Khalid Idris Doya">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Ta’addanci: Gwamnan Zamfara Ya Dakatar Da Shirin Gurfanar Da Kakakin APC

by Khalid Idris Doya
December 23, 2020
in LABARAI
2 min read
Gwamnan Zamfara
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya dakatar da shirinsa na daukan matakin shari’a a kan mai rikon mukamin sakataren watsa labarai na jam’iyyar APC, Yekini Nabena bisa wani zargin da aka ambato shi na yi a kan gwamnan.

Shi dai Kakakin na APC a makon jiya ranar Alhamis, ya zargi wani gwamna daga cikin gwamnonin arewa maso yamma da taimaka wa ayyukan ‘yan ta’adda musamman ‘yan bindiga a wannan shiyyar biyo bayan garkuwa da daliban makarantar Kankara.

samndaads

Duk dai da cewa a rahotonnin da aka yada, shi Yekini bai fito balo-balo ya kira sunan gwamnan Zamfara ba, amma alamu sun nuna da shi yake yi, kuma har hakan ta kai ga gwamnan daukan matakin cewa zai je kotu domin neman hakkinsa na kokarin bata masa kima da mutunci, amma sakamakon shiga tsakani, gwamnan ya dan jinkirta matakin kawo yanzu.

A wani hirarsa da ‘yan jarida a ranar Talata, gwamna ya shaida cewar zargie-zargen sun tsaya masa a wuya bai kuma ji dadi ba, amma ya dauki matsayar dakatar da shirinsa na maka kakakin APC din a kotu biyo bayan shiga tsakani da kwamitin riko na jam’iyyar APC tare da kungiyar gwamnoni suka yi.

“Na jinkirta matakin tafiya kotun don kalubalantar kakakin APC ne biyo bayan matakin da jam’iyyar ta dauka na cewa za ta ladabtar da Yekini bisa rashin amincewa da gamsuwa da zargin da ya min ni da gwamnatina.

“Idan za ku iya tunawa kwanan nan, a ranar Alhamis din makon jiya, 17 ga watan Disamban 2020, mai rikon mukamin sakataren watsa labaran jam’iyyar APC, Mista Yekini Nabena ya yi wani bayani mai tsarkakiya wanda ba a tabbatar da shi ba a kaina da gwamnatina, inda ke zargi na da agazawa, daukan nauyi da taimakon ‘yan bindiga a shiyyar arewa maso yammacin kasar nan.

“Wadannan zarge-zargen sun yi tsauri matuka wadanda ba za a iya burnesu a karkashin tabarma ba, musamman ma batun da ya shafi lamuran rayukan jama’a, mutuntaka da kimata,” a cewar gwamnan.

Gwamnan ya kuma shaida cewar tun lokacin da ya zama gwamnan jihar Zamfara ya tashi tsaye wajen bada gudunmawarsa inda aka samu tsarkake jihar daga inda ya amsa na tabarbarewar lamuran tsaro, yana mai cewa an samu cigaba sosai da yadda ya amshi gwamnan jihar.

“A lokacin baya Zamfara ta kasance jiha mai hatsarin zama ko ziyara, sakamakon yawaitar kashe-kashe, garkuwa da mutane, satar shannu da lalata kadarorin jama’a, amma yanzu idan aka kwatanta da baya an samu nasarori sosai kan wannan lamuran,” inji shi.

Ya kuma nisanta kasansa da dukkanin zarge-zargen da shi Kakakin APC ya yi masa, inda ya yi nuni da cewa yana zaman jiran matakain da APC za ta dauka kafin ya je ga matakinsa na gaba, inda ya ce muddin bai gamsu da hukuncin da uwar jam’iyyar APC za ta dauka a kan shi ba, to zai yi tunanin matakin da ya dace ya dauka domin wanke sunansa da kuma kimarsa.

SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamnati Ta Raba Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Rutsa Da Su

Next Post

Rundunar Sojin Sama Ta Kara Firgita ’Yan Boko Haram A Borno

RelatedPosts

Zaben Dan Majalisa

Za A yi Zaɓen Gwamnan Anambara Ranar 6 Ga Nuwamba – INEC

by Khalid Idris Doya
38 mins ago
0

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa a ranar...

Ogun

Fashewar Tankar Mai Ya Ci Rayuwar Mutum Uku Da Jittaka Shida A Ogun

by Khalid Idris Doya
8 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya, A ranar Talata ne mutum uku...

Bafarawa

’Yan Nijeriya Sun Fi So A Magance Rashin Tsaro Fiye Da Korona, Cewar Bafarawa

by Khalid Idris Doya
8 hours ago
0

A Juya Kuɗin Rigakafin Cutar Naira Biliyan 400 Zuwa Tsaro...

Next Post
Rundunar Sojin Sama

Rundunar Sojin Sama Ta Kara Firgita ’Yan Boko Haram A Borno

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version