Daga Mahdi M. Muhammad,
Shugaban Rundunar Sojojin Saman Nijeriya Air Marshal Oladayo Amao, ya bayyana kwarin gwiwar cewa, rundunar za ta share ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka a Nijeriya nan gaba kadan.
Ya yi wannan alkawarin ne a lokacin cin abincin bikin Easter tare da mambobin tawagar ‘013 Fast Response Force’ da ke Minna, inda ya yi ta’aziyya ga iyalai da abokan aikin matukan jirgi uku da suka mutu a aikin Allawa a ranar 1 ga Afrilu, 2021.
Air Marshal Amao ya sake tabbatar da kudurin Shugaba Muhammadu Buhari da na sojojin saman Nijeriya na kawo karshen tawaye da ‘yan bindiga.
Shugaban hafsan, wanda ya samu wakilcin Air Bice-Marshal Remikius Ekeh, ya yaba wa rundunar ta 013 da ke ba da agajin gaggawa da kuma bangaren rundunar na ‘Operation GAMA AIKI’, da kuma jajirtattun jami’an sojojin sama maza da mata, kuma ya bukace su da su ci gaba da tsayawa kyam a cikin yaki da tayar da kayar baya da ‘yan ta’adda.
Ya gaya musu cewa, kada su karaya a kan jajircewarsu da kuma aiki tukuru domin cika alkawuran kare rayukan ‘yan Nijeriya da dukiyoyinsu.
Shugaban NAF din ya tabbatar da cewa, ana ci gaba da kokarin kwato jirgin NAF na ‘Alpha Jet Aircraft’ da ya fadi, wanda aka ce ya bata a ranar 31 ga Maris, 2021.
Ya bayyana cewa, labarin wai ‘yan ta’adda ne suka harbo jirgin, karya ne.
Lokacin da aka gama binciken, ya sha alwashin cewa za a gabatar da duk hujjojin da ke akwai