Khalid Idris Doya" />

Tantance Lambar Banki: Gwamnatin Bauchi Za Ta Zakulo Ma’aikatan Bogi – PDP

Jam’iyyar PDP da ke mulki a jihar Bauchi, ta bayyana cewar tsarin da gwamnan jihar Bala Muhammad ya zo da shi na kafa kwamitin da za su binciki yadda wasu ma’aikata ke amsar albashi ba tare da lambar tantancewa ta asusun ajiyar banki ba, da cewar shirin zai bayar da cikakken damar fidda ma’aikatan bogi da wadanda suke cin kudaden haram.

Idan za ku iya tunawa dai, gwamnatin jihar ta yi ikirarin cewar yanzu haka ma’aikata da masu amsar fansho su dubu 41,448 ne ke amsar albashi ba tare da lambar tantancewa na banki ba, wanda hakan ya sanya gwamnatin cikin shakkun cewar akwai ma’aikatan bogi da wadanda suke cin albashi fiye da daya a cikinsu, hakan ya sanya gwamnatin daukar matakin tsaida albashinsu na watan Oktoba har san sun kawo lambar tantancewa na banki.

Da ya ke ganawa da ‘yan jarida a Bauchi, Yayanuwa Zainabari, sakataren watsa labarai na jam’iyyar a jihar Bauchi, ya bayyana cewar ta wannan hanyar ne kawai gwamnati za ta cire baragurbi masu cin albashi fiye da daya da kuma ma’aikatan bogi masu ci da gumin wasu da suke amsar albashi a karkashin gwamnatin jihar.

Ya ce sun gano cewar duk da ritaya da wasu ma’aikata ke yi, sun gano cewar adadin ma’aikata na karuwa duk da cewar jihar ba ta dibi sabbin ma’aikata ba, don haka ne ya bayyana cewar akwai gayar bukatar bincike sosai kan lamarin domin ci gaban jihar.

Zainabari ya kuma kara da cewa a bisa karuwar ma’aikatan bogi da suke kara danna wa gwamnatin jihar wahala ne ya sanya gwamnan daukar matakin tantancewa domin fitar da baragurbi da kuma daddale hakikanin ma’aikatun da suke jihar.

Ya sha alwashin cewar wannan aikin tantancewar zai gudana ne kawai domin fito da hakikanin ma’aikatun da suke kan albashi.

A cewar shi, “Da zarar kowani ma’aikaci ya mika lambar tantacewarsa ta banki, na tabbatar albashinsa za ci gaba da shiga masa babu wanda za a rike masa albashinsa. Gwamnati ba za ta musguna ma kowa ba, illa iyaka za mu tantance mu fitar da baragurbi,” A fadin shi.

Ya nemi ma’aikatan da abun ya shafa da su bayar da cikakkin hadin kai domin a samu cimma nasarar aikin tantancewar.

Jami’in watsa labarai na jam’iyyar yayi amfani da wannan damar wajen gode wa gwamnan a bisa kokarin da yake yi wajen nada hazikan da suka dace don ba shi hadin kai wurin kyautata jihar.

 

Exit mobile version