Connect with us

MAKALAR YAU

Tafakkuri A Kan Ni’imomin Allah Lokacin Korona

Published

on

Hausawa su na da wani irin Karin magana mai kayatarwa da ke cewa, “ka gode wa Allah ko da a bakin kura ka ke.” Tabbas wannan karin magana ya yi kyau sosai wurin karfafa wa masu imani kwarin gwiwa a cikin yanayi na jarrabawar Ubangiji. Sannan har ila yau, karin maganar ya na nuni da ishara ga masu hankali su fahimci falalar Allah a cikin kowane yanayi. Duba dai bakin kura, kowa ya san da mutum ya tsinci kasa a bakin kura, sai dai wani ikon Allah, amma zai bakunci lahira. Amma duk da haka a ka ce mutum ya gode wa Allah ko da ya tsinci kansa a wannan yanayi.

Kenan mu da ke rayuwa a doron kasa yau kaf a cikin duniya, mun tsinci kanmu a yanayi irin na bakin kura, ma’ana halin da mu ke ciki na fama da annobar Korona. Wannan hali da mu ka shiga ya sa; ya zama wajibi mu yi waiwaye a kan ni’imomin da Allah ya yi ma na wadda kila ba mu taba tsinkaye a kai ba sai ta sababin zuwan Korona.

Misali, ba mu taba sanin cewa babbar ni’ima ce da Allah ya yi mana ba, ta idan mutum ya wayi gari ya shirya; ya nufi wurin da yake neman abinci cikin ‘yanci da walwala ba tare da tsangwama ko takura ba, sai ta sanadin Korona.

Mun taba tunanin cewa cudanya a tsakaninmu da shugabanninmu da abokan aiki, a yi hira ta rayuwa cikin annashuwa da farin ciki babbar ni’ima ce da Allah ya yi mana? Yanzu wannan ba halin yi, galibin mutane kowa yana gida a garkame ba halin fita sai ga ‘yan kalilan. Su kansu ‘yan kalilan din da aka bari su fita kowa yana tsoron kowa, saboda Korona. Ashe sakewar da muke samu ta hulda a tsakaninmu babbar ni’ima ce da Allah ya yi mana wadda zuwan Korona ya taimaka wajen yin tafakkuri a kanta.

Mun taba tunanin cewa tsare-tsaren da muke yi na jerin abubuwan da za mu aikata a ranaku ko makonni ko shekaru masu zuwa da suka kunshi kasuwanci, hutu, bukukuwa da sauransu kuma da yakinin abubuwan za su yiwu ba tare da cin karo da wata matsala ba, garabasa ce da Allah ya ba mu? Yanzu hakan na yiwuwa a gare mu? Ashe Korona ta tunatar da mu cewa yin wadannan abubuwa ba tare da fargaba ba, wata babbar ni’ima ce da Allah ya yi mana.

Hatta bautar Allah da muke zuwa yi a wuraren ibadunmu cikin ‘yanci da walwala, Rahama ce ta ganin dama da Allah ya yi mana. Na san cewa kowa ya san yadda aka rufe manyan wuraren ibadu na duniya saboda Korona. Masu ibada suna ji suna gani babu halin zuwa. Ashe wajibinmu mu gode wa Allah a bisa ni’imar da ya yi mana ta zuwa bauta masa cikin ‘yanci.

Tafiyar da harkokin rayuwa da makota, cudanya da abokai da ‘yan’uwa da abokan arziki a duk inda muka ga dama, ita ma ni’ima ce ta musamman da Allah Mahalicci ya yi mana. Korona ta fito mana da abin a fili.

Galibi, hankulanmu ba su taba tunanin cewa amfani da ababen hawa na haya masu daukar jama’a daban-daban, walau babura ko bus-bus, a tafi ana hira a tsakanin abokan zama na cikin motar ko dan acabar da ya dauko mutum, har ma wani lokaci da goyon wani a kan wani saboda rage kudin mota, duk wata falala ce daga Allah Ta’ala ba. Amma Korona ta sa mun fahimci wannan.

Halartar tarukan jama’a, matsawa ko zama kusa da kusa, rungumar ‘yan’uwa da musabaha a tsakanin juna ba tare da fargabar komai ba, duk Rahama ce da Allah ya yi mana lokacin da muke yi ba tare da ta-ka-tsan-tsan ba.

Duk wadannan misalan abubuwan da na kawo, kadan a cikin al’umma suke ankare da su kafin zuwan Korona, amma galibi sai da Korona ta bulla muka fahimci cewa ni’imomi ne da Allah ya yi mana da ya dace mu rika gode masa a kai. ‘Yanci ne da muka mora ba tare da tsinkaye a kan falalar da ke cikinsa ba har sai da Korona ta zo ta raba mu da su.

Korona ta girgiza masu iko, sanan ba ta bar talakawa ba, kowa yana ganin ta-kansa. Ba a kasa daya ba, ba a yanki daya ba, ba a nahiya daya ba, a daukacin fadin duniya.

Lokaci bai kure mana ba, yana da kyau mu zurfafa tunaninmu a kan ni’imomin da Allah ya yi mana tare da gode masa a kai. Sannan idan Allah ya yaye mana Korona, muka dawo cikin walwala da ‘yanci, mu yi kokarin yin waiwaye adon tafiya kan ni’imomin Allah domin godiya gare shi don ya kara mana.

Bala’in da duniya ta shiga a kan Korona yana da girma. Masu Karin magana na cewa, duk abin da ya koro bera ya fada wuta, to ya fi wutar zafi. Saboda Korona, an samu Turawan da suka rika kyamatar komawa kasashensu na asali. Wa ya taba tunanin Turawan Italiya da ke Somaliya (kasar da yaki ya kusa durkusarwa bakidaya) za su ki komawa kasarsu, alhali izinin zaman da aka ba su ya kare, amma kiri-kiri suka ce ba za su koma ba, suka nemi gwamnatin kasar ta sabunta musu izinin saboda tsoron Korona a kasarsu?

Wa ya taba tunanin Firaministan Somaliya da ya koma Birtaniya da zama domin tsira da rayuwarsa zai mutu a can sakamakon kamuwa da Korona? Ya bar gida don tsira da rayuwarsa amma ashe ya kai kansa ne wurin ajali.

Wa ya taba tunanin katangar da Shugaban Amurka Donald Trump ya gina a tsakanin kasarsa da Meziko zai zama alheri ga ita Mezikon, saboda kamarin da Korona ta yi a Amurka, har ma kasar tana korar Amurkawan da ke neman mafaka a cikinta domin gudun kamuwa da annobar cutar, kuma ita ma kasar ta ce ba za ta karbe su ba?

Wa ya taba tunanin kasashen da suke fama da bakin-haure da ke kashe makudan kudade a kan matsalar a yanzu sun huta, babu wani bakon-haure da ke sha’awar tsallakowa ta cikinsu ya shiga yankin Turai?

Ko akwai wanda ya yi tunanin manyan kasashe na duniya masu ji da kansu ta fuskar karfin soja da na tattalin arziki, a halin yanzu duk za su shiga cikin firgici da tsoro irin haka?

Wa ya taba tunanin likitoci masu kula da lafiya za su zama ababen tausayi, masu mutuwa farad daya a lokacin da suke duba wani majinyaci?

Dukkan wadannan isharori ne gare mu cewa mu yi tunanin komawa ga Allah, wanda dama daga wurinsa muke, kuma wurinsa za mu koma. Allah ya datar da mu a kan hakan tare da gode wa ni’imominsa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: