Ta’addanci: Za mu Goyi Bayan Nijeriya Don Kawo Ƙarshen Boko Haram —Gwamnatin Ingila

Daga Abubakar Abba

Gwamnatin ƙasar Ingila ta sha alwashin za ta ci gaba da mara wa gwamntin Nijeriya baya, wajen kawo ƙ arshen ta’addancin ‘yan ƙ ungiyar Boko-Haram.

Ministan Rundunar Soji na ƙasar, Mark Lancaster ne ya bada wannan tabbacin bayan da ya kai ziyarci cibiyoyin Sojoji da dama da ke shiyar Arewa-aso-gabas, inda jami’an Soja na ƙ asar ta Ingila, ke bai wa Sojojin Nijeriya horo na musamman don daƙ ile  hare-haren ‘yan Boko-Haram.

Mark ya kuma gana da masu bada horon na musamman ga Sojojin na Nijeriya da ke yankin.

Sojojin na musamman suna kuma bada shawarwarin dabarun yaƙ i ga Sojojin na Nijeriya a kan yadda za a kawo ƙ arshen ayyukan ‘yan ƙ ungiyar ta Boko-Haram.

Duk a lokacin ziyarar, Mark, ya kuma kai wata ziyara Makurdi Babban Birnin jihar Biniwai da jihar  Kaduna don gana wa da jami’an Sojin ƙ asar ta Amurka da ke bai wa sojojin rundunar sojin Nijeriya horo na musamman.

Bugu da ƙ ari, Mark duk a cikinmakon, ya kai wata ziyarar ga Cibiyoyin soja na tsaro da a yanzu ƙ wararrun sojojin ƙasar ta Ingilla ke kan ba su horarwar ta musamman, ya kuma gana da manyan jami’an soja a Birnin tarayyar Abuja, a kan yadda ƙ asarsa, za ta ci gaba da taimaka wa Nijeriya, don magance ƙ alubalen da ƙ asar ke fuskanta na tsaro.

Ministan ya ce,”Gwamnatin Ingila tana tare da Nijeriya a kan ƙ oƙ arinta na kakka ɓ e ta’addanci a ƙ asar.”

A cewar sa,”Ƙ wararrun sojojinmu da suka yi fice a duniya, suna taimaka wa sojojin Nijeriya don su samu horo na musamman yadda za su dumfari yaƙ i da ta’addanci na ‘yan Boko-Haram.”

Ya ce, a bisa ƙ wararrun sojojinmu da muka girke a Arewa-maso-yamma, za su bai wa sojojin Nijeriya da aka tura yankin a kan yadda ake kwance bama-bamai da ‘yan ƙ ungiyar ta Boko-Haram ke sanya da kuma ƙ asar baki ɗaya, ya ƙ ara da cewar Igila ta boɗe hanya wajen bai wa Nijeriya goyon baya don kare ƙ asar daga ta’addancin na ‘yan Boko-Haram.

Tun lokacin da gwamnatin ƙ asar Ingila ta fara taimaka wa rundunar sojin Nijeriya wajen gangamin yaƙ ar ta’addanci ta hanyar koyar da sojojin kwasa-kwasai da horar wa da ka aka yi masu zuwa yau, sun samu horas wa a kan darussa da suka haɗa da, dabarun yaƙ i da maida martani a kan hare-haren ‘yan ta’adda da dabarun kwance bama-bamai a duk inda aka dasa su da tsare-tsaren gudanar da yaƙ i da shugabanci don daƙ ile barazanar ta ‘yan Boko-Haram da kuma ayyukan jin ƙ ai.

Ƙ asar Nijeriya tana ɗaya daga kan gaba wajen yin haɗin gwiwa da ƙasar Ingila wajen yaƙ ar ta’addanci a nahiyar Afirka, kuma Igila da Nijeriya, sun jima suna yin haɗin gwiwa, inda ƙ asar ta Ingila ta turo ƙ wararrun sojojinta  40 don bai wa sojojin Nijeriya horo na musamman da

kuma ba su shawarwari na dabarun yaƙ i. Ƙasar ta Ingila, ba wai tana ƙ ara wa Nijeriya ƙ arfi ba ne wajen maida martanin a kan ta’addacin ƙ ungiyar Boko-Haram ba ne kawai, amma Sojojin ƙasar ta ingila, suna kuma aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙ awar ta ƙ asar Jamani wajen haɗin giwa da sojojin ƙ asa da ƙ asa, don taimaka wa wajen ƙ arfafa magance dasa bama-bamai.

Har ila yau, ƙ asar Faransa da Amurka da ita Ingila, suna bada ɗauki ga yankuna wajen samar da bayanai da tsare-tsare tsakanin Nijeriya da ƙ asashen da Nijeriya ke maƙ wabtanta da su ta hanyar ‘yan ƙalilan ɗin ƙ wararrun jami’an soja da Ingila ta turo haɗe da dakarun Soja na ƙ asa da ƙasa da ke a shalkwatar N’Djamena cikin ƙasar Cadi.

Gwamnatin Ingila, ita ce ƙ asa ta farko da ta fara bada gudummawa ga sojojin Nijeriya da dakarun soja na ƙ asa da ƙ asa, naFam Miliyan 5 don sayen makamai.

In za a iya tuna wa, sama da ƙwararrun jami’ain sojin ƙ asar Ingila 700 ne, aka turo  Nijeriya don horar da sojojin Nijeriya na gajeren lokaci don taimaka wa sojojin da ke fagen fama horarwa ta musamman  tun farko shekarar 2015.

Bugu da ƙ ari, sama da jami’an soja 28,500 ne, gwamnatin Ingila ta horas a kan ilimin tsaro a wannan lokacin.

Gwamnatin Ingila ta bayyana cewa, a shirye take, don ƙ arfafa dangantakar ta da Nijeriya wajen taimaka wa harkar tsaro kuma tasha alwashin baza ta yi ƙ asa a gwiwa ba, wajen bai wa sojojin ƙ asar hararwa ta duniya ta zamani,don magance ta’addanci a ƙ asar nan.

Exit mobile version