Tabbas APC Za Ta Yi Takara A Zamfara –Dakta Dauda

A yayin da lamurran siyasa suka dau dumi a Nijeriya, musamman ma a jihohi inda jam’iyyu tuni sun fidda sunayen ‘yan takarar matakai, wadanda suka hada da gwamnoni, ‘yan majalisar dattawa, tarayya da ‘yan majalisar jihohi.
Sai dai lamarin ba haka yake ba, ga jam’iyyar APC ta Jihar Zamfara, inda har zuwa yanzu ana ta tataburza tsakanin jam’iyyar APC da hukumar INEC kan sunayen ‘yan takarar jam’iyyar, wadanda za su fafata a zaben shekarar 2019 da ke gabatowa.
A bangaren hukumar zabe ta INEC, babu an takara ko guda da zai shiga zaben 2019 a fadin Jihar Zamfara. Inda hukumar ta kafa hujja da cewa ta dau wannan matakin ne bisa hujjar cewa ba a gudanar da zaben fidda gwanin jam’iyyar ba.
Ita kuwa uwar jam’iyyar APC ta kasa, ta kalubalanci wannan mataki na Hukumar INEC, inda ta bayyana cewa akwai ‘yan takararta wadanda jam’iyyar ta fidda su ta hanyar bin matakin sulhu a tsakani.
Daya daga cikin ‘yan takarar na jam’iyyar APC, Dakta Dauda Lawal Dare (Gamjin Gusau), ya bayyana cewa hukumar INEC ba ta da wannan hurumin na hana jam’iyya shiga zabe, matukar ba wata dokar hukumar ta sabawa ba.
Gamjin Gusau ya bayyana wannan matsayar tasa ne a wata hira da LEADERSHIP A Yau, inda ya nanata cewa, suna nan akan bakarsu ta yin takara a Zamfara.
Dakta Dauda yayi kira ga magoya bayansu na jam’iyyar APC a fadin Jihar Zamfara da su yi watsi da duk wata jita-jita, domin uwar jam’iyyar tana nan tsaye kan lamarin, kuma nan ba da jimawa ba za a ji labara mai dadi.
Sannan kuma ya kara da yi wa al’ummar Jihar Zamfara jaje bisa irin halin rashin tsaro, fargaba da rashin kwanciyar hankali da suka tsinci kawunansu a ciki.

Exit mobile version