Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home FITATTUN MATA

TABAWA ’Yar Tauri: Gwarzuwarmu Ta Mako

by Tayo Adelaja
October 29, 2017
in FITATTUN MATA
4 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tabawa tana cikin ‘yan tauri na farko-farko don a lokacin da ta shiga harkar babu mata da ke sana’ar tauri. Sunanta na gaskiya Hafsatu Muhammad Sani

Tarihinta

An haife ni  kimanin  shekara saba’in da biyar da suka wuce a garin Rano. A lokacin ana ɓoye yara ba a sa su a karatun boko don haka ba mu yi karatun boko ba sai dai na allo, kuma ko shi ɗin ma an fi ba wa karatun maza muhimmanci sosai don haka mu dai mukan bi yayyenmu ne maza zuwa makarantar allo. Gidanmu babban gida ne, mahaifinmu ‘ya’yansa ishirin da ɗaya ina da yayye uku amma duk cikinmu na fi kusa da mahaifina. Dalilin da ya sa mahaifina ya ja ni a jiki a lokacin shi ne,  nice ‘yar fari gun mahaifiyata a lokacin kuwa ‘yan fari ba  a kulawa da su,  mahaifiyata sam ba ta ta tawa wannan ya sa mahaifina ya ja ni jiki ko ina ya cire ƙafa ni nake mayar da tawa. Ko da ma na tasa duk inda za shi muna tare.

Fara wasan taurinta.

Ya batun aure da iyali ga tauri kuma an ci tauri?

Duka haka aka yi ai bikin magaji ba ya hana na magajiya. Aure duk wanda ya fito sai da ya tabbatar ya ji ya gani magabata sun  faɗa masa ka ɗauka duk lokacin da wasa ya kama za ta don dai kai ba zaka iya kange ta ba, in har ta ji an busa ƙaho an yi kirari dole sai ta fita. Idan da gaske yana sona zai amsa da ya amince sai a yi auren. A haka duk na yi aure-aurena. Yarana uku biyu maza ɗaya mace  amma mazan sun rasu tun suna ƙanana sai macen yanzu jikokina tara na wajen macen yanzu haka nan da kika same ni ina zaune gidan babban jikana ne.

‘Ya’yanki sun gaji tauri ko?

Ai da yake yarana kin ga na wani gida ne kuma in ba sa sha’awar tauri ba za su yarda su ci ba. Musamman yaran yanzu da boko ya ratsa su. Amma kin ga shi jikana da yake shi namiji ne ɗansa ina nan ina dafa shi.

Bayan sana’ar tauri ki na wata sana’a?

Bayan sana’ar tauri kuma ina sana’ata ta ɗanwake wadda ita ma na yi suna a cikinta, duk lokacin da ba wasa ina yin aba ta . Yanzu kuma da tsufa ya kamani ina zauna a gida amma duk da ina  sana’ar sayar da itace.

Ya shiga jeji da farauta a na yi har yanzu?

Mene sirrin nasararki?

Duk abin da na samu a rayuwa biyayya ta ba ni shi. Na sami nasarori da yawan gaske a rayuwa sunana ya je inda ban taɓa tunanin zan taka ba. Sannan lokacin da Buhari yana mulki lokacin soja shi ya naɗa ni sarkin dawan Kura da Rano sannan ya yi min kyauta shi da wasu sojoji shi ma kuwa na samu wannan kyauta ne ta sanadiyyar jarumtar da na nuna.

Wanne ƙalubale ki ka samu?

Tauri sana’a ce ta sai da rai don haka ban taɓa sa ran in na fita zan dawo da raina ba don haka ma kullum zan fita sai na yi sallama da mutanen gida ko dai na dawo ko a dawo da ni sana’a ce ta cika baki da ashariya sai fankama ko wa ye kai ko waye ubanka wannan kaɗai ya ishe ka ƙalubale. Sannan yadda a yau sana’ar tauri ke neman rushewa nan ma babban ƙalubale ne. Yaran yanzu saboda boko duk sai suke ganinmu kamar ma ba a kan dai-dai muke ba. Hatta gwamnati a yau ta sa takunkumi na shiga jeji sai an karɓo izini. Kuma a hakan ma in an yi rashin sa’a sai a farmana a jejin ko watannin baya haka aka kasha mutanen mu a jeji. Yawan da jama’a suka yi a yanzu asiran ma na taurine sun yi wuyar saboda a ƙa’ida in za a fita ɗebo asiran ba a son a ga kowa tun daga kan hanya har zuwa jejin to a yau ko me tsakar dare ka fito sai ka ga mutane. Na sha fitowa cikin dare ina gaf da shiga jeji zaka ci karo da wani ya gaisheka dole ka koma.

Rashin jajircewa ta yaran yanzu ita ma babban ƙalubale ne ni na fita farauta da tsohon ciki kawai don kare sunan mahaifina inda a jejin da suka lura da yadda na galabaita a kafaɗa aka dora ni amma hakan bai sa na ce a juya ba.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

ƘUNDIN MASARAUTA

Next Post

Surukan Zamani

RelatedPosts

Ellen Johnson Sirleaf: Mace Ta Farko Da Ta Fara Zama Shugaban Kasa A Afrika

Ellen Johnson Sirleaf: Mace Ta Farko Da Ta Fara Zama Shugaban Kasa A Afrika

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Daga Khalid Idris Doya Ko-kun-san…. Ellen Johnson Sirleaf ce mace...

Hajiya Dijatu Yerima Balla: Fitacciya A Fannin Ilimi Da Shakatawar Yara

Hajiya Dijatu Yerima Balla: Fitacciya A Fannin Ilimi Da Shakatawar Yara

by Sulaiman Ibrahim
3 weeks ago
0

Ko-Kun-San… Dijatu Yerima Balla tsohuwar malamar makaranta ce, kuma mamallakiyar...

Amina

Amina Nikatau: Sarauniyar Da Ta Mulki Masarautar Zazzau Bisa Jarumta

by Muhammad
4 weeks ago
0

Ko-kun-san…. Sarauniya Amina Nikatau ce ta ki aure domin kar...

Next Post

Surukan Zamani

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version