Tabarbarewar Ilimi A Nijeriya, Ina Mafita? (1)

Kwamared Sunusi 0803 606 4695

Ba wannan ne karo na farko da nake rubutu akan makomar Ilimi a kasar nan ba, amma zai zama na farko a jaridarmu me farin jini ta LEADERSHIP A Yau.

Ilimin Boko wata fitila ce ga al’umma, kusan zan iya cewa ba abu ne sabo ba idan ana maganar daraja da Ilimi ya ke dashi a rayuwar Dan Adam.

Ilimin Boko wani mataki ne da yake nuna daraja da kimar al’umma a idon al’ummun waje. Ilimi ya zama wani mataki da duniya ke auna darajar kasa da kuma yarukan da ke cikinta.

Ko mu ki, ko mu so, a yanzu babu wata kasa, al’umma, ko wani yare da zai ci gaba ba tare da ya samu wayewar ilimin Boko ba, gaba daya rayuwarmu ta zama ilimi ne sitiyarin tukata, walau a gwamnatance, kasuwanci da kuma gina dimokradiyya. Ilimi kuma shi ne wani sikeli da ke auna ma’aunin fuskantar rayuwar al’umma, shi ya sa idan kana so ka wargaza al’umma to da ka wargaza harkar ilimunsu lalle ne ka ruguza su.

Duk da cewar a tarihi zuwan Ilimin Boko daga Turawan yamma ya gamu da cikas da kalubale a kasarmu, musamman Kuma arewacin Nijeriya, yankin da ya kumshi daukacin al’ummar yaren Hausa/Fulani da dangoginsa. To amma idan mu ka dubi kasar gabadaya muka auna za mu fuskanci cewar Harkar Ilimi na fuskantar barazana mafi muni, musamman ganin irin makudan kudaden da ake kashewa a harkar ta ilimi. Abin akwai daure kai, musamman idan muka saita kwakwalenmu don gano ainihin inda matsalar take, shin daga Gwamnati ne, ko kuma Mutanen da suke daukar ilimin? Ko Kuma masu tura su (Iyaye)?

Idan har za mu fadawa junanmu gaskiya, kuma mu dauki cewar wannan makala ce ta fahimta da kuma neman bakin zare, za mu ga cewar lalle a duniya an yi mana zarra wajen daraja da tsarin karatu, tarin kalubale musamman idan muka dauka daga 1999 (dawowar mulkin dimokradiyya) har kawo yanzu, shi ne lokaci mafi muni da zamu iya cewa an samu koma baya da kuma rauni wajen saisaita ilimi yadda al’ummar kasar za su daki kirji su ce gwamnati na basu nagartaccen Ilimi, ko kusa ko alama babu wanda idan ya dubi tsarin ilimin kasar ba zai tausaya masa ba, domin kuwa mafi yawan al’ummar kasar  talakawa ne, da ke rububin karatu a makarantun gwamnati, tun daga matakin firamare har zuwa jami’a, makarantun gwamnatin sun zama ita kadai ce mafitarsu, duk da Shugabannin da mu ka yi, da Ministocin Ilimin, za mu iya cewa ba su aikata wani abin a zo a gani ba wanda har za mu ce musu sam barka, sai dai kawai a yi kawaici a ce ba laifi. To amma babu uzuri ganin yadda Ma’aikatar Ilimi ta zama fitilar da kowanne dan kasa ya ke kallonta, amma kuma nanne mafi samun rashin tagomashi idan muka kwatanta kanmu da kasashen ketare wanda suka samu nagartaccen ilimi saboda jajircewar shugabanninsu. A matsayin kasa irin Nijeriya ya ci a ce ta yi kafada da kafada da sauran kasashen duniya, amma abin takaici kasashen da muke gani su ne aka sanmu, amma nan ne inda yanzu yaranmu ke zuwa don samun ilimi mai nagarta da kololuwar daraja, kasashe irinsu Malaysia, Ghana, Masar, Sudan da sauransu. Babu wata tantaman rashin ingancin namu ya sanya suke guduwa can. Namu sun gamu da cikas, lalura da kuma tabo saboda nakasunsu da lalacewar tsarinsu.

Mu duba mu ga yadda tun daga matakin sakandare har zuwa jami’a ba a daina satar amsa ba yayin jarrabawa, tun daga kan NECO, JAMB da POST UTME za ka ga yadda ake cinikin bayar da amsa, da magudin jarrabawa. Siyar da satifiket din karya, buga sakamakon jarrabawa na karya. Har kawo yau kuma ba a daina yaye dalibai masu rauni akan abin da aka karantar da su ba, tun daga yaren Ingilishi da ya zama shi ne yaren Boko, har kawo zuwa ainihin sashen da aka karanta. Abu ne mai sauki kaga wanda ya gama digiri na biyu (Masters) ba ya iya yin yaren turanci, haka kuma za ka ga lauyan da ya shafe akalla shekaru 8 ya na karatun shari’ah, amma ya shiga kotu yana kinkinar turanci, Injiniya ya kasa gyara karamin injin bada wuta, malami ya kasa fuskantar da daliban darasun da yake karantar dasu, wannan fa duka shaidu ne kwarara da suke nuna rashin tsari da kuma rashin darajar ilimi a kasar nan.

Abin tambayar a nan shi ne, shin daga ina ne aka haihu a ragaya? Kuma ina mafita. Amsar a bayyane take kuma kowa ya santa. Gwamnati da ya zamar mata hakkin samar da ingantaccen ilimi, ta nuna gazawa, wannan ya sanya tsarin ya tabarbare kuma ya lalace, shi ya sanya tun daga matakin firamare ake rasa gini tun ran zane, tubalin gina katangar karatu mai kwari na firamare, nan ne kuma ake fara samun magudi da lalacewar tsarin, har zuwa sakandare inda matakin ya ci gaba da lalacewa, wannan ya sanya wasu makarantun gwamnatin a wasu garuruwan tamkar kwango saboda yadda gwamnati ba ta nuna kulawarta garesu. Shi ya sanya babu yadda za a yi ’ya’yan masu hannu da shuni ka gansu a makarantun gwamnati, domin kuwa sun san karatu ne mara inganci, yayin da kuma yaran talakawa ke rububin shiga duk da cewar sun san lalle akwai bukatuwar gyaran, da su yi ta bulunbituwa a gari, gwara su je can su sauke faralin yin karatun da dadi ba dadi.

Shin yanzu haka zamu zura idanu kullum madadin gyara ya zo, sai dai abin ya yi ta tabarbarewa, shin haka mu ’ya’yan talakawa za mu zura wa gwamnatoci ido, su na ta shudewa ba tare da nuna wata damuwa don gyara harkar ilimi ba?

 

Exit mobile version