Ta’azzar Fyade: Ina Mafita?

Fyade

Daga Samira Bello Shinko, sshinco@yahoo.com,

mmeerah@gmail.com,

A ‘yan watanin nan kallon akwatin Talabijin, sauraron Radio, buda shafukan Jaridu da zaurukan sada zumunta na zamani yana matukar sosa min rai da ƙkona min zuciya; saboda yanda nike cin karo da labaran fyade,musamman ga yaramata kanana. Wani rashin imanin idan ka gani sai kaji kamar ka shide dan takaici. Babban abin haushin kullum Allah wadai ake da abun amma sai karuwa yake kamar wutar daji. Kaina ya daure har yau na kasa gane meh ke kawo wanan bakar dabi’ar?

MENENE FYADE?

Fyade dai yana nufin amfani da karfi ko tirsasa kai dan yin jima’i da mutum (Mace ko Namiji) ba tare da so ko yardar wannan mutum ba. Kuma a fi danganta fyade ga mata da yara kanana saboda sune suka fi rauni a cikin al’umma. Abin mamaki shine duk da gidan karuwai daya yawaita (zuwa gidajen karuwan ma fa babban zunubi ne) wasu bata garin sun fi son su nemi biyan bukatarsu ta hanyar yiwa ‘yayan jama’a ta’adancin fyade. Duk da mutane da yawa suna dora laifin kwacokaf a kan cewa irin shigar da mata ke yi ta nuna tsiraici ke janyo musu,amma su kuma yara kananan fa? Ko su ma yara ‘yan shekara uku da wata uku nuna tsiraicin ya janyo musu?

A binciken da na yi da iya nazarina na fahimci cewa wadannan abubuwan da zan zayyano a kasa suna cikin dalilan da ya saka ake samun matsalolin Fyade a al’umma:

 1. Watsar da koyawar addinin mu da al’ada: da yawa mun watsar da koyarwar addinin mu da al’adun mu na kunya,saka t sutura ta addini da sauran su. Misali matan suna shigar nuna tsiraici,mazan kuma basu iya kawar da kansu yanda addini ya musu umurni. Kunya tayi karanci a cikin al’umma duk da sunan wayewa. Yara kanana kansu iyaye basu da lokacin kula da su kowa neman abin duniya ya saka a gaba.
 2. Sakacin iyaye: iyayen kansu suna da laifi sosai saboda sakaci da ko in kula da suke nunawa yaran su (musamman iyaye mata), a yawa basu damu da sanin inda yaran su ke zuwa ba, wata ita da kanta zaka ji tana cewa jeki waje kiyi wasa, wai ta dame ta.
 3. Tsafi da tsubbace-tsubacce: wannan wata masiba ce mai zaman kan ta ,saboda rashin Imani ke kai mutum wurin bokaye,duk don neman abin duniya. Can bokan marar imani zaka ji yana basu umurni da cewar sai sun aikata wani aikin rashin Imani za su samu biyan bukata. Ciki harda yiwa yara kanana fyade, ko kuma Mahaifi ya yi wa ‘yar sa, waiyazu billah!
 4. Shaye-shaye: wannan mummunar dabi’ar ta zama ruwan dare ga matasa,duk da cewa tana da mummunar illah a gare su. Samarin da ke shaye-shaye (mussaman masu zaman kashe wando) idan suka fita hayacin su yana iya saka su aikata ko wane irin ta’adanci,ciki harda fyade.
 5. Tunani irin na jahilai: akwai maza da yawa da ke da jahilci a kan addini,da yawa tunda sun ji malamai suna kafa hujja da cewa ba haramun bane auren yarinya karama, shikenan su a wurinsu da babbar mace da yarinya karama duk dayane. Idan suka tashi dabbancin su kowa ma suka samu za su iya yi mata.
 6. Zugar abokai: idan aka ci sa’a mutum bayada abokan kwarai na gar,i za su iya kwadaita masa abu shi kuma saboda halayar dan adam to son ganin kwafkwafi sai ya je ya aikata. Ta yiwu ma Matashine matsala ya samu da wata,sai su basa shawaran ya hukunta ta ta hanyar fyade tunda ba abinda ya kai wannan daraja a rayuwar mace.
 7. Son ganin kwakwaf ‘curiousity’ wannan kuma dabi’ar dan adam ce,duk da addini yace mata su suturce jikin su,wani Namijin a lokacin yake so yaga me kike boyo saboda lalacewar zamani,idan aka hadu da marar tawakali da Imani sai ya aikata fyade dan kashe kwarkwatar idon sa.
 8. Abinda Bature yake cewa ‘Phidopilia’wato mata matsala ce da ke da alaka da kwakwalwa, wanda yake dauke da ita zai ke jin cewa aikata abinda ya saba da hankali da mutuntaka shine abinda ransa yake so, kuma ba zai taba samun nutsuwa ba sai yayi hakan musamman akan sha’awa, koda yana da mace zai gwammace yayi fyade da wata akan biyan bukatar sa da matarsa ta aure.

ILLOLIN DA FYADE KE HAIFARWA

 1. Tozarci ga wacce aka yiwa.
 2. Jin ciwo a bayyane ko a badini.
 3. Rashin lafiya (sedual transmitted diseases).
 4. Cikin shege da zubar da shi.
 5. Rashin iya barci,tsoro,firgici,rashin iya cin abinci.
 6. Tsana da bakin ciki.
 7. Nakassa ko rasa rai gaba daya.
 8. Tsangwama daga mutane.
 9. Gudun aure ko rasa wanda zai aure su.
 10. Gulma,tsegumi da zunde.
 11. Tsananin damuwa (Depression)
 12. Matsalar kwakwalwa (Trauma)

HANYOYIN MAGANCEWA KO KAWAR DA FYADE

Wanan aikin bana mutum daya bane,kowa yana da gudumuwar da zai bada domin a samu a kawar da wannan ta’adacin na fyade: kama daga iyaye,mata,Hukuma (gwamnati), malamai da al’umma baki daya. Zan fara da iyaye da su mata kansu dan su abin yafi shafa fiye da kowa, ina ga idan aka bi wadanan shawarwarin da zan bayar a kasa za a samu a rage wanan matsalar:

 1. Ki guji saka kaya matsatsu ko masu shara-shara,yara kanana ma a dinga suturta su.
 2. Ki guji kebewa da Namiji ko muharramin ki ne (saboda zamanin ya canja).
 3. Ki guji zuwa unguwa ke kadai,ko yin dare a wajen ziyarar ‘yan uwa da dangi.
 4. Ki daina bi hanyar da samari ke yawan Zama; musamman idan wurin kafa na saurin daukewa.
 5. Ki guji rigima da maza Matasa za su iya daukar fansa ta wanan hanyar.
 6. Masu Yara kanana, ki guji bawa maza ‘yar ki da sunan raino.
 7. Ki kula da fitar ‘yar ki, idan da hali ko makaranta zata je a hadata da dan rakiya.
 8. Ku San irin makarantun da zaku saka ‘yayan ku da halin malaman.
 9. Ki koyar da ‘yar ki cewa gabanta nata ne ita kadai, kada ta Bari kowa ya gani ko ya taba mata.
 10. Ki koyar da ita rashin kwadayi ko karban abu a hanun mutane.
 11. Ki koyar da ita tsoron kebewa da Namiji ko sa’an ta ne.
 12. Ki kasance nai mata addu’a da Kuma nema mata tsari ba dare ba rana (wanan ne babban abinda zamu saka a gaba).
 13. Koyar da yara ilimi jinsi (Sed Education) da kuma dora ginshikin tunanin su akan kiman ta dan adam da darajanta shi (Humanity)
 14. Gina tarbiyyar yara maza da mata akan sanya tsoron Allah a gaba cikin dukkan sha’anin rayuwar su, da kuma sa musu kyamar zina da fyade tun daga kurciya kafin su girma.

Hukuma, malamai da al’umma suma kowa yana da gudummuwar da zai bada kamar haka:

 1. Malamai su tashi tsaye wurin fadakar da mutane da ilmantar da su.
 2. Hukuma ta zartar da hukunci mai tsauri ga duk wanda aka kama da wanan mummunar dabi’ar,kuma su tallafi rayuwar wace aka zalunta.
 3. Al’umma su dinga saka ido, duk wanda aka kama kada a rufa masa asiri,kuma su tabbatar an masa hukuncin da ya dace da shi.
 4. Iyaye da al’umma su daina rufe zance irin wannan idan ya faru, a fada domin daukar mataki. rashin fadar ke sakawa abun yana ta yaduwa.
 5. Dukk wanda aka kama idan ya ce wani boka ya saka shi, a kamo bokan shima a hukunta sa,idan da hali a raba sa da duniyar.

Ina saka rai idan aka bi wadanan hanyoyin zamu kawo karshen wanan ta’adancin na fyade, ubangiji Allah ya kara kare mu da zuria’ar mu daga wanan masifar, allahuma ameen.

 

Exit mobile version