Idris Aliyu Daudawa" />

TAAT Za Ta Bun kasa Kiwon Dabbobi

Masana ilmin fasaha na Afirka sun yi taro na kwana daya da masu ruwa da tsaki, a al’amuran aikin gona, da niyyar samun wata hanya wadda za a samu bun kasaal’amarin daya shafi, kiwon dabbobi wa danda ba yawa gare su ba, saboda a bun kasa kiwon anda hakan zai sa har ma a ri ka kais u zuwa kasashen waje wajen kasuar dabbobi.
Da yake jawabi lokacin da aka fara taro na kaddamar da kiwon dabbobi wa danda suke kanana , darektan kasa da kasa na cibiyar koyar da ilmin kiwon dabbobi Dokta Tunde Amole ya bayyana cewar shi taron an shirya shi ne saboda, a kara ma masu kiwon dabbobi, ilmi na yadda zasu lura dasu kamar yadda ya dace, bugu da kari kuma a samu karin hanyoyin da za a samu hul da da masu bada rance, da niyyar saboda a samu wata ha din guiwa dasu.
Da yake magana da manema labarai bayan da aka kammala taron Shugaban hukumar bun kasa aikin noma ta jihar Kano Farfesa Mahmud Daneji, ya bayyana cewar shi taron an yi shi shi ne lokacin da ya kamata, inda kuma ya kara jaddada cewar gwamnatin jihar Kano tana jiran bayanan bayan taron , saboda ta san koda akwai wuraren da zata taimaka.

Exit mobile version