Yusuf Shuaibu">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTALIN ARZIKI

Tabbas Za A Cefanar Da Kadarorin Gwamnati Domin Samun Kudin Kasafin 2021 – Gwamnatin Tarayya

by Yusuf Shuaibu
January 18, 2021
in TATTALIN ARZIKI
2 min read
Bututun Man Nijeriya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Bayan shirin amso bashi a cikin gida da na kasashen ketare domin cike gurbin kasafin kudin shekarar 2021, gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa, dole ne a sayar da wasu kadarorin gwamnati domin samun sauran kudaden kasafin shekarar 2021. Haka kuma gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, sayar da wasu kadarori wadanda ba na mai ba su ne za su kasnce karin hanyoyin samar da kasafin kudin na shekarar 2021. Wannan yana daga cikin jawabin da ministar kudi da kasafi ta tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed ta bayyana a Abuja wajen taron masu ruwa da tsaki na kasafin kudin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta rattaba hannu a kan kasafin kudin shekarar 2021 a ranar 31 ga watan Disambar 2020 na naira tiriliyan 13.58, wanda kasafin kudin ya zarce daftarin da aka kai majalisa da karin naira biliyan 505 a watan Oktobar 2020. Kudaden da za a kashe wajen gudanar da harkokin gwamnati ya kai na naira tiriliyan 5.6 da naira tiriliyan 4.1 wanda za a kashe na manyan ayyuka, yayin da aka samu cibin naira tiriliyan 5.2. Ko da yake mutane da dama sun kalubalanci yadda gwamnatin tarayya take amso bashi wajen cike kasafin kudi a duk shekara. A wannan shekarar, gwamnatin tarayya za ta amso bashin naira tiriliyan 5.6 a nan cikin gida da kuma kasashen ketare. A cikin jawabin ministar ta bayyana yadda za a cike gibin kasafin kudin. Shugaban kasa da Misis Zainab ta bayyana cewa, dole ne Nijeriya ta amso bashin kudade daga Bankin Duniya da Bankin Musulunci da sauran kasashe kamar irin su Brazil domin cike gibin kasafin kudin wannan shekara.

A cewar kundin kasafin kudin, inda gwamnati za ta sami sauran kudaden kasafin kudin shi ne, cifenar da kadarorin gwamnati da kuma kadarorin wadanda ba na mai ba.

“Cefanar da kadarorin gwamnati da kuma sayar da kadarorin gwamnati wadanda ba na mai ba yana daga cikin karin hanyoyin samun kudaden kasafin kudi,” kamar yadda wani bangare daga cikin kundin ya bayyana.

A cikin watan Nuwambar shekarar 2020, akwamitin majalisa mai kulawa da kadarorin gwamnati ya bayyana cewa, bai da masaniyar sayar da kadarorin gwamnati daga wajen hukumar kulawa da kadarorin gwamnati. Wannan ya gudana ne lokacin da ake gabatar da kasafin kudin shekarar 2021. Kundin da aka gabatarwa kwamitin ya nuna shirin gwamnatin tarayya na shayar da tashoshin wutar lantarki na Geregu da Omotosho da kuma Kalaba a kan naira biliyan 434 a shekarar 201. Haka kuma, kudin ya bayyana shirin sayar da cibiyar gidan tarihi na Tafawa Balewa Skuare da dukkan tashorin jiragen ruwa kan naira miliyan 836, yayin da za a jinginar da filin wasa na Jihar Legas da na Abuja kan naira miliyan 100.

Shugaban kwaminitin, Theodore Orji ya bayyana cewa, kwamitin bai da masaniya a kan wannan shiri. Ya bayyana cewa, ya yi wa shugaban hukumar da ke kulawa da kadarorin gwamnati, Aled Okoh korafin bai sanar wa mambobin majalisar bayanan da suka dace.

Lokacin da aka tuntubi mai tsawatarwa na kwamitin, Sadiya Abdullahi ta bayyana wa manema labarai cewa, za a magance matsalar da ke faruwa. Ta kara da cewa, Mista Okoh zai bayyana a gaban kwamitin majalisa domin ya gabatar da mahimman bayanai a kan kararorin gwamnati da za a sayar da kuma farashin wadannan kayayyaki. Ta ci gaba da cewa, kwamitin da hukumar da ke kula da kadarorin gwamnati da gwamnatin tarayya za su yi aiki tare wajen warware wannan matsala.

SendShareTweetShare
Previous Post

Kamfanoni 96 Sun Bukaci Aikin Gyara Bututun Man Nijeriya

Next Post

CBN Ya Fitar Da Tsarin Gudanar Da Hada-hadar Kudade Ta Yanar Gizo

RelatedPosts

Emefiele

Bunkasa Tattalin Arziki: Nijeriya Na Bukatar Kara Kaimi Wajen Adana Abinci – Emefiele

by Yusuf Shuaibu
10 hours ago
0

Daga Mahdi M. Muhammad   Gwamnan Babban bankin Nijeriya (CBN),...

Bankuna

Rahoton Bangaren Bankuna Yana Nuna Samun Cigaba Mai Matukar Ma’ana – CBN

by Yusuf Shuaibu
10 hours ago
0

Daga Mahdi M. Muhammad   Rahoton karshe na Babban bankin...

Gwamnatin Masar

Lantarki: Nijeriya Za Ta Hada Kai Da Masar

by Yusuf Shuaibu
10 hours ago
0

Daga Mahdi M. Muhammad   Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya...

Next Post
Manoman Auduga

CBN Ya Fitar Da Tsarin Gudanar Da Hada-hadar Kudade Ta Yanar Gizo

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version