Ta’addanci: Bakin Ne Ke Kawo Bindigogi A Ba Su Zinare A Zamfara -Matawalle

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce ‘yan kasashen waje suna musayar makamai da zinare da sauran albarkatun ma’adinai mai daraja a jihar sa.

Shugaban Kasa Muhammadu Da Bello Matawalle Gwamnan Jihar Zamfara yayin da yake nuna zinare da wasu ma’adinai da ake hakowa a jiharsa.

Matawalle ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar Shugaban kasa bayan gabatar da wasu zinari da wasu ma’adinai masu daraja da aka hako a cikin Jiharsa ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a gidansa, Abuja.
“Yana da matukar mahimmanci a gare mu a matsayinmu na gwamnati, musamman, batun rashin tsaro, mu san asalin matsalar rashin tsaro. An albarkaci jihar Zamfara da albarkatun ma’adinai da yawa kuma wasu mutane a cikin kasa suna shigo wa don siyan zinare da wasu ma’adinai, kuma wani lokacin maimakon su biya mutane kudi, sai su biya su da makamai. Na yi wasu bincike. Don haka, gwamnatin jihar za ta sayi wasu daga wadannan ma’adanai domin mu toshe wannan barakar. Don haka, yanzu haka gwamnatin jihar tana shiga tsakanin masu hakar ma’adinan. Za mu sayi wasu zinare daga gare su duk da karancin albarkatun da muke da su, ”in ji shi.
Ya ce gwamnatinsa ta yanke shawarar rungumar shirin Shugaban kasa na Artisanal Gold Mining Development Initiative don dakatar da aikata laifin da masu hakar ma’adanai ba bisa doka ba ke gudanar wa a jihar.

Matawalle, wanda ya ce a yanzu haka gwamnatin jihar tana janyo masu hakar ma’adanan jikinta ta hanyar siyan wasu daga zinaren dake gare su, ya jaddada cewa ya sanar wa shugaban kasa abubuwan dasuke damun jihar tasa na bangaren masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.

 

Exit mobile version