Connect with us

Uncategorized

Tabarya, Kowa Ya Hadiye Ki  Zai Kwana Tsaye

Published

on

Ai wannan al’amarin haka yake saboda kuwa ba yadda za a yi a samu zama domin dama ai ita tabarya wata  aba ce, ga ta dai nan sundundun, tsayen nan shi ne babban rufin asirin wanda ya hadiye ta, shi ya sa ma wadanda suka iya sarrafa harshen Hausa sosai suke cewar shi mai tarko ba ya taka kara, idan ko ya kasance mai irin dabi’ar  yin hakan ne, zai kuwa dade yana bata wa kansa lokaci saboda kuwa ai ba komai zai kama wa ba, koyaushe hakan zai ta yi ta walagigi bai san cikin halin da yake ba, duk wani motsin da zai yi ai yana ganinsa karshe abin da yake son ya kama. Amma ya za a ce mutum ya aika wa mutane da goro cewar yana gayyatarsu, su zo su sha biki, sai daga baya kuma bayan duk wanda aka gayyata sun hallara sai kuma ya fara cewa, ai shi ko dai bai da wuraren da zai saukar da su, ko kuma maganar cimakar da zai ba su, har iya lokacin da za su yi, hakanan ma maganar take idan mutum ya aika wa matsala goron gayyata, bayan ta zo ya fada mata cewar ba ya da mazauninta, amsar da za ta ba shi, ba ta wuce kar ya samu wata damuwa saboda ai ita ma ta taho  tare da abin zaman ta. Sau da yawa mutane suna yin wasu abubuwa wadanda za a yi tunani ko sun samu tabuwar hankali ne, ko kuma  dai akwai wani abu ne na daban wanda ya faru gare su, har suka kasance suna halayya irin ta kananan yara. Dole ne mana a ce halayya irin ta su domin kuwa ba wata makawa, ko an hada su da kananan yaran ai ba wani laifi aka yi ba, shi dama dan kuka ai shi ke ja wa uwarsa jifa, wani lokacin ma har rauni akan ji mata.

An ce so hana ganin laifi wannan al’amari haka yake, domin duk yadda aka yi na, a lalata shi wannan abin da ake so, shi wanda yake son shi watakila ma soyayyar abin zama ta kara shiga zuciyarsa, komai runtsi shi bai ganin duk wani abin kyama, musamman ga abin da yake so. A kada a kuma raya shi hasken al’amarin ma yake kara gani koda wanne lokaci. Wasu al’amarin na su nema ma yake yi ya wuce makadi da rawa, to wuce makadi da rawa mana, saboda wani abin ma ko an tambaye su ba’asin da suke ganin ko ba a yi adalcin ba, ba kuma za su iya yi wa kansu adalcin ba, saboda kuwa gaskiyar ce ba za su iya fada ba, don kawai suna ganin idon wani wanda suke ganin saboda wani ihisanin da yake musu, sai su ga ai bai dace su fadi gaskiyar ba, don ganin alfarmar da shi yake masu. Suna ganin shi ke ba su ba mahaliccinsu ba, tunda su dama kamar ci-ma-zaune ne, sana’oin ma da suke yi, yanzu sun bari suka kuma mayar da kansu ragwaye.

Duk wanda yake bin al’amuran da suka shafi kawo wa tattalin arzikin kasa tu’annati yadda ake aiwatar da su, na binciken wadanda suka yi sama da fadi da dukiyar kasa, ko kuma nace karbar rashawa da cin hanci, kowa ya san yadda ita Hukumar EPCC take fuskantar matsaloli wajen kokarin da take yi na hukunta wadanda suka ci amanar kasa. Wato yadda sai da aka fara bin diddiki sannu a hankali kafin ta kai ga gurfanar da wadanda ake zargi da aikata laifin cin amanar kasar, sai ka saurari irin su suna maganar ai wannan Alkalin ko ma abinda  yake yi  shi ma ya san ya bata masun bai dace ba, kawai ita Hukumar tana yin abin da bai dace ba, ba don komai ba sai saboda ta kama nasu, wanda suke yi ma ganin mutumin kirki, bayan kuwa shi yana halin bera, wanda yake daukar abin da ba nasa ba, ya kai ya boye a hankali har sai an lura sosai tukuna, za a gane ashe ba karamar barna irin su ke yi ba. Zai yi dai wuya a ce shi wanda ake zargi da aikata wani laifin cin amanar kasa wanda sau da yawa, yana tsare ne ko dai gidan Yari ko kuma yana hannun ita Hukumar EFCC, amma sai ka ga mutane sun yi tururuwa sun je kotu domin nuna goyon bayansu gare shi, wani ma har idan aka yanke hukuncin, zai je gidan Yari, shi wanda yake yi ma goyon bayan, yayi fursuna, har wasu ake samu suna yin zanga zanga, ta nuna basu ji dadin da har aka  gai ga kawowa,  ga irin haka ba saboda har za a kai ga yanke hukunci. Abin yanzu yama zama ‘’Ga wani abin dariya wai yaro bayan ya tsinci hakori, saboda dai ai shi , a iya nasa sanin ya san da shi ne ake  yin dariyar.

Saboda wasu sun dauka shi al’amarin da zai sa a je a yi zanga-zanga, saboda da wani tamkar kasuwanci ne, idan dai wani ya je ya tafka ta’asarsa, sai ya sa a samar masa hayar wadanda za su je su yi zanga-zangar, a ba su wani abin da bai taka kara ya karya ba. Ga shi kuma wanda ake zargi da aikata cin amanar kasa shi ya san abin da ya aikata saboda ya san ana da gamsassun shaidu , su kuma ga su suna ta bata wa kansu lokaci. Idan ma kuna maganar soyayya ne wadda dole sai kun nuna kuna tare da shi, kune magoya bayansa, wani babban ma abin da ya fi dacewa wanda za ku yi  shi ne, ku rika yi masa ko masu addu’a watakila Allah ya sa ko ya samu, ko kuma su samu kubuta daga zargin da ake yi masu, amma ba wai kawai ku zo kotu kuna nuna ai ku ba ku ji dadin da hakan ta faru ba a gare shi, ku ba jami’an tsaro ba, ko kuma ma’aikatan kotu ba, amma kuna neman ku sa kanku, ko kai shi wurin da Allah bai kai ku ba. Babban ma abin da ya dace ku rika yi masu idan har kun kusance ku masoyan sune na hakikan da cewa ya yi ku rika ba su, shawarwari a kan kada su kuskura su yi kusa da kayan talakawa, saboda wancan wurin ba muhallinsu ba ne, idan da kuna yin haka wasu abubuwan da suke faruwa a yanzun, har ma ake ganin ana takura masu,  ba a kuma kyauta masu, ko da akwai al’amarin takurawa da wani cin mutunci, ai da tuni an wuce wurin. Amma ba ku yi hakanan ba, tunda kuna ganin ai kuna dan samun na rufe wata kafar data takuara ku, ai maganar hakan ma  dabata koma taso ba.

Su ma wadanda suke taba kayan da ba nasun ba, ai sun san cewar ba su kyauta ba ne ko kadan abin ba wani dadin ji bare ma gani, sabodai duk wata kulawa ana ba su, minene kuma na sai har sai sun kai ga sa idoakan abubuwan da ba nasu ba, bayan sun kwana da sanin laifi ne tare da kuma cin amanar kasa, idan suka yi haka din. Suma kansu suna iya tunawa da cewar ai lokacin da aka rantsar da su, sun rantse ne da Littattafai  biyumasu tsarki, wato Kur’ani da kuma Bible, wannan ya nuna ke nan suna sane da abubuwan da suka aikata,kuma shugabanni ai ba kyau su canza ra’ayinsu, na rikidewa su koma wata sabuwar halitta, bayan sun hau kan karagar mulki.

Idan dai har mutum bai son Jaki ya kada shi, to tun farko ma kada ko kwatanta hawan shima ya yi, saboda daga karshe kunya zai sha, domin kuwa Jakin yana bari sai ya je cikin kaya, ko kuma duwatsu, lokacin zai ce to shi fa zai yi tutsu, kai kuwa wanda ya riga yah au Jakin, aisai kuma maganar rungumar kaddara wadda kowa ya kwan da sanin ta riga fata. Kamar dai irin halin da wasu ke ciki yanzu tuni sun hau Jakunan karin rashin sa’a gare su kuma sai suka kasance Aholakai ne.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: