Daga Khalid Idris Doya
Ministan yada labarai da al’adu a Nijeriya Lai Muhammad, ya zargi wasu manyan kasashen duniya da cewa su ne ke kawo cikas ga Nijeriya wajen samun makaman da ake bukata domin tabbatar da yaki da ‘yan ta’adda a fadin kasar.
Kamfanin Dillacin Labarai ta kasa (NAN) ya habarto cewa, Alhaji Lai ya shaida hakan ne a birnin Makurdi ta jihar Benuwai a sa’ilin da ya ziyarci gwamnan jihar Gwamna Samuel Ortom ziyara.
“Ba za mu taba daina kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba. Wajibi ne kuma mu sani cewa mu na fada ne da ‘yan ta’addan da ke samun kudi daga ko’ina a duniya saboda haka muna bukatar hadin kai daga kasashen duniyar.
“Misali, Nijeriya ta yi yunkurin sayo makamai da hanyoyi domin yaki da ‘yan ta’adda, amma saboda wani dalili kasashen sun hana makaman.”
Ministan ya ce amma duk da hakan gwamnati za ta ci gaba da kokarinta har sai ta ga bayan ‘yan ta’addan da suke addabar kasar nan.
A ‘yan kwanakin nan dai gwamnatin shugaba Buhari tana shan suka matuka kan matsalolin tsaro musamman bayan kisan kiyashin da aka yi wa manoma a kauyen Koshebe ta jihar Borno, lamarin da ya kara ingiza jama’a wajen kushe kokarin gwamnatin kan yaki da ‘yan ta’adda.