Idris Sulaiman Bala">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTALIN ARZIKI

Tabarbarwar Lamurra: Shugaba Buhari, Rike Sitiyari Da Kyau

by Idris Sulaiman Bala
November 24, 2020
in TATTALIN ARZIKI
4 min read
Tabarbarwar Lamurra
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tun daga lokacin da cutar Korona ta tasa duniya gaba musamman lokacin da ta yi kamari a watan Maris din 2020, al’amura suka rikice, manyan kasashe masu tinkaho da cigaba suka koma kowa ya yi takansa, kanana masu tasowa suka gurfana da gwiwowinsu, wadanda ba a saka su cikin lissafin masu hawa turbar samun bunkasa suka shaki kamshin mutuwa. Korona dai ta zama kanwa uwar-gamin sumar da duniya. Don haka babu mamaki idan kasashen duniya sun shiga wani hali tare da fafutikar neman murmurewa.

Sai dai a yayin da kusan galibin kasashen na duniya suke kokarin kawar da matsala guda wadda ba ta wuce ta tayar da komadar tattalin arzikinsu ba, mu a nan Nijeriya abubuwan da ake neman magancewa sun yi yawa, wai “shege da hauka”.

samndaads

Murna da farin ciki sun cika zukatan ‘Yan Nijeriya lokacin da gwamnati ta fara sassauta dokar kullen da aka kakaba saboda Korona. Ba a kai ga farfadowa ba, kwatsam sai ga zanga-zangar neman kawo karshen rundunar tsaro mai yaki da fashi da makami da garkuwa da jama’a da aka fi sani da SARS. Daga bisani lamarin ya kazance ya zama babban tashin hankali da kashe-kashen rayuka da kone-konen dukiyoyi da fashe-fashen rumbunan ajiyar abinci da sauran kayan masarufi na gwamnati da sunan ganima.

Tabbas wannan bala’i ya kara ta’azzara matsalar rashin tsaro da Nijeriya take bundun-bundun a ciki sama da shekara 10 da suka gabata, da suka kunshi sace-sacen jama’a ana neman kudin fansa, kisan kare dangi ga al’ummomin yankunan karkara da kuma yaki da boko haram da ya-ki-ci-ya-ki-cinyewa.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani Hakimi da dansa, a kauyen Gidan Zaki, da ke yankin Karamar Hukumar Zangon Kataf da ke jihar ta Kaduna.

Masu garkuwa da mutane sun kashe mutum biyu, suka sace mutane da dama a yankin Karamar Hukumar Giwa ta jihar.

‘Yan bindiga sun yi kisa a Marabar Kajuru ta Jihar Kadunan, suka sace wasu. Masu garkuwa sun harbi mutun daya aka kai shi asibiti jinya, sannan suka sace wani malami, da kuma wasu yara biyu a Kwalejin Foliteknik ta Nuhu Bamalli da ke Zariya, a Jihar Kaduna.

Masu garkuwa da mutane sun tare hanyar Kaduna zuwa Abuja, kusa da Katari ta jihar Kaduna, suka kashe mutum biyu suka yi daji da wasu, sai dai jami’an tsaro sun ce sun ceto su, sannan daliban Jami’ar ABU da aka sace a hanyar su tara, sun shafe kwanaki a hannun ‘yan bingidan kafin a ceto su a karshen makon da ya gabata.

Makasa sun je Kauyen Albasu da ke Sabon Birni a yankin Karamar Hukumar Igabi ta jihar Kaduna, suka kashe mutum goma sha biyu.

Bugu da kari, makasa sun je yankin Ikara ta Jihar Kaduna, suka kashe wani Mai Gari suka yi tafiyarsu.

Masu garkuwa sun je Rigachikun ta jihar Kaduna, suka kashe wata mai juna biyu, suka sace mijinta tare da neman kudin fansa.

Al’umomi da ke kusa da tashar jiragen sama ta Kaduna, da na kusa da Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin Soja (NDA) sun ce a nan wuraren ‘yan bindiga suka fi sakata su wala.

Masu motocin sufuri zuwa Birnin Gwari sun ce hanyar ta zama tarkon masu garkuwa da mutane, kodayake an ce al’amura sun fara sauki a nan.

Mutanen yankin Sabon Garin Zariya da ke Jihar Kaduna, sun ce kauyakunsu sun zama tungar barayin shanu.

Mutanen Mando da yankin Asibitin Ido na Kasa da ke cikin garin Kaduna, su ma sun ce da ido daya suke bacci.

Daga Kudan ma ta jihar Kaduna, labari ne na an yi kidinafin wasu mutanen garin. Haka dai labarai a kan tabarbarewar tsaro suka cigaba da kai-komo a makon da ya gabata.

A yayin da gwamnati take laluben yadda za ta shawo kan matsalar tabarbarewar tsaron wadda take kara ta’azzara, sai kuma ga Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar da rahoton cewa Nijeriya ta shiga matsin tattalin arziki wanda ya nuna rabon kasar ta shiga irin wannan mummunan halin tun shekara 33 da suka gabata.

Rahoton hukumar ya ce hada-hadar tattalin arzikin kasa ya samu koma baya da kashi 3.62 a sulusi na uku na shekarar 2020.

Kamar yadda rahoton na NBS mai shafuka 96 ya nunar, “halin ni ‘yasun da tattalin arzikin kasar ya shiga a sulusi na uku na 2020, ya nuna irin tasirin da dokar kulle ta takaita kai-komon jama’a da hada-hadar tattalin arziki a dukkan sassan kasar nan ta yi, wacce aka kakaba a farkon sulusi na biyu na shekarar domin shawo kan annobar Korona”.

Kodayake, bayani mai bayar da kwarin gwiwa a cikin rahoton shi ne, akwai wasu sassa na tattalin arziki guda 18 da suka samu bunkasa a sulusi na uku wanda ke nuna an dara wanda aka samu a sassa 13 kawai a sulusi na biyu na shekarar ta 2020, akwai bukatar Shugaba Buhari ya saurari shawarwarin da masana tattalin arziki suke bayarwa kan yadda za a fitar da jaki daga duma.

A sake duba manufofin bunkasa tattalin arzikin kasa da gwamnatinsa ta sanya a gaba kafin zuwan Korona, a dora su a sikeli, a zubar da wadanda ba su dace da lokacin da ake ciki ba, a shigo da wadanda za su taimaka a tayar da komada, saboda idan kida ya canza; dole ne rawa ta canza.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, mai matukar farin jini da karbuwa ga ‘Yan Nijeriya, muna maka fatan samun nasarar a wannan jan aiki da ke gabanka, sannan a kara rike sitiyarin shugabanci da kyau!

SendShareTweetShare
Previous Post

Nijeriya Na Bukatar Dala Tiriliyan Uku Kafin Cike Gibin Ababan More Rayuwa

Next Post

Mun Yi Maulidi Ne Don Jaddda Kauna Ga Manzon Allah – Ali Datti

RelatedPosts

Layin Dogo

Gwamnati Za Ta Kashe Biliyan N71 Wajen Kwangilar Titinan Dogo Shida

by Idris Sulaiman Bala
22 hours ago
0

Gwamnatin tarayya za ta kashe kudade wajen gudanar da hanyoyin...

TAJBank

TAJBank Na Kokarin Inganta Harkokin Ilimi A Nijeriya

by Idris Sulaiman Bala
22 hours ago
0

Bankin TAJBank wanda yake gudanar da kasuwancinsa ta tare da...

Lantarki

Bangaren Lantarki Ya Tafka Asarar Naira Biliyan 20.5 Saboda Karancin Gas

by Idris Sulaiman Bala
2 days ago
0

Bangaren wutar lantarki a Nijeriya ya tafka asarar harajin naira...

Next Post
Ali Datti

Mun Yi Maulidi Ne Don Jaddda Kauna Ga Manzon Allah – Ali Datti

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version