Umar A Hunkuyi" />

Ta’addanci: Buhari Ya Kadu Da Yawan Wadanda A Ka Kashe A Sakkwato

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna damuwa da kaduwarsa a kan adadin mutanen da su ka rasu a hare-haren ta’addancin da a ka kai ranar Asabar a wasu al’ummai uku da ke karamar hukumar Rabah ta Jihar Sakkwato.

Shugaban, wanda a ka ba shi labarin abinda ya faru din da kuma kame-kamen da ’yan sanda su ka yi ya zuwa yanzun, ya yiwa Gwamnan Jihar ta Sakkwato, Aminu Tambuwal da al’ummar Jihar ta’aziyya a kan rashe-rashen da a ka yi.

Shugaba Buhari ya soki duk wasu ayyuka na tarzoma da ta’addanci a kan ‘yan Nijeriyan da ba su ji ba, ba su gani ba. Ya kuma tabbatar da doka za ta yi aiki a kan duk masu aiwatar da irin wadannan ayyukan. Cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasan, Garba Shehu, ya shelanta, shugaban kasan ya yi addu’ar hanzarin samun saukin wadanda aka jikkata a lokacin harin.

Ya kuma bayar da tabbacin gwamnatin na shi ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kan fafatawan da take yi da ‘yan ta’adda da masu satar Shanu a ko’ina cikin kasar nan.

Exit mobile version