Ta Zurma Kafarta Cikin Lambatu Yayin Da Take Duba Sakon Waya

Lambatu

Wata siririyar yarinya ‘yan kasar Sin ta makale a inda ta zurma kafarta a tsakanin karafunan lambatu yayin tafiya tana duba sakonni a waya.

Yarinyar da har yanzu ba a bayyana sunanta ba, ta mai da hankali sosai kan wayarta ta hannu yayin tafiya a kan titi a cikin birnin Mianyang, a kudu maso yammacin lardin Sichuan na kasar Sin, yayin da take kokarin aika wa abokinta sakon ba tare da kallon abin da ke gaban ta ba, a inda ta zurma siririyar kafarta cikin tsanin karfen ta yadda ba zai fita ba har sai an yanke karfen lambatu din.

Wani Basamariye mai kirki ya kira jami’an kashe gobara kafin a cece ta bayan an jira na minti 45.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobarar Ming Lai ya ce, “Mu na zuwa wurin mu ka yanke karafunan lambatu din sannan muka cire kafar budurwar. Kafarta ta dan yi rauni kuma ta kuma ta ji rauni daga wajen cire karafunan, amma raunin bai yi muni kuma za ta warke da sauri wanda ba sai ta bukati asibiti ba.”

Wani ganau a wurin da lamarin ya faru wanda ya bayyana cewa, “Budurwar ta ji kunya sosai, domin ta rufe fuskarta da hannayenta lokacin da mutane suka taru, kuma tana cewa ba ta son kara mintuna a wurin.”

Exit mobile version