Ta’ammuli Da Kwayoyi: NDLEA Ta Bukaci Majalisar Yobe Ta Yi Wa Tufkar Hanci

????????????????????????????????????

Hukumar sha da hana fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a jihar Yobe, ta yi kira ga majalisar dokokin jihar da cewa ta samar da dokokin da zasu dakile bazuwar wasu sabbin hanyoyin gargajiya wadanda matasa kan yi amfani dasu masu gusar da hankali. Sabbin hanyoyin sune amfani da kashin kadangarru da zakami tare da fetur, a matsayin kayan sa maye.

Shugaban hukumar a jihar Yobe, Mista Apeh Reuben, ne yayi wannan kiran a karshen wannan mako, a sa’ilin da yake zanta wa da manema labarai a ofishin sa dake Damaturu, babban birnin jihar.

Yayin da ya bayyana cewa wadannan ayari na kayan shaye-shaye masu sa maye; mafi akasari, matasa ne ka kwankwadar su, a sabon salon dabarar kaucewa kamun jami’an NDLEA a duk lokacin da suka fito aiki.

“Sannan kuma, duk da yake ana yin wadannan kayan maye ta hanyar gargajiya, zasu haifar da babban lahani ga lafiyar masu shan su. Har yau, kayan maye ne wadanda basu cikin jerin miyagun kwayoyin da doka ta hana(a hukumance), saboda wannan ne muke kira ga majalisar dokokin jihar kan ta samar da dokar hana shan wadannan nau’i na kayan mayen domin ceto rayuwar matasan mu”.

Reuben ya sake nusar da cewar wannan sabuwar hanyar shan kayan maye, dada ruruwa take a kowacce rana duk da yadda suke kokarin dakile ta, amma dai ya ce suna bukatar matakan doka domin kare rayuka fadawa munan hadura ga manyan gobe.

Ya kara da bayyana cewa, a cikin yan watanni kadan, hukumar su ta damke mutane 217 wadanda take zargi da sayar da miyagun kwayoyi a jihar, kana da kama kayan maye, wadanda nauyin su ya kai kilo gram 1,165,456 na tabar wiwi hadi da gram 109,827 na dangogin ta.

Har wa yau ya sake bayyana cewa, a cikin watan Junairun 2018 kadai, hukumar su ta cafke mutum 24 da take zargi da fataucin miyagun kwayoyi tare da mashayan su- ciki har da mace, da miyagun kwayoyin da nauyin su ya kai kilo gram 120,205.

Kwamandan wanda ya nuna aihinin sa dangane da yadda yaduwar sha da safarar miyagun kwayoyi a jihar Yobe, ya sake cewa, a cikin watani 13; kadai, sun kama mutane 222 da suke zargi da ta’ammuli da miyagun kwayoyin.

“Kuma tuni muka gurfanar da mutane 32 a kotu, 16 daga cikin su a cikin wannan wata na Janairun 2018 ne, inda kuma sauran ke ci gaba da zaman rima, a babbar kotun tarayya (Federal High Court),  Damaturu. Sannan kuma wannan yanayi ne abin damuwa sosai.”

Kwamandan ya nemi samun cikakken goyon baya da hadin kan gwamnati da kungiyoyi masu zaman kan su, tare da bayar da tabbacin tsayuwar dakan hukumar NDLEA wajen shawo kan matsalar sha da safarar miyagun kwayoyin birki, kamar yadda doka ta gindaya.

“Har wala yau kuma, mun gudanar da shirin wayar da kan al’umma a makarantun sakandire domin rage kaifin matsalar”. Inji shi.

 

Exit mobile version