Ci gaba daga makon jiya
Siyasarsa
Za a iya cewa, Nda-Isaiah, ya fara aiwatar da manufarsa ta siyasa ne tun a fagen rubuce-rubuce da ya jima yana yi a Jaridu, sai daga baya ne ya fado tsundum cikin fagen siyasar a aikace fafur, musamman lokacin da ake kici-kicin hadakar jam’iyyar APC.
Cikin sakon ta’aziyyar gwamnan jihar Ogun, Prince Abiodun, ga iyalan Nda, ya tabbatar da cewa, marigayin, na yin siyasa ne da akida, tare da son cigaban al’uma. A aikace, Ndan, ya nuna haka a lokacin da Buhari ya ka da shi a takarar da ya yi. Bai ta da rikici ba, bai ce, sai shi ne kadai ba ya cancanta a zaba. Ta tabbata shi ne ma ya jagoranci bangaren yada labarai na takarar Buharin, har zuwa lokacin da aka sami nasara. Ga shaidar kyakkyawan salon siyasar tasa da gwamna Abiodun ke shelantawa;
“…The country has lost a rare gem of big ideas, whose politics was laced with conbiction, selflessness and without bitterness. Iam still in shock. I was jolted by the news”.
Ga fassarar kalaman;
Ta tabbatar marigayi Nda, na yin gwagwarmayar siyasa ne kadai, don son ganin rayuwar al’uma ta inganta, ba don zari ko halayya ta cinye-du ba!!!.
“…Sam Nda-Isaiah was a resolute and dogged fighter on the side of the people…”.
Ogun State Gobernor
Cikin Harshen Hausa, ga abinda gwamnan ke cewa;
“…Sam Nda-Isaiah kuwa, ya kasance dan gwagwarmaya mai kwazo, a kullum ba ya kosawa cikin fafutukar kwatowa al’uma hakkokinsu…”.
Kyankyasar Jaridar Leadership
A karshe, babu shakka al’umar Najeriya manyansu da kananansu, na masu mika sakon ta’aziyyarsu ga Iyalai, “yan’uwa, ma’aikatan gidan Jaridar ta Leadership, jihar Niger da ma sauran al’umar Kasar nan bakidaya, bisa rasuwar wannan Dan Kishin Kasa, Sam Nda-Isaiah, Aare Baaroyin na masaraurar Akure, bisa katafariyar gudunmuwar da ya bayar tsawon lokaci ga mabanbantan fagage na rayuwa cikin wannan Kasa. Mu na masu fatan kyawawan ayyukansa su bi shi, tare da zame masa manyan gwala-gwalen nasara cikin wannan Duniya da muke ciki.
Kammalawa.