Mahdi M Muhammad">

Ta Zuba Tafasasshen Ruwa A Butar Tsarkin Mijinta Har Ya Salube Al’aura A Kano

Wata matar gida da aka bayyana da suna Sumayya Shu’aibu a ranar Litinin ta bayyana a gaban wata Kotun Majistare dake zaune a Jihar Kano kan zargin zuba ruwan zafi a cikin butar ruwan sanyi da mijinta ke amfani da ita wajen tsarki.

Sumayya, wacce kotu ba ta bayar da shekarunta ba, wacce ke zaune a karamar hukumar Minjibir da ke Kano, ana tuhumar ta da haifar da mummunar rauni da mijinta. Amma ita wacce ake zargin ta musanta aikata laifin.
Lauya mai shigar da kara, Asma’u Ado, ta fadawa kotun cewa, wacce ake tuhumar ta taba aikata irin wannan laifin a wani lokaci can a watan Satumbar 2020 a karamar hukumar Minjibir dake Kano.
Mai gabatar da kara ya fada wa kotun cewa, wacce ake tuhumar ta dafa ruwan zafi sannan ta zuba a cikin butar da mijinta ke amfani da ita, inda ta yaudare shi da amfani da shi wajen yin tsarki. Sani, wato mijin, ya samu rauni sosai a gabansa, laifin ya ci karo da tanadin sashi na 245 na Kundin Manyan Laifuka.
Babban Alkalin Kotun, Mustapha Sa’ad-Datti, ya bayar da belin wacce ake kara a kan kudi Naira 50,000, tare da amintattun mutane biyu.
Ya ba da umarnin cewa, daya daga cikin wadanda za su tsaya ma ta ya kasance ma’aikacin gwamnatin da ba ya kasa da mataki na 10, yayin da wanda zai tsaya ma ta na biyu dole ne ya kasance dan uwanta ne.
Ya dage zaman karar har sai ranar 16 ga Maris, domin cigaba da sauraron ta.

 

Exit mobile version