Connect with us

NISHADI

Tabbas Sai Mawakan Arewa Sun Danne Kudu Nan Gaba Kadan – Lil Beekay

Published

on

Shaharerran mawakin Hiphop Aliyu Bukar wanda aka fi sani da Lil beekay wanda ya rera wakar JOGODO, ya kuma yi BACK TO BACK da wakar SCIENCE STUDENT wanda sukayi tare da matashin mawakin hip hop Abk Don. Sun tataunawa da ya yi wakilinmu Umar Muhsin Ciroma, ga yadda hirar ta kasance:

Da farko masu karatun mu zasu so suji cikakken sunanka da takaitaccen tarihinka.

Sunana Aliyu Bukar, haifaffen garin Kaduna  na girma a Kaduna Mahaifina haifaffen garin Maiduguri ne, a Kaduna nayi makaranta tin daga firamari har sakandiri yanzu ina zuwa Polytecnic Kaduna.

Wani matakin karatu kake yanzu?

Ina aji 2.

Me yaja ra’ayinka ka fara waka?

Tin ina yaro karami na tashi da ra’ayin waka, lokuta da dama nakan zauna in ta sauraren wakokin da, inna gamaji sai na dinga juya wakar, daga baya ina shekara 11 sai na fara rubuta waka amma ban shiga dadin rerawa, sai daga baya lokacin dana kai shekara 14 na fara yin waka da kaina kullum burina naga na tashi na zama shahararren mawaki a Duniya, kuma abokai nasun taimaka mun gurin samun ra’ayin waka.

Ya kaji ranar farko da ka fara shiga dakin rera waka?

Naji wahala gaskiya sosai kuma sai naji kamar an daura mun duniya akaina, kasan dik abun da mutum zai fara farko sai yaji daker, amma yanzu Alhamdulillah an goge, zuwa daya nake ma waka.

Da wani suna al’umma suka fi sanin ka dashi?

Lil beekay

A wani shekara ka fara waka?

2010

Daga lokacin daka fara waka kawo yanzu kana da wakoki kamar nawa?

A kalla wakoki na zasu kai 20, saboda ni abun da na yarda dashi shine ba yawan wakoki kesa mutum yayi sunaba, ka iya waka mai ma’ana wanda zai fasa gari shine kawai.

Ko zaka iya gaya mana sunayen wasu daga  cikin wakokin da kayi?

Eh, ga sunan kamar haka:  Back to back, Jeneth, Jogodo, You, Tel me yes, Their body, More blessings, Momys blessing, Omo alaji, Oyana, Men, Finally, Binary, Na you, Gibe me lobe, Ginger, Oo my god, Khadija, Saraunya, Rahmasadau, Science student.

Cikin wakokinka wanne kafi so?

Nafison  Science student

Me wakar ka Science student yake koyarwa?

Toh, wakar science student tina tarwa ne ga matasan kasar nan baki daya da su daina shaye-shaye ba abu bane mai kyau, domin shaye-shaye yana daya daga cikin abubuwan dake ingiza Al’umma ga halaka.

Daga lokacin daka fara waka kawo yanzu wasu nasarori ka samu?

Alhamdulillah, Nasamu nasarori marasa adadi don kuwa kaga ko hiran da mukeyi yandu ma ai nasara ne, sannan ma samu kyaututtuka da dama a guraren wasannin da na halarta, haka kuma al’umma kaduna da saura garuruwa sona bani goyan baya.

A wasu shekaru kasamu lambar yabo, kuma a ina?

Na samu a 2017 Nas b show Kaduna, 2018 ma na samu na NBM sallah funfair haka kuma a 2017 sallah funfair, da sauran gurare wasu na manta dasu.

Zamu so musan guraren daka je wasanni?

Gaskiya suna da yawa amma ga wadanda na iya rike wa, nayi wasa a Barnawa Kaduna Da kuma Kabala Costine Kaduna, haka kuma naje garuruwa da dama kamar Zariya, Naje Mina, Naje Abuja Naje Maiduguri na kuma je Niger republic

Ya kaji ranar da aka fara gayyatan ka wasa gaban masoyanka?

Naji dadi sosai saboda cigaba ne, kuma daga wannan lokacin ne nasan cewa wataran sai ya zama babu kamata a Duniya, saboda tin ranar farko na naja masoya da daman a shiga ran mutane Alhamdulillah. Wani kalubale ka fuskanta daga lokacin daka fara waka kawo yanzu

Gaskiya na fuskanci kalubale da dama musamman a gida Saboda a dangi bakowa bane yake so na da waka ba, haka kuma kana ma cikin tafiyar sai kaga da wuya kasamu masu tallafa ma, ko da ma ka samu mai taimaka ma din sun yarda zasu taimaka ma sai kaji sai sun bukaci dudi a hannunka.

Wani shawara zaka ba matasa masu kokarin fara wakar hausa hip hop?

Su dage su daura dik rintsi dik wuya watarana sai labara, su dinga sa niyar cewa shi za suyi a matsayin sana’a kuma su yadda da Kansu, don waka Sana’a ce mai kyau.

 Wani kalubale kuke fuskanta a Arewa?

Da daman wasu manya a Arewa kyamarmu sukeyi sai kaji wasu na fadin ba abu mai kyau mukeyi ba musamman Irin wakan da nakeyi, ba’a cikaji a Arewa ba saboda ni gaskiya ban cika sa hausa a cikin waka ba.

Wani kalubale kuke yawan fuskanta a tsakaninku mawakan Arewa?

Maganar gaskiya shine mawakan Arewa basu da hadin kai kwata kwata kuma sannan yawancin manyan suna da girman kai da bakin ciki, Kowa baya so ya taimake kowa.

To kai wani kokari kake gurin ganin kanku ya zama daya?

Ina kokarin yin wakoki tare da mawakan hiphop Hausa da yanayin waka na, don kaga ko Science Student dina nayi remid dinshi ne da Abk don.

To wani jan hankali zaka yima manyan mawakan dake Arewa?

Manyan mawakan da ke arewa su dinga tinawa cewa taimakan su akayi su kayi suna, Suma su taimake na kasa dasu akwai mawaka daya wa dake bukatarsu.

Cikin mawakan da muke dasu a Arewa da wa kafi kusanci?

Abk don

Wani kyakkyawan nufi kake ma Arewa hiphop nan da zuwa shekara daya?

Gaskiya Arewa hiphop za’a ji mu a Duniya baki daya don tabbas sai mun danne kudu nan gaba kadan.

Kana aiki ne karkashen wani kungiya ko zaman kanka kake yi?

Eh ina aiki ne yanzu a karkashin Nas B Record Studio.

Daga karshe me zaka cema masoyanka?

Nagode matuka da suka bani goyan baya kuma ina mai tabbatar masu da bazan taba yadda suba.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: