Connect with us

LABARAI

Tabbas Buhari Zai Kara Farashin Lantarki -Ministan wuta

Published

on

A makon nan ne gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa maganar karin kudin wutar lantarki ya na nan, duk da surutan da kungiyoyi su ka rika yi a game da shirin da ake yi.

A jiya ranar Talata, 16 ga watan Yuni, 2020, Ministan harkokin wutar lantarkin Najeriya, Sale Mamman, ya ce sabon tsarin farashin wutan zai fara aiki awatan Yuli.

Injiniya Sale Mamman ya yi wannan bayani a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa kan lamarin wutar lantarki a birnin tarayya.

Sale Mamman ya ce gwamnati za ta cigaba da shirin da ta dauko na kara farashin wutan ne domin annobar Korona ta yi tasiri a kan ‘yan kasuwar lantarkin.
Ministan ya shaidawa Sanatocin kasar cewa hukumar NERC ta yi niyyar fara amfani da sabon farashin wutan ne a watan Afrilun 2020, amma sai aka saurara.
“Hakika, annobar cutar Korona ta riga ta yi tasiri wajen rage karfin aiki saboda matakan da aka bi a Duniya wajen takaita yaduwar cutar.” Inji Mamman.
“Saboda haka wannan ya taba karfin wutan da ake samu da kuma bukatar lantarki a ko ina.”
“Halin da harkar wuta ta ke a Najeriya shi ne ana kashe makudan kudi wadanda aka dogara da kungiyoyin kasashe masu bada tallafi, da bashi da kuma kudi daga kasafin kasa.”

Yayin da wasu suke nuna rashin jin dadinsu a game da wannan, Ministan ya ce su na neman hanyar da za abi wajen samun kudi daga waje domin ganin an inganta harkar wutan kasar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: