A ci gaba da kokarin da ta ke yi na bunkasa samar da kayan aiki don ci gaba da gudanar da ayyukan da ake bukata a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya, rundunar sojin saman Nijeriya (NAF) ta kammala aikin dawo da wasu jiragen sama guda 2 na ‘L-39ZA’ a cikin kasar, tare da hadin gwiwar ainihin kayan aikin masana’antu na ‘Messrs Aero Bodochody’ na jamhuriyar Czech, tare da hadin gwiwar injiniyoyin NAF da masu fasaha.
Wannan sanarwar ta fito ne daga hannun Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola, a inda yake cewa, bikin mika jiragen 2 ya gudana ne a ranar 4 ga Disamba 2020, a makarantar horar da tukin jirgi na NAF (403 FTS), Kano.
Daramola ya ce, daidaita Shirye-shiryen cigaban rayuwa a cikin jirgin NAF, wanda ba a taba yin irin sa ba a tarihin Nijeriya, na daya daga cikin nasarorin da rundunar NAF ke samu a yanzu. Aikin da aka kammala akan jiragen 2, shine sabon salo a cikin jerin, kuma zai kara habaka adadin wadatattun jiragen sama don NAF don ci gaba da aiwatar da ayyukan da suka dauru da wuyar ta.
Da yake jawabi yayin bikin karba da mika jiragen, babban bako kuma babban jami’in, Shugaban hafsan sojojin sama (CAS), Air Marshal Sadikue Abubakar, ya bayyana cewa, aikin sake farfado da jirgin L-39ZA din na uku, shi ma yana ci gaba a hankali, tare da tabbacin cewa, za a kammala kuma a ba da shi mako mai zuwa.
Shugaban ya ci gaba da cewa, tsaro ba wai kawai game da jirgin sama ba ne, da bama-bamai, harsasai da rokoki, amma yana bukatar sa hannu da hadin kan dukkan ‘yan kasa. Don haka ya yi kira ga duk ’yan Nijeriya masu kyakkyawar manufa da su yi amfani da karfi wajen gano abin da sojojin da sauran hukumomin tsaro ke yi tare da tallafa wa kokarinsu na kawar da kasar daga dukkan makiyanta.
Da ya ke ci gaba da magana, Air Marshal Abubakar ya bayyana cewa, a matsayin wani bangare na shirye-shiryen kara inganta yanayin aikin jiragen sama, rundunar tana gab da kammalawa ayyukan ‘Depot Maintenance (PDM)’ da kuma ‘abionics upgrade’ da karin jirage 2 na ‘Alpha-Jet’ a rukunin horar da jami’ai na 407, Kainji.
Ya kuma bayyana cewa, jirage 2 na F7-Ni suna cikin kulawa a Makurdi, yayin da ake jigilar nau’ikan jirage guda 7 zuwa China don yin kwaskwarima da habaka ‘abionics’.
Ya ce, “Shirye-shirye suna cikin manyan kayan da za su gudanar da babban bincike kan jirage masu saukar ungulu na ‘Mi-24B’ da ‘A-109’, yayin da aka kammala shirye-shirye don PDM kan karin jiragen ‘C-130H (NAF 918)’, kuma ana shirin fara aikin ne daga Farkon shekara mai zuwa. Wannan zai kawo adadin 3 na jirgin ‘C-130H’ da aka samu nasarar sake farfado da su a cikin kasar, abin da ba a taba yin irinsa ba a tarihin shekaru 56 na NAF. “
“Bugu da kari, rundunar ta dauki isar da karin jirgi mai saukar ungulu na Mi-171E a cikin makon. Wadannan wasu kananan nasarori ne da tsare-tsaren rundunar a cikin yunkurinta na adana manyan jiragen sama don saduwa da bukatun ayyukan kasar”, in ji CAS.
A cewarsa, an kara fadada aikin makarantar don tallafawa ayyukan kawar da tayar da kayar baya a yankin arewa maso gabas da kuma ayyukan yaki da ‘yan bindiga a Arewa maso yamma.
“Dole ne in ce makarantar ta yi daidai da abin da NAF ke tsammani kamar yadda ta ci gaba da samar da manyan matuka jirgin sama na NAF, da samr da kayan ayyukan sama da ake bukata don ayyukan tsaro na cikin gida da ke gudana. A wannan shekara kadai Makarantar ta yaye matukan jirgin yaki guda 4 kamar yadda sauran Matasan jirgi (SPs) guda 6 suka sami nasarar kammala shirin horon su na 90%”, in ji Shugaban.
Yayin ya ke taya murna ga Kwamandan Sojan sama da ke ba da umurnin horon Sama (AOC ATC), Air Bice Marshal (ABM) Musa Mukhtar, da kuma Kwamandan 403 FTS don nasarorin da suka samu, shugaban ya yi amfani da wannan damar wajen bayyana babban godiyar NAF ga Kwamandan askarawan kasa, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Mai girma Ministan tsaro da mambobin majalisar kasa saboda irin goyan bayan da suke ba shi na tabbatar da cewa an samarwa Sojojin da isassun kayan aiki don tunkarar kalubalen tsaro, duk irin tabarbarewar da tattalin arziki ya yi.
Ya ce, “Muna mika godiyarmu ta musamman ga shugaban kasar kan wannan karimci tare da sake jaddada cikakken biyayyarmu ga shugaban kasar musamman a kokarinsa na samar da zaman lafiya da tsaro a cikin al’ummarmu mai daraja,”.
Har ila yau, Shugaban ya yaba wa kokarin abokan hulda daga ‘Aero Bodochody’ da kuma injiniyoyin NAF masu hadin gwiwa da masu fasaha don isar da aikin a kan lokaci.
Tun da farko a jawabinsa na maraba, Kwamandan 403 FTS, Skuadron Leader Mansur Yusuf, yayin da yake yabawa da kokarin shugaban, ya bayyana cewa, sake farfadowa da sakin jirgin ga NAF babu shakka zai bunkasa karfin gwiwa a ci gaba da yaki da masu tayar da kayar baya da ‘yan bindiga a cikin kasar, yayin da ya ke kara darajar horar da matuka jirgin NAF. Ya kuma tabbatar wa da shugban da jajircewar ma’aikatan 403 FTS don yin amfani da kariya ta hanyar amfani da dandamali kamar yadda rundunar da al’umma ke samun kyakyawan nasarori.
“Na yi imanin cewa babu wata hanya mafi kyau da za ta iza matuka jirgin sama, face samar samu da ingantattun jiragen sama su tashi”, in ji shi.
Makasudin wannan taron shi ne karbuwar sabon jirgin da aka sa ke farfado da shi, wanda ke dauke da wasu abubuwa na sararin samaniya wadanda NAF da ‘Aero Bodochody’ matukan jirgi suka aiwatar cikin gwaninta. Hakan ya biyo bayan sanya hannu da kuma mika takardun jirgin daga ‘Aero Bodochody Technical Team’ zuwa Shugaban babban injiniyan NAF (CAcE), ABM Musibau Olatunji. Musibau daga baya ta ba da takardun ga shuguban sojin saman, wanda shi kuma ya ba da su ga shugaban horarwa da ayyuka, ABM James Gwani, wanda ke alamar sakin jirgin wajen horo da sauran ayyuka.
Har ila yau, wannan gagarumin taron ya gabatar da kaddamar da gidan tarihi na 403 FTS da ‘Hall of Fame’.
Sauran wadanda suka halirci taron sun hada da manyan jami’ai daga hedikwatar NAF tare da Kwamandojin rundunonin soja da ke Kano da kuma shugabannin hukumomin tsaro a Kano da mambobin Filin tashin jirgin sama na Malam Aminu Kano.