Connect with us

LABARAI

Tabbas Zan Yi Kafar Angulu Ga Gwamnatin Da Ta Gaza Kawo Ci Gaba A Bauchi –Ali Pate

Published

on

Daya daga cikin ‘yan takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi a lemar APC, Muhammad Ali Pate ya maida martani kan batun da ke cewa shi dan kwangilar siyasa ne kawai, inda shi kuma ke shaida cewar masu wannan batun sun tabbatar zai iya yin nasara ne a kansu.

Ya yi martanin ne a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida a sakatariyarsu da ke Bauchi a shekaran jiya, Ali Pate ya shaida cewar bai fito neman takarar gwamnan jihar Bauchi sai da ya nazarci hakikanin matsalolin da jihar ke fuskanta, don haka sha alwashin samar wa jihar Bauchi hanyoyin samun kudaden shiga ta habaka tattalin arziki da zarar ya kasance gwamnan jihar a zaben 2019.

Da yake maida martani a bisa wadanda suka kiransa da mai neman a bata kowa ya rasa ya ce, “akwai jami’an da suke jikin wani dan takara da suka ce ina son na yi kafar angulu wa gwamnatinsu. Sai na amsa da cewa, tabbas ina son na yi kafar angulu wa gwamnatin da bata kawo ci gaba, kuma na san jama’an jihar Bauchi ma za su yi kafar angulu ga duk wanda ya gaza kawo musu ci gaba,” Kamar yadda yake maida martaninsa

Dangane da manufarsa ta fitowa neman gwamnan jihar Bauchi kuwa cewa yake “Na fito wannan takara a karkashin jam’iyyar APC ne ba don komai ba sai don jihar Bauchi ya dace ta ci gaba fiye da yadda take a yanzu. Kowa ya sani cewar,” A ta bakinsa Pate

Cigarin Misau ya shaida cewar ciki da wajen jihar Bauchi matasa basu da aiki yi don haka ne ma yake da kyaukkyawar tsari wa matasa da zarar aka bashi damar zama gwamnan jihar, “masu sana’armu na karkara basu da jari, ‘yan kasuwarmu jarinsu baya-baya yake yi, ma’aikatanmu suna cikin yanayin aiki da matsaloli ne, tsoffin ma’aikata ‘yan fansho suna kuka da yanayin da ake ciki. Don haka dukkani wani dan jihar na kwarai da ke da wani abun da zai yi ba zai nade hannunsa ya ce ba zai yi komai kan matsalolin da suke jihar ba. a sakamakon gogewarmu na abun da muka sani a da, da yanzu na ga ya ya dace na fito domin kawo gyara mai sunan gyara a jihar Bauchi,” Inji dan takarar gwamnan

Ya shaida cewar jama’an jihar sun amince masa ya fito neman wannan kujerar, don haka ne ya shaida cewar suna da kwarin guiwar samun nasara a zaben 2019 da ke tafe.

Ali Pate ya shaida cewar yana da kwarewa kan ci gaba da habaka tattalin arzikin jihar, yana mai bayanin cewar zai kuma tashi tsaye wajen tabbatar da samar da kudaden shiga wa jihar ta Bauchi.

Ya shaida cewar abun takaici ne wasu jahohi da wasu kasashe suna morar fasahar da Allah ya yi masa ba tare da ya zo jiharsa ya shimfida sabon tsarin da zai kai jihar tundun mun tsira ba, “yanzu haka ka je jihar Ondo, shekara guda da ta wuce sun gina asibitin kiwon lafiyar al’umma suka sanya wa wannan jami’ar sunana, mun basu gudunmawa ne ya sanya suka sanya sunanmu, don haka da gudunmawar da zan iya bayarwa jihata,” inji Pate

Da yake facakala da matakin da uwar jam’iyyar APC a jihar Bauchi ta dauka na tsaida gwamnan jihar Bauchi a matsayin dan takarar gwamnan jam’iyyar, Pate ya ce, “wannan labari ne kawai suke yi, ta yaya ne za ku ce kun saida mutum daya ya nemi kujerar gwamna bayan akwai ‘yan takara har guda hudu?, idan za a yi wanna sai a nemi dukkanin ‘yan takarar gwamnan a ji amma basu yi haka ba, abun da suke so shine, suna so ne su kange kowa abun da ake yi a cikin shekaru hudun nan a ciki gaba da yinsa, mu kuma mun ce sam ba haka za a yi ba,” A cewar shi

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: