Bello Hamza">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Ta’aziyyar Rasuwar Malam Umar Hunkuyi, Editan Labarai

by Bello Hamza
December 20, 2020
in RAHOTANNI
6 min read
Ta’aziyyar Rasuwar Malam Umar Hunkuyi, Editan Labarai
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A ranar Laraba 16 ga watan Disamba 2020 ne Allah ya yi wa abokin aikimu Malam Umar Abubakar Ciroma rasuwa bayan ya yi fama da rashin lafiya a gidansa da ke Kaduna, ya rasu ya bar mata daya da yara 16, Muna addu’ar Allah ya gafarta masa, ga ta’aziyyar wasu daga cikin abokan aikimu akan rasuwar.
Mun Yi Rashin Dattijon Arziki—Musa Muhammad, Babban Shugaban Gudanarwa
Malam Umar Abubakar Ciroma, dattijo, hazikin ma’aikacin da ba ya kasala a harkar aiki. Gaskiya rashin Malam Umar ba karamin rashi ne LEADERSHIP A Yau ta yi ba, musamman Editoci, wadanda su ne ke hulda da shi kai tsaye.
Malam Umar mutumin ne da zai yi wiya ka nemi shi a waya game da wani aiki, ya zama ba ka same shi ba, ko kuma ka same shi, amma ya kawo maka uzuri. Na san akwai lokuta da dama da Malam Umar ke takura wa kansa don ya biya bukatar wurin aikinsa.
Lokacin da ya kwana a asibiti na farko, ina Abuja ban samu na je Kaduna don duba shi ba, har sai karshen wani mako, bayan na ajiye jakata a gida na wuce asibitin da aka kwantar da shi. Bayan na shiga na tambayi dakin da ya ke, sai wata ma’aikaciya ta ce mani ai an sallame shi a ranar. Ba tare da bata lokaci ba na wuce gidasa da ke Abuja Road, Rigasa Kaduna.
Na je na same shi jiki ya yi sauki, har ma saboda karfin hali da kwazo irin na Malam Umar ya ke ce mani, yana jin in ma bai fara aiki a kashegari ba, to in Allah ya yarda jibi zai fara. Haka kuwa aka yi, jibin nan sai ga Malam Uamr ya fara aikinsa, har ma Edita, Nasir Gwangwazo yana mamaki.
Na san Malam Umar shekaru masu yawan gaske, mun yi aiki kut da kut da shi, mun zauna teburi da teburi tare. Mutum ne mai girmama kowa, mutum ne mai son raha, mutum ne da ban taba ji ko ganin wanda suka yi fada ko sa-in-sa da shi ba, ban taba ji ko ganin ana ba shi hakuri kan suna husuma da wani ba.
Ni dai ba abin da zan ce illa, Allah gafarta wa Malam Umar, Allah ya rahamshe shi ya sa aljanna ce makoma, Allah ya sa jinya ta zama kaffara. Mu kuma da sauran iyalansa, Allah ba mu hakurin wannan rashi, Allah kawo mana kwafinsa a teburin Editan Labarai.

 

samndaads

 

Malam Umar Abubakar Ciroma Muntum Kirki Ne- Muhammad Awwal Umar, Daga Minna
Inna Ilillahi Wa Inna Ilaihir Raji’un!
Tabbas kowani mai rai mamaci ne, amma na kidimu a lokacin na da ga sanarwar rasuwar Malam Umar jiya da misalin karfe 2;16 na rana a group din Leadership AYAU na dandalin WhatsApp, a lokacin ina ofishin sakataren Etsu-Nupe kan ta’aziyyar Shaban Nupe da maigidan mu Mista Sam Nda-Isaiah ( Kakaki Nupe) bisa jagorancin kungiyoyin Media Action Group akan ayyukan hukumar HYPADEC da kungiyar Tinubu Support Organisation wanda duk ina da matsayi a cikinsu.
Mutum na farko da na fara kira dan tabbatarwa zuciyata abinda ta kasa fahimta shi ne Malam Musa Muhammad Awwal, wanda shi ne mafi kusanci gare shi da na san su tare tun muna jaridar Dillaliya, inda bayan jajantawa da tausayawa na tuntubi sauran Editoci abokan aiki, sannan na kira amininsa na kusa Malam Ibrahim Musa, editan jaridar Al-Mizan da kusan a kowani lokaci mu kan yi waya dan samun shawarwari sama da shekaru ashirin.
Haduwa ta da marigayi Malam Umar ta karshe, shi ne a babban dakin taro na Legbo Kutigi da ke Minna, lokacin da ya shigo tawagar Malam Nigga na Kaduna dan karbar lambar yabo daga gidauniyar Garkuwan Talba kusan shekaru biyu zuwa uku da suka gabata, mun tattauna wasu matsaloli da kuma neman shawarwarinsa akan abubuwan da suka tsaya min a zuciya.
Na san Malam Umar shekaru ashirin da suka gabata lokacin da na ke aikewa jaridar Dillaliya rahotanni daga Minna, shi ne ya tabbatar min da ID Card a matsayin wakilin jaridar a lokacin bisa amincewar marigayi Malam Tahir Gwantu da yake jagorantar jaridar a matsayin edita. Dukkan su marigayan Malam Ibrahim Musa ne ya hada ni da su, inda ya umurci su yi riko da hannu na dan nusan da ni akan aikin jarida.
Da kan sa ya ba ni labarin dawowarsa kamfanin Leadership, wanda mun yi maganganun da ya ba ni kwarin guiwa sosai, wanda ba mu taba samun cikakkiyar sati uku ba mu yi waya ba har zuwa kwanciyarsa asibiti da sallamarsa. Tabbas rashin Malam Umar babban rashi ne wanda ba zan taba mantawa da shi ba saboda irin gudunmawar da ya ba ni ta hanyar shawarwari da kwarin guiwa, na dauke shi wani jigo a rayuwata sosai, na kan hadu da shi a waya a duk lokacin da na shiga kunci kuma ba tare da son kai ko keta ba yana ba ni shawarwarin da kan taimaka min wajen fahimtar lamurra.
Allah ya jikan Malam Umar, ya karbi uzurinsa ya gafarta ma kurakuransa, yasa jinyar ta zamo hanyar wanke kurakuransa.
Ina jajantawa ‘yan uwa da abokan arziki akan wannan babban rashi da mu ka yi.
Muhammad Awwal Umar, Daga Minna, jihar Neja.

Na Yi Matukar Kaduwa Da Samun Labarin Rasuwar Malam Umar Chiroma—-Muhmmad Maitela
Na yi matukar kaduwa a lokacin da na samu labarin rasuwar Malam Umar Chiroma, saboda bakin gwargwadon sanayyar da ke tsakaninmu kana da yadda muka yi aiki dashi na dogon lokaci. Yayin da a wannan tsakanin mun shaku a kyakkyawar mu’amala.
Malam Umar mutum ne mai karimci, hakuri da dattaku, wanda iya mu’amalar da ta gudana tsakanin mu dashi, na shaide shi da siffofin da na bayyana da farko, sannan baya ga hakan, wayayyen mutum ne wanda ya fahimci rayuwa tare da juriyar zamantakewa da kowa.
Malam Umar ya kasance mutum mai kokari da fara’a a kusan kowane lokaci; mutum ne mai hadiye fushinsa wanda abu ne mai wahala ka fahimci bacin rai a fuskar sa. Sannan wani abun birgewa a rayuwar sa, a kusan kowane lokaci za ka ga yana kokarin bayyana tawali’u da bude kofar yi wa mutum uzuri, kuma ba ya kausasa zance balle ya rike mutum a zuci.
Ko shakka babu, iyalai da yan uwa, amminai tare da sauran abokan aikin Malam Umar Chiroma mun yi babban rashin dattijo kuma jajirtaccen mutum mai kima a idon kowa, musamman kamfanin jaridar LEADERSHIP A YAU, kana da sauran wuraren da yake aiki. Wanda bisa ga hakan ne, ina mai bayyana matukar alhini tare da mika jajen ta’aziyya ga iyalai, yan uwa da aminan Malam Umar Chiroma, kebance Editoci da sauran ma’aikatan jaridar LEADERSHIP A YAU.
Allah ya jikan shi da rahama kuma ya sa aljannatul Firdausi ce makomar shi kuma ya albarkaci yaran da ya bari, alfarmar Ya Rasulallah(s)!

 

Malam Umar Hunkuyi Dattijon Kwarai Ne—Khalid Idris Doya
Malam Umar Hunkuyi yana daga cikin dattajin mutanen da na ke matukar girmamawa da mutunta, hakan kuwa bai rasa nasaba da yadda marigayin yake da kyakkyawar alaka da mutunta kowa da kowa, ga kuma iya mu’amala da jama’a.
Marigayi dai a haife ya haifeni, amma bisa dalilin haduwarmu a fagen aiki ya kan daukeni da kima sosai wanda hakan ya bani damar mutuntashi da kimantashi ainun.
Haduwata da shi ido da Ido na karshe da shi tun ranar 23 ga watan Maris na 2019 a jihar Sokoto yayin da muka halarci bikin daurin auren Darakta, Idris Bala Sulaiman. A wannan lokacin, mun samu damar da marigayi ya karfafeni tare da kara min kuzari. Ya ke ce, “Khalid kana kokari a kara dagewa”, sannan a dan lokacin da muka yi a wannan ranar ya bayyana min wasu kalamai na mutuntawa da har yanzu suke tasiri matuka a gare da ni, dukka dai domin ya kara min karsashi da himmatuwa a fagen aiki
A matsayinsa na Editan Labarai na jaridarmu, duk wani lokacin da zai bukaci ka yi wani aiki, zai nemeka da rarrashi da salama, wanda har sai ka yi aikin cikin annashuwa ba tare da ma ka ji wani zafin aikin ba. Irin haka da dama ya wakana tsakaninmu.
Hatta wayar da muka yi da Malam Umar (marigayi) lokacin da zai tafi hutu domin jinyar rashin lafiyar da ke damunsa. Ya kirani domin na rike masa ayyukansa a wannan jaridar ya kirani cikin girmamawa, “Salamu Alaikum!” Na amsa da Wa’alaikumussalam, Malam ina wuni ya ayyukan. Ya ce sai godiya. Nan dai na yi shiru ina sauraronsa, sai ya ce da ni, “Malam Khalid ina son zan dan tafi hutu ne domin jinyar rashin lafiya da nake fama da ita. Don haka don Allah akwai takardar neman tafiya hutu da zan cika, sannan akwai inda zan sanya wanda wanda zai rike min ayyukana kafin na dawo, don haka zan sanya sunanka in ba matsala,”
Kimarsa a gareni da mutunta shi da nake ya sanya ko tari ban yi masa ba na amsa da cewa babu matsala Malam, Allah ya baka lafiya ya sanya kaffarace. Can na ji ya yi shiru daga baya ya katse wayar.
A zuciyata na yi ta jujjuya zancen, salon rokonsa da bukatarsa ta dattako ne, kankan da kansa da mu’amalarsa na mutanen kwarai ne ainun.
Bayan kama masa aikin da na yi na wucin gadi, wata rana ya turo mana da sakon neman addu’ar cewa an kwantar da shi a asibiti, muka yi ta masa addu’ar Allah ba shi lafiya. Bayan wasu ‘yan kwanaki ya sake sanar da mu cewa an sallameshi a asibiti har ma ya na kokarin kwashe kayayyakinsa domin komawa gida. Muka yi ta murna da jin hakan. Sannu a hankali har na ga ya dan rubuta wasu rahotonni da wani tattaunawa da ya yi da wani a kwanakin baya. Alamun da ke mana nuni da cewa jikinsa da sauki sosai.
Ganin hakan a raina na ce Insha Allah Malam Umar Hunkuyi ya kusa dawowa bakin aikinsa. Kwatsam mai zai faru sai ganin sanarwar Shugaban Sashin jaridar Leadership A Yau, Malam Musa Muhammad na yi yana sanar da rasuwar Malam Umar A Yunkuyi. Na kaduwa na jinjina matuka, na masa addu’ar Allah gafarta masa ya sanya shi cikin Aljannah Madaukakiya.

SendShareTweetShare
Previous Post

Ozil Zai Fara Buga Wasa A Arsenal A Watan Janairu

Next Post

Tsokaci Kan ‘WI-FI’ Da Yadda Ake Amfani Da Shi

RelatedPosts

Gina Hanyar Ruwa: Babu Kudin Kowa A Cikin Wannan Babban Aiki, Inji Mai Turaka

Gina Hanyar Ruwa: Babu Kudin Kowa A Cikin Wannan Babban Aiki, Inji Mai Turaka

by Bello Hamza
9 hours ago
0

Mai taimakawa gwamna Masari akan wayar da kan jama’a akan...

’Yan Sandan Kano Sun Cafke Mace Mai Garkuwa Da Mutane

’Yan Sandan Kano Sun Cafke Mace Mai Garkuwa Da Mutane

by Bello Hamza
1 day ago
0

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta shaida cewar wata mace...

Ta’aziyar Rasuwar Sam Nda Isaiah

Sam Nda-Isaiah Ya Rasu Lokacin Da Ake Tsananin Bukatar Gudunmawarsa – Jami’ar Jos

by Bello Hamza
4 days ago
0

Shugabannin jami’ar Jos sun bayyana rashin jin dadinsu dangane da...

Next Post
Tsokaci Kan ‘WI-FI’ Da Yadda Ake Amfani Da Shi

Tsokaci Kan ‘WI-FI’ Da Yadda Ake Amfani Da Shi

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version