Mahdi M Muhammad" />

Tabbatar Da Tsaro: NAF Ta Gundunar Da Gagarumin Atisaye A Hanyar Abuja-Kaduna

Hanyar Abuja-Kaduna

A ci gaba da kokarin da ta ke yi na bunkasa kwarewa jami’an ta fannin shirin yaki domin tunkarar kalubale daban-daban na tsaron cikin kasa da tsare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya, rundunar sojin saman Nijeriya (NAF) a ranar, 2 ga Janairun, 2021, ne ta gudanar da atisayen hadin gwiwa na bincike da ceto (CSAR), a bangaren Sojoji na musamman (SF) da ‘K-9 (JCSAED)’ a kauyen Rijana da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Wannan sanarwar ta fito ne daga hannun Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar, Air Bice Marshal Ibikunle Daramola, a inda yake cewa, Atisayen wanda ake kiransa da “TAIMAKO YA ZO”, an tsara shi ne don samun dabaru, koyarwa na aiki don ingantaccen ayyukan CSAR ga wasu jami’an NAF wadanda idan ya kama dole ne su fita daga jiragen saman su a yanayin ayyukan gaggawa.

Daramola ya kara da cewa, sanin yadda za su ceto sauran jami’an daga mahalli mai hatsari yana da mahimmanci, musamman hakan na iya amfani a wajen ceto mutane a hannun masu satar mutane, kamar yadda NAF ta yi kwanan nan tare da wasu jami’an tsaro wajen ceton yaran da aka sace na makarantar sakandaren kimiyya ta Gwamnati.

Da yake jawabi yayin atisayen, Babban bako na musamman, Shugaban sojojin sama (CAS), Air Marshal Sadikue Abubakar, ya bayyana cewa, burin NAF gaba daya shi ne tabbatar da an horas da jami’ai da kayan aiki don kiyaye manyan matakan yaki da tasirin aiki. A cewarsa, a kokarin inganta NAF SF ta hanyar ingantaccen karfin aiki don mayar da martani kan kalubalen tsaro da dama da ke addabar kasar a fannonin yaki da ta’addanci, tsaron filin jirgin sama da ayyukan ta’addanci, NAF a shekarar 2019 ta gudanar atisayen yaki da ta’addanci da dama a jihohin Kaduna, Kano, Neja da Osun.

Shugaban ya ci gaba da cewa, mahimmancin horo ga rundunar yaki kamar NAF ba za a iya tsayawa da gudanar da shi ba yayin da ake samun horo na yau da kullum, wanda hakan shi ne ginshikin shirye-shiryen yaki. Ya ce, “A fahimtar hakan ne NAF ke tabbatar da cewa jami’an ta suna da nutsuwa kuma suna cikin koshin lafiya a kowane lokaci, ta hanyar horo da atisaye na yau da kullum domin mu ci gaba da kasancewa cikin shiri don kare kasarmu”.

Air Marshal Abubakar ya bayyana cewa, har ma da tsarin makamai na zamani, jami’ai masu kwarewa za su kawo sauyi a kowane yanayi na rikici. Wannan falsafar, in ji shi, an shigar da ita cikin manufofi da ka’idojin NAF ta yadda kowane jami’i zai ci gaba da kasancewa a shirye na yaki don tabbatar da inganci wajen gudanar da ayyuka da dama na sojoji.

Shugaban ya kara da cewa, a cikin yunkurin cimma kwarewar aiki, mambobin hukumar suna fuskantar tsauraran matakai na horo da kuma fallasa su zuwa yanayi daban-daban na kasa don ba su damar habakawa da kuma dorewar babban matakin gwagwarmaya. Ya ce, “Wannan, babu shakka, zai taimaka wa jami’anmu wajen yin aiki a mafi girman matsayi a duk lokacin aikinsu”.

Shugaban ya kara da cewa, a wannan lokacin na gudanar da atisayen ya kasance yazo daidai lokacin da za a iya gwada gwagwarmaya da karfin jami’an NAF don fuskantar kalubalen tsaro mai matukar wahala a halin yanzu da kasar ke fuskanta.

Air Marshal Abubakar, wanda ya nuna gamsuwarsa da jin dadi game da atisayen, ya ce, albarkatun da ake kashewa a kowace rana don tabbatar da cewa an ba wa jami’an NAF kwarewar da horon da ake bukata don gudanar da ayyuka cikin nasara, yana samar da sakamako na zahiri.

Da yake ci gaba da magana, shugaban ya ce, ya gamsu da wannan Atisayen dangane da daidaito tsakanin ayyukan sama dana kasa. A cewarsa, “tsaro ba wai kawai na harsasai, bama-bamai da rokoki ba ne, ya shafi duk wanda ya sa hannayensa ne don tabbatar da cewa kasar ta samu tsaro.

Wannan Motsawar za ta kasance mai ci gaba, mun yi daya anan. Daga yanzu zuwa Yuni 2021, zamu samar da 6 daga wadannan Atisayen. Yawancin wadannan Atisayen yanzu zasu koma yankin Arewa maso yamma, musamman a jihohin Zamfara da Katsina. Mun kuma tada sansanin NAF a Funtua don kara tabbatarwa da kuma kawo tsaro har ma da kusanci da mutane”.

Shugaban ya yi amfani da wannan damar don nuna matukar godiyarsa ga babban kwamandan askarawan kasar, Shugaba Muhammadu Buhari, kan mara baya da goyon baya ga ci gaba da bunkasa ayyukan NAF. Ya kuma godewa mambobin majalisar kasa da  Ministan tsaro, Shugaban hafsoshin tsaron da sauran shugabannin hafsoshin, domin ci gaba da mara wa NAF baya.

shugaban ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa NAF na ci gaba da jajircewa don aiwatar da ayyukanta na kundin tsarin mulki, kuma za ta ci gaba da sauke nauyin da ke kanta na kare mutunci da ikon kasar nan, walau ta yin aiki kai tsaye ko kuma tare da hadin gwiwar sojojin sama da sauran hukumomin tsaro.

Gudanar da atisayen a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, in ji CAS, zai yi tasiri kwarai da gaske wajen dakile masu aikata laifuka daga fitowa don afkawa ‘yan kasa marasa laifi.

Tun da farko a jawabin marabarsa, Kwamandan Rundunar Sojan Sama (AOC), Kwamandan Ayyuka na Musamman (SOC), Air Bice Marshal (ABM) Charles Ohwo, ya bayyana cewa, Atisayen ya yi daidai da kokarin da shugana sojin ke yi don bunkasa ci gaban dan Adam ta hanyar karfi da kuma haifar da horo na daidaitacce aikin kwarewar jami’ai.

Manyan abubuwan da aka gudanar a wannan atisayen sun hada da bayanin yadda ake gudanar da aiki da kuma bayar da umarni daga Kwamandan 013 Force Response Force, Skuadron Leader Bictor Uba tare da karamin rundunarsa da kuma kwamandojin bangaren, wadanda aka gudanar a bayan kofofin.

Wannan ya biyo bayan rashin aiwatar da tsarin aiki, wanda ya nuna harbe-harben kananun rokoki daga NAF da jirgi mai kai hare-hare, tare da shigar da jami’an CSAR da gwajin saurin gudu da kuma karar NAF SF (PANTHERS) da abubuwan K-9 da motsawar tawagogi zuwa yankin da ake so.

Har ila yau, an sake samar da harsasai ga sojojin da ke kai harin ta hanyar saukar da dabaru daga jirgi mai saukar ungulu da kuma ceton matukan jirgi da suka fadi kasa cikin mawuyacin hali, fitar da tawagar da aka kaiwa hari ta sama yayin da ake ba su taimako na kusa da sama ta hanyar jirgin helikwaftan yankin da ake nufi.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci bikin sun hada da Manyan Shugabanni NAF, Babban jami’in Runduna ta 1, Sojojin Nijeriya, Kwamandan Sojojin Sama, Kwamandan Sojojin Kwalejin Ma’aikata, Jaji, Mataimakin Kwamandan Kwalejin tsaro na Nijeriya, daraktoci daga hedikwatar NAF, Kwamandoji na NAF da kuma Shugaban al’ummar Rijana, Dagacin Rijana, Fadan Achi, Mr Ayuba Dodo Dakolo, da sauran manyan hafsoshin soji da yawa.

Exit mobile version