Abubakar Abba" />

Ta Ya Za A Magance Karuwar Zubar Da Ciki Ba Bisa Ka’ida Ba?

Tsoro da abin kunya da buna kyama ya sanya miliyon mata tsunda zubar da juna biyu harda yin hakan ba’ a bisa ka’ida ba, inda suke zuwa harmatattun asibiti don su zubar da juna biyun da suka dauka  kuma hakan yana jefa rayuwar su da lafiyar su a cikin hadari.

A wannan rahoton da SADE OGUNTOLA ta rubuta kuma ABUBAKAR ABBA ya fassara, kwararru akan harkar kiwon lafiya sun bayyana cewar, kaucewa mutuwar masu zubar da ciki ba’a bisa ka’ida ba, za’a iya samun nasara hakan ne idan irin wadannan matan sun kula da ‘yancin su yin jima’i da kuma kula da kiwon lafiyar  su.

Lokacin da ‘yan fashi da makami suka yiwa wata Mildred Haruna (wanda wannan ba shine sunanta na ainahi ba) fyade, a anguwar su dake cikin jihar Legas a shekarar 2005, ba ta taba tsammanin fyaden da aka yi mata da daren ranar ba zaici gaba da rikitar mata da rayuwar ta ba.

Bayan dimautar data tsinci kanta bayan yi mata fyaden, Mildred ta gano cewar, ta samu juna biyu kuma dimautar tata, taci gaba da karuwa saboda, duk da shawarar data yanke na ta bar juna biyun, sai dai dan albashin da take karba ba zai iya ba ta sukunin daukar dawainiyar

abinda zata haifa ba.

Sannan kuma mutane za su dinga kallon abinda zata haifa a matsayin shege tunda baida uba.

Sai dai, taga abinda yafi mata mafita shine ta zubar da cikin amma sai dai ba abu ne mai sauki a gare ta ba domin kuwa, maganar zubar da ciki abu ne da ya kamata ayi shi a asirce.

Ta yanke shawarar zuwa asibiti don ta yiwa likita korafin ba ta da lafiya yadda zata ja hankalin likitan.

Amma ba za ta yi korafin jin tabin hankali ba ko nuna akawai damuwa tare da ita ba saboda jaririn dake cikinta yana ci gaba da kara girma, inda a karshe dai ta haifi abinda ke cikinta.

A wata sabuwa kuma, wata ‘yar shekara ashirin da biyu mai suna Comfort, wadda dalibace a jami’a, itama an dirka mata ciki.

Sakamakon cikin, ta shiga cikin rudani da jin tsoro akan abinda zaije yazo, inda daga baya ta yanke shawar zubar da cikin ta hanyar zuwa gun likitan bogi.

Sai dai, ta samu nasarar zubarda cikin, amma daga bisani ta fara jin zafi wanda ya janyo mata ta fara kwarar da jini an kuma yi gaggawar kaita Asibiti daga bisani da ta mutu.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewar an samu kimanin miliyan ashirin da biyar na zubar da ciki ba bisa ka’ida ba da aka kiyasta ya faru a fadin duniya dukkan shekara, musamman a kasashen masu tasowa.

Daga cikin wannan adadin, miliyan takwas na zubar da cikin, anyi su ne ba bisa ka’ida ba ko kuma a cikin wasu yanayi masu hadarin gaske.

Bugu da kari, yawan  zubar da cikin da aka yi ba a bisa ka’ida ba, ya faru ne a nahiyar Asia kuma uku daga cikin hudu na zubar da cikin, ya auku ne a nahiyar Afirika da Latin Amurka.

Zubar da cikin da aka yi ba’a bisa ka’ida wanda har ya janyo mutuwa, yafi yawa a Afirika.

Ganin irin tunanin mafi yawancin ‘yan mata da kuma mata da suka dauki cikin da basu shirya ba, kwararru akan kiwon lafiya sunyi imanin cewar, zubar da ciki ba a bisa ka’ida ba yana kara zama babbar matsala akan harkar kiwon lafiya, musamman a kasashen da masu  karamin karfin tattalin arziki, harda Nijeriya.

Maganar gaskiya, jin tsoro da fadawa a cikin abin kunya da nuna kyama sune ke jefa miliyoyin mata zuwa Asibitocin boji don a zubar masu da cikin ba’a bisa ka’iba, inda hakan ke shafar lafiyar su da kuma rayuwar su kuma matan sune suke jin jiki in hakan ta faru gare su a

kowanne lokaci.

Ana samun zubar da ciki ba ‘a bisa ka’ida ba idan wanda zaiyi aikin zubar da cikin  baida wata kwarewa ko kuma a Asibitin da bai cika sharuddan zama Asibiti ba ko kuma dukkan biyun.

Abin takaici, nuna kyama ga matan da suka samu ciki ba tare da yin aure ba ko kuma a tsakanin ‘yan mata, ya kan sanya su fada a hannun likitocin bogi, inda hakan yake janyo masu ziyartar kabari ba tare da sun shirya ba.

Ba kowa wacce mace data sanu ciki ba tare da aure ba, takan kasance abin nunawa a gari.

A cewar wata Darakata ta Ipas Hauwa Shekarau tace,”sai dai mutane baza su samu cikakken labarin ba.”

Ipas kungiya ce mai zaman kanta da take gudanar da ayyukan kiwon lafiya a fadin duniya da kuma tabbatar da mata suna zubar da ciki a bisa ka’ida da samar da magunguna.

Shekarau ta bayyana hakan ne a wani taron bita na kwana uku da tsare-tsare data shiryawa ‘yan jarida.

A cewar ta,“za su sanar da masalaha ga abokin wanda zai samar masu da hanya mafita, amma wadanda za su jagorance su zuwa ga zubar da ciki ba a bisa ka’ida.”

Shekarau taci gaba da cewa, sai dai abin takaici, damuwa ta zubar da ciki tanada yawa dake hana mutane akan daukar matakan da ya dace.”

A cewar ta,“tunda basu san komai ba a zahiri, suna kawai dauka maganar kamar ba wata illa bace.”

Ta yi nuni da cewa “wannan shine yake haifar da fadawa ga hannun likitocin bogi  da rashin samun kulawa na kiwon lafiya da ya dace.”

Tace, illolin zubar da ciki ta hada da, zai iya janyo cutar cancer ta nono kuma matar data zubar da ciki ya kai har sau hudu, zatafi saurin mutuwa haka yin amfani da magunguna don a zubar da ciki zai iya janyo cutar (menopause).

Bugu da kari, hana samun damar zubar da ciki, itace hanyar da tafi dacewa wajen rage zubar da ciki kuma idan mace tana zubar da ciki zai hana mata haihuwa saboda wasu sassan dake cikin jikinta za su lalace.

Ta bayyana cewar “kuma wani abin takaici, kin bin ka’ida wajen zubar da ciki ba wai kawai yana shafar yawan zubar da ciki bane, yana kuma hana cimma burin da ake bukata.“

Ta yi nuni da cewa, mafi yawancin kama  masu zubawarwa da mata ciki da aka yi  suna karewa ne a kotu kuma ba’a yanke masu hukunci, sai dai idan wadda aka zubarwa da cikin ta mutu ko kuma wata illa ta same ta.”

A cewar ta, miliyan 1.25 na zubar da ciki da akeyi a duk shekara, ya faru ne a Nijeriya a shekarar 2012 a bisa binciken da ciniyar Guttmacher ta gudanar.

Wannan adadin, kamar a tsoma Allura ce a cikin ruwa sakamakon wani bincike da wani Asibiti ya gudanar a cikin jihohi sha takwas a Nijeriya.”

Yawan karuwar zubar da ciki ba ‘a bisa ka’ida yana da yawan gaske.

Sai dai, ta koka da akan tsar-tsaurar dokar da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka a fadin duniya, inda tace, hakan zai kara nuna kyama akan zubar da ciki domin hakan zai kara sanya illa akan binciken da kungiyoyi suke yi akan shirin lafiyar mata a nahiyoyin.

Tsarin garin Medico da aka sani na doka ya rufewa kasar Amurka bayar da kudi ga kungiyoyi masu zaman kansu wanda suke gudanar da aikin da ya shafi zubar da ciki ko bayar da shawarwari ko kuma kare ‘yancin mata na daukar juna biyu.

A cewar Shugaban kungiyar gangamin kayyade iyali Dakta Ejike Orji, zubar da ciki ba ‘a bisa ka’ida ba yana faruwa ne sakamakon nauyin tattalin arzikin kasa.

Orji ya zayyana illolin dake tattare da zubar da ciki ba’a bisa ka’ida wadanda kuma ya ce sune suka janyo hana daukar ciki a Nijeriya.

Ya ce, “akwai rashin jin dadi ga magidantan da basu iya daukar ciki, ya kara da cewa, a maganar gaskiya, mace musamman wadda ba ta iya daukar ciki ‘yan uwan nijinta sukan jefata a cikin damuwa.”

Dakta Orji ya ce koda yake, a kalla ga dukkan mata biyar da suke zubar da ciki ba’ bisa ka’ida ba, daya na iya mutuwa, kuma akwai wasu illolin dake biyo baya in sunyi hakan kuma akwai tsada sosai sakamakon kamuwar da matan suka yi da illolin zubar da cikin a yayin yi masu

magani.

Babban abinda yafi yi janyo barazana wajen zubar da ciki a bisa ka’ida, yana haifar kwararar jini da kamuwa da kwayoyin cuta da jin rauni a cikin sassan dake jikin matan.

A cewar sa, tsadar kudin da ake kashewa wajen samar da lafiya sakamakon matsalolin da suka auku a yayain zubar da ciki ba’a bisa ka’ida ba, yana zama nauyi ga harkar kiwon kafiya a tsakanin kasashe masu tasowa.

Ya yi nuni da cewar “amma za’a iya magance wannan tsadar ta zubar da cikin idan an rugumi hanyar kayyade iyali data kamata.”

Ya bayyana cewa, zubar da ciki wani abu ne mai wahalar gaske kuma abin tausayi da mutane suke ganin wani abu ne na rashin ‘yanci.

Shi kuwa Mista  Edoza Obiawe wanda shima yake aiki a IPAS, “ya ce, samun ‘yancin daukar ciki wani abu ne na ‘yancin dan adam.

Samun wadatacciyar tarawa da ingantaciyyar kiwon lafiya sun hada da; samar da magunguna na zamani da kula da zubar da ciki ko kuma karewa kamuwa da kwayar cutar kanjamau, wasu abu ne da za su taimaka wajen cimma burin ci gaba.”

Ya yi nuni da cewa, hanawa mata sararin zubar da ciki musamman idan akwai barazana ga rayuwar mata da suka dauki ciki, ko kiwon lafiyar su ko kuma idan cikin an same shine sakamakon fyade zubar sa cikin  ya sabawa ‘yancin dan adam.

A karshe ya ce,” idan ‘yan mata suna da koshin lafiya suna kuma da ‘yancin su, za su kuma  iya zuwa makaranta don su koyo wasu dabaru don kula da lafiyar su yadda za su zama manya da aka tallafawa.”

 

Exit mobile version