Connect with us

RAHOTANNI

Ta’addanci: Sojojin Nijar Sun Hallaka ‘Yan Bindiga A Sokoto

Published

on

An tabbatar da cewa daruruwan ‘yan bindiga ne sojojin tarayyar Nijar suka kashe ajiya safiyar Litinin. Majiyar tace, sojojin sun kai farmakinne da misalin karfe 3:15 na dare.
Majiyar sunce sojin Nijeriya sun kashe sama da ‘yan bindiga 100 sun kuma kone maboyarsu a garin Burqusuma, da ke kan iya kokin Nijeriya da tarayyar Nijar
Sojojin Nijeriya da Sojojin tarayyar Nijar babu wanda yatabbatar da wannan kai harin amma shugaban kungiyar “Movement For Social Justice” dake Sokoto da mazauna garin su suka tabbar da faruwan lamarin.
Altine yace:” Jami’an tsaron sunzo ne tsakiyar dare lokacin da ‘yan bindigan ke bacci, a yayinne sojin sukakai farmaki, har sukai nasarar kashe sama da mutum 100, su ka kama dayawa daga cikinsu sannan suka kone mashinan hawansu.
Yana daga cikin muhimman abubuwan dasukasa akai nasarar kamesu, wannan shahararran mai garkuwa da mutane, wato Sarkin Fawa Shago yana hannun sojin Nijar a tsare.
Wani mazaunin garin mai suna magaji ya gayawa jaridar HumAngle cewa ” Lokacin da jamian tsaron Sukazo duk guduwa mukayi. Kuma wannan bashine nafarko ba da sojin Nijar ke shigowa don neman kame wadannan ‘yan bindigar.”
An tambayeshi, ko sojin sun kashe wani farar hula, ko sun kona dukiyar mutanen kauyen? Magaji ya bada amsa da cewa “Wasu cikin ‘yan bindigar sun maida wuta yayin farmakin, wasu kuma sun gudu daji da raunuka. To bazan iya saniba ko akwai wani farar hula da yayi rauni, tunda mudai guduwa mukayi don ceton rayukan mu.”
Majiya ta gayawa HumAngle cewa anga sojin agarin Dan Ayagi dake kan iyaka kusa da Bangi dake Tarayyar Nijar.
Majiyar tace, Sojin Nijeriya suna kula da Iyakokin kasar Nijeriya akan hare-haren da akakai kwanakin baya a Karamar hukumar Sabon Birni.
Advertisement

labarai