masu binciken sun yi imanin cewa raunukan da aka yi wa yarinyar da almakashi a yayin da take raye su suka yi sanadin mutuwarta.
An kuma bayar da rahoton cewa, da kyar aka kwantar da Gomes sannan aka kai ta ofishin ‘yan sanda a cikin gundumar da ke kusa da Delmiro Goubeia. Gomes ta ba da rahoto mara kyau ga ‘yan sanda washegari da safe cikin harsuna da dama na tsafi.
A wata sanarwar kuma, an ce ta musanta cire idanun ‘yarta da kuma sanya harshen ‘yarta a bakinta. Gomes ta kuma fadda wa hukumomi cewa, ita ba ta kashe ‘yarta ta ba, aljanin da ke jikin yarinyar ta kashe, don haka ‘yarta na nan da rai.
An san wacce ake zargin tana fama da matsalar tabin hankali na bacin rai, kuma an yi imanin cewa ita ce ta kai harin a lokacin da ake gwajin masu tabin hankali.
Sakamakon rokon lauyan gundumar Marabilha Kleytione Pereira, Gomes, wacce ta ci gaba da kasancewa a hannun ‘yan sanda, an tura ta zuwa Asibitin Kula da masu tabin hankali don cikakken kimantawa da halayyar dan adam.