Wata mai suna Sarah Robbins-Cole, mai shekara 52 da haihuwa, ta fahimci cewa tana da tufafin da zai shiga da kowane irin bukukkuwa, don haka babu bukatar ta sayi wani sabon tufafi.
Sarah Robbins-Cole tabbas ta ci moriyar kudin ta sayi wata doguwar riga mai baka har tsawon gwiwa. Ta sanya rigar ne don aiki, daga baya kuma na fara fita da shi don nunawa mutane har ma a ranar Kirsimeti.
A zahiri, ‘yar shekaru 52 din ta sanya rigar ta Rowena, wacce aka yi ta daga audigar ‘merino’, na tsawon kwanaki 100 a jere. Shugaban Cocin kuma malamin kwalejin Sarah Robbins-Cole ya yi barkwanci da cewa tana daukar aikinta a zahiri, ta zama mai tufafi daya.
Sarah, wacce ke zaune a garin Boston da ke kasar Amurka, ta shiga gasar sanya tufafi daya har na tsawon kwana 100 a ranar 16 ga Satumba, 2020 a yunkurin rayuwa ba tare da canja salo ba da kuma taimakawa wajen ceton duniya. Tana jin dadin hakan sosai, don haka ta saita kanta a matsayin sabon kalubale a shekarar 2021.
Ta kara da cewa, “Na lura cewa, a shekaruna ina da tufafi na kowane irin lokaci, kuma idan ina bukatar rigar kwalliya, zan yi kakkabe daya daga cikin tufafin na tun na 1992. Ina tunanin kakkabe wurin ajiye tufafina, amma zan jira in ga irin kayan da zan sa a shekara mai zuwa.”
Sarah tana da ‘ya’ya uku tare da mijinta dan kasar Burtaniya, kuma iyalan suna da karnukan ceto biyu. Tana daga cikin mata kusan 250 da suka dauki kalubalen sanya tufafi na tsawon kwanaki 100, wanda ake amfani da shi mai suna ‘Wool & Dress’.