Connect with us

LABARAI

Tabarbarewar Tsaro: Gwamnonin Arewa Za Su Fara Amfani Da Mafarauta Da ‘Yan Tauri

Published

on

Biyo bayan ci gaba da tabarbarewar tsaro a arewacin Nijeriya, gwamnonin yankin 19, a karkashin lemar kungiyar gwamnonin arewa 19 (NSGF), sun kudurci aniyar daukar ingantattun hanyoyin shawo kan matsalar tsaro wajen amfani da yan banga da yan tauri a yankin.
Gwamnonin sun sun yanke daukar matakin da daren ranar Alhamis, yayin da gwamnonin su ka cimma matsayar kafa kakkarfan kwamitin tsaro wanda zai samar da yankin alaka tsaknain jami’an tsaro da yan sa kan (mafarauta da yan banga) domin fuskantar kalubalen tsaron da ya addabi yankin.
Bugu da kari kuma, taron gwamnonin wanda ya gudana a karkashin jagorancin shugaban kungiyar, Gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong, kwamitin tuntuba wanda ya kunshi sarakunan gargajiya, addinai, da shugabanin al’umma a karkashin jagorancin Gwamna Lalong, wajen tattaro ma su ruwa da tsaki domin fuskantar matsalar tsaron a yankin.
Sauran yan kwamitin sun hada da Gwamna Amadu Fintri na jihar Adamawa, Gwamna Abubakar Bello na jihar Nija da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato.
Haka zalika kuma, kungiyar gwamnonin ta bayyana cewa, gayyato yan banga, mafarauta da sauran kungiyoyin al’umma wajen aikin samar da tsaro tare da jami’an tsaron Nijeriya domin, “domin samun ingantattun bayanan tsaro a cikin hanzari, wanda hakan zai taimaka wajen daukar matakin gaggawa da sakamako mai karko.”
Har wala yau kuma, sun yi kira na musamman ga gwamnatin tarayya ta aiwatar da tsari da kudurorin gamayyar kungiyar kula da ci gaban tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) dangane da takaita zirga-zirgar jama’a, wanda ya ke da nasaba da kai-komo kan iyakokin tsakanin kasa da kasa zuwa Nijeriya, musamman a yankin arewacin Nijeriya.
Haka zalika kuma, kungiyar gwamnonin ta yaba da kokarin gwamnatin tarayya wajen tunkarar matsalar tabarbarewar tsaro a yankin, wanda kuma kungiyar ta bukaci karin daukar ingantattun matakan shawo kan matsalar tsaron, kana ta taimaka wajen kawo karshen ayyukan yan ta’addan yan bindiga dadi, barayin shanu da masu garkuwa da jama’a hadi da ma su aikata miyagun laifuka a yankin.
A hannu guda kuma, kungiyar dattijan arewa ta nemi gamayyar kungiyoyin matasaan arewa (Coalition Of Northern Groups) ta jingine zanga-zangar nuna bacin rai da ta fara, ta dalilin tabarbarewar tsaron, inda ta bukaci su canja wata hanyar yi wa gwamnatin tarayya matsin lamba hadi da na gwamnonin jihohi wajen lalabo ingantacciyar hanyoyin shawo kan matsalar tsaron.
Gamayyar kungiyoyin ta bayyana hakan tare da wasu shawarwarin da ta cimma matsayar tare da dakon daukar ingantattun matakan shawo kan matsalar, tare da bai wa gwamnatin shugaba kasa Muhammadu Buhari da sauran gwamnatoci shawarwarin bin hanyoyin da su ka dace don kawo karshen matsalar tsaron, da karin hasken cewa sun gudanar da zanga-zangar ne ba don komai ba face kira ga gwamnatoci dangane da halin da ake ciki yanzu na tabarbarewar tsaro a arewa.
Har wala yau kuma, biyo bayan wadannan jerin-gwano kashi biyu da aka gudanar a jihohin Nija da jihar Katsina, ya jawo jami’an tsaro sun kama shugaban kwamitin amintattu a gamayyar kungiyoyin (CNG), Nastura Ashir Shariff, zuwa Abuja wanda sai daga baya aka sako shi- ranar Alhamis.
A nata bangaren, a wata sanarwar manema labarai da kungiyar dattijan arewa ta fitar, ta hannun Daraktan yada labaran kungiyar Dr. Hakeem Baba- Ahmed, ya ce kungiyar dattijan arewa ta bayyana cewa dukan kungiyoyin da ke arewacin Nijeriya za su dauki matakan sanya ido wajen matsin lamba ga duk wani da ke rike da madafun iko domin yanto yankin.
“Saboda haka mu na kira ga shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari a karkashin jagorancin jam’iyyar APC su aiwatar da alkawuran da su ka dauka kafin a zabe su.”
“Wanda a cikin rashin sa’a, mun samu wasu bayanan da ke nunin akwai wasu bata-gari da ke shirin kawo wa zanga-zangar lumanan da ake gudanarwa a wasu shiyoyin arewacin Nijeriya.”
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci jama’ar jihar Katsina su ci gaba da hakuri, ya ce saboda yadda gwamnatin shi ke kokarin shawo kan matsalar yan ta’adda a yankin.
Sakamakon hakan ya jawo shugaban kasa Buhari gudanar ganawar musamman da hafsoshin tsaron Nijeriya, tare da bayyana musu tashin gamsuwar shu dangane da yanayin aikin samar da tsaron inda ya umurce su da daukar sabbin matakan bai jama’a kariya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: