Connect with us

LABARAI

Ta’addanci: Al’ummar karamar Hukumar Faskari Na Cikin Tsaka Mai Wuya

Published

on

Al’ummar karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina suna cikin tsaka mai wuya sanadiyyar yawan kasha su da ‘yan ta’adda ke yi ko kuma yin garkuwa da su kusan kullum.

Lamarin ya tsananta a cikin watanni biyu zuwa uku babu wata mazaba da yan ta’adda basu kai farmaki ba inda suke kashe mutanen da yin garkuwa da su domin neman kudin fansa da kwashe masu dabbobi inda a yanzun mutanen karamar hukumar basu barci sanadiyyar wannan bala’i da suke ciki babu shakka al’ummar karamar hukumar sun koka kwarai da gaske ganin yadda ake asarar rayuka da karbar miliyoyin Naira a matsayin kudin fansa.

A halin yanzun yan ta’adda sun kusa kwace ma manoman karamar hukumar shanun da suke yin noma wadanda suka rage kalilan ne suma tuni suka kaisu kasuwa domin saidawa.

Wakilinmu ya zanta da jama’a da dama inda suka bukaci da a sakaya sunayensu a mazabar Sheme ‘yan ta’adda sun kashe mutum 9 a lokutta daban daban banda sauran mazabu matasa 3 a cikin garin Sheme sun kashe mutum 2 a kauyen Matseri sun kashe wata Matar aure 1 a kauyen kamfani da mutum 1 a kauyen Badole da mutum 1 a kauyen Nasarawa da yin garkuwa da mutum 7 a garuruwan Sheme, Unguwar Boka, da Matseri duka a mazabar Sheme saida a ka biya kudin fansa na Miliyoyin Naira.

Irin wadannan lamari ya faru a mazabun Mairuwa, Tafoki, Daudawa,Yankara, Yar Malamai, Sabon Layi, Galadima, Mai gora, da Faskari, inda ‘yan ta’addar suka kashe mutane da yawa da sace su domin yin garkuwa da su saida aka biya Miliyoyi Naira da kwashe masu dabbobin su duka a karamar hukumar Faskari saboda ya zama ruwan dare kullum kuma a ko ina.

A kwanakin baya barayin sun yi ma yan sandan yankin kwanton bauna inda suka harbi motar yan sanda kuma suka sami D P O a hannu da kafa a kan hanyar Sheme zuwa Yankara daf da shiga garin Yankara yanzu haka D P O yana kwance a wata asibiti inda yake karbar magani.

Al’ummar yankin sunyi kira ga hukumomin da abun ya shafa dasu taimakesu su kawo masu dauki ganin yadda kullum sai yan ta’adddar sun fita kuma sai sun kashe kuma suyi garkuwa da mutane su kwace masu dabbobinsu a halin da ake ciki yanzun manoman yankin basu da sauran shanun da zasu yi noma ko tumakan da suke kiwo domin saidawa ko suna.

Jama’ar yankin sun yi kira ga shugaban kasa Alhaji Muhammad Buhari da ya taimakesu ganin yadda yan ta’addar ke cin karensu ba babbaka.

Mutanen da wakilin mu ya zanta dasu suka bukaci a sakaya sunansu sunce yan ta’adda sun fi yi masu kisa fiye da cutar cobid 19 don haka suna kira ga Gwamnatin tarayya ta daure ta taimakesu a turo masu yan sandar kwantar da tarzoma hade da Karin Sojoji domin Allah ya kawo masu karshen wannan bala’i da suke ciki.

Ministar jinkai da walwalar al’umma, Hajiya Sadiya Farouk (a tsakiya), tana duba asibitin da hukjumar bunkasa yankin arwa maso gabas ta samar wanda ta kuma kaddamar a madadin shugaba Muhammadu Buhari aka kuma mika wa gwamnatin jihar Borno don amfann ‘yan gudun hijira a garin Maiduguri ramar Juma’a, 26 /6/ 20. Gamnann jihar Borno Babagana Zulum ne ke atre da ita.
Advertisement

labarai